Kofar Kabuga

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ƙofar Kabuga, Kano 1621


Gabatarwa


Ƙofar Kabuga


Ƙyauren Ƙofar Kabuga

An gina wannan ƙofa ta Kabuga a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Nazaki . Ƙwalli (1997), ya tafi akan cewa sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga bugun lalle da mutane suke yi a wannan ƙofa. A cewar sa, yankin wannan ƙofa waje ne na noma lalle, sannan kuma bayan mutane sun ɗebo lallen daga gonakin sukan kawo shin an ya bushe sannan su buge shi su ɗebe ganyen daga baya kuma su tafi das hi zuwa gari dan sayarwa.

Amma a ra’ayin Gwangwazo (2003), cewa ya yi asalin sunan wannan ƙofa ya samu daga labarin wani babban malami masani da matarsa ta mutu. Shi wannan malami watarana ya tafi unguwar Madabo raɗin suna ya bar matarsa a kwance ba lafiya, kafin ya dawo sai ta rasu. Da ya dawo sai ya taras da ita an tafi da ita maƙabarta har an saka ta cikin rami an fara ɗora tukunya, sai ya bubbuge tukwane ya shiga ciki ya kwanta tare da ita yana kuka, yana cewa sai dai a rufe su tare. Da jama’a suka ga haka sai suka fitar da shi da ƙarfi suka riƙe shi sannan suka binne shi. To daga wannan lokaci sai mutane suka riƘa yin inkiyarsa da Malam Kabi Gawa hart a kai wasu suna rage sunan su ce Malam Kabuga. Saboda haka aka sawa wannan ƙofa suna da Kabuga.

An ce ta wannan ƙofa sarakunan Kano suke fita zuwa yaƙin Ƙaraye da Zazzau. Sannan kuma ta wannan ƙofa baƙin fatake suke shigowa daga Gwanja.

Manazarta:


Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna.

Ƙwalli M. K. (1996). Kano Jalla Babbar Hausa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Sarakunan Kano 1805 -2003. Gwangwazo M.A. (2003). Kano Garin Albarka (B), Kudu da Arewa.

Gwangwazo M.A. (2003). Tarihin Kano Kafin Jihadi, Wangarawa sun iso Kano, Littafi na Biyu.

Gwangwazo M.A. (2003). Gani ya Kori Ji, Kano da ƙofofinta Fiye da Shekaru 800. Abba Press Nigeria Limited. Aminu Kano Way, Goron Dutse by Prison Junction. Kano-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub