Shafin Farko

Malamin Makaranta


Gabatarwa

Malamin makaranta shi ne mutumin da karantarwa ta zamo sana’arsa. Ta wata sigar kuma ana iya cewa, malami shi ne mutumin da ya taimaki wani ya samu ilimi, fasaha, ko wata daraja (Wikipedia, 2017). Sannan kuma an ce malami shi ne mutumin da yake karantarwa ko kuma yake tallafawa koyo (Missokia, 2013).

Gudunmawar da malami ya ke bayarwa a cikin al’umma tana da yawa. Matsayi da darajar malaman makaranta takan bambanta daga al’umma zuwa wata al’ummar ko kuma daga ƙasa zuwa wata ƙasar. Amma wani abu guda shi ne cewa, duniya har yau bata ƙoshi daga ƙishin ruwan ƙwararrun, gogaggun malamai a kowane fanni na rayuwa ba; abin nufi shi ne cewa, har zuwa yanzun nan da ka ke karanta wannan rubutu, duniya baƙin ɗayanta, tana da buƙatar ƙarin ƙwararru kuma gogaggun malamai a kowane fanni na rayuwa.

Tushen cigaban kowace al’umma a duniya shi ne ilimi mai inganci, nagartar ilimi kuma ta ta’allaƙa ne kaco-kaf a kan malamai. Kenan, ana samun ingantaccen ilimi ne kawai idan akwai ƙwararru kuma gogaggun malamai. Shi malami, cikakken abin koyi ne ga ɗalibai a kowane matakin karatu. Dukkan wani motsin malami, abin kwaikwayo ne a wajen ɗalibai. Salon magana, saka sutura, salon tafiya, cin abinci, barkwanci, da sauran su, na daga cikin ababen da ɗalibai kan koya daga malamansu. Mai karatu, zan so ka ɗan tsahirta, ka waiwaici rayuwarka ta karatu tun daga firamare zuwa matakin da ka ke a yanzu, malamai nawa ka kwaikwaya? Ko kuma, lura da malamai masu karantarwa a makarantun addini, kai da ma malamai masu wa’azi, za ka taras cewa, jama’a kan kwaikwayi rayuwarsu.

Nauye-Nauyen da ke Kan Malami

Tica uban karatu!, in ji marigayi Ɗanmaraya Jos, Ka sani cewa, kana da matuƙar tasiri a rayuwar ɗalibanka, sannan kuma kana da gudunmawa mai tarin yawa da za ka iya basu, musamman ma yaran da ke karatu a matakan da ake kira matakin farko (O’leɓel). Da zarar sun zo makaranta, to fa kai ne a matsayin mahaifinsu, ɗan’uwansu, abokinsu, sannan kuma malaminsu mai basu tarbiyya. Tirƙashi, wannan matsayi da girma ya ke.

Akwai ɗawainiyoyi masu tarin yawa da ke kan malamin makaranta baya ga asalin aikinsa na karantarwa. Babbar manufar tura ɗalibi makaranta ita ce ya samu ilimi. Shi kuma ilimi bai taƙaitu da iya karatu, rubutu ko koyon sana’a ba. Margaret (1978), ta siffanta mutum mai ilimi a matsayin mutumin da zai iya yiwa kansa tunani. Ƙari a kan haka kuma, ya zamo mai kyakkyawar hulɗa da jama’a, sannan kuma managarci wanda zai iya amfanar da kansa da kuma al’ummarsa.

Gina mutumin da ya tattara waɗannan siffofi da aka zayyana a wannan sakin layi na sama da ma wasu, na daga cikin nauye-nauyen da ke kan malami. Kenan, karantarwa, reno, shirya wasannin motsa jiki, faɗakarwa, kula da tsaftar muhalli, cusa halayen kirki a zukatan ɗalibai, adana bayanai game da ɗalibi, tallafa wa girman jiki, koyar da kyakkyawar hulɗa da jama’a, da sauran abubuwan da suke da dagantaka da waɗannan, dukka sun rataya a wuyan malami. Ya malam, kada ka manta a farko-farkon wannan rubutun na ce kai uba ne/uwa, ɗan’uwa/’yar’uwa, aboki/ƙawa, mai reno, sannan kuma malami ga ɗalibin da ke gabanka.

Siffofin Nagartaccen Malami

Siffofi a nan na nufin ƙualities, nagarta kuma ta ɗauki ma’anar good. Kenan idan aka ce siffofin nagartaccen malami a wannan rubutun ana nufin Ƙualities of a good teacher; waɗanda kuma halaye ne da ake son dukkan malami mai karantarwa ya mallake su. Samun waɗannan siffofi, su suke saka malami ya zama ya zauna a zukatan ɗalibai zaman dirsham; su suke mayar da malami ratsa unguwa, a haifi kamar ka. Muhimmai daga cikin waɗannan siffofi akwai:

  1. Sanin Fanni: Abu ne mai matuƙar amfani ya zamo malami ya san fannin da ya ke karantarwa. Masu iya magana sun ce, idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa, da kuma cewa, maras abu baya bayar da shi; wato ba a kyauta da babu. Kuma yaro baya ɗaukar yaro, sai dai rungume ni, mu faɗi.
  2. Yana da kyau sosai ga malamin da zai karantar da wani darasi ya zama masanin wannan darasin. Wannan na bai wa malami cikakkiyar damar fuskantar dukkan ƙalu-balen da ka iya taso masa a lokacin karantarwa. Kada ka kuskura ya kai malam, ɗalibanka su fahimci cewa sun fi ka sanin fannin da ka ke karantar da su. Kashinka ya bushe! Ilimi yanzu ya yawaita a duniya, a daidai lokacin da ka ke karantarwa, za a iya samun wani ɗalibin mai wayo ya tsunduma Intanet, ya samo bayanan da suka fi naka, ko kuma ya duba wasu littattafan tun kafin shigarsa aji, ko bayan ka karantar da shi ya je ya duba ya taras cewa, ka ɗan kauce hanya, duk waɗannan suna ragewa malami daraja a idon ɗalibai.

    Saboda haka, abu ne mai matuƙar muhimmanci ga malami ya zama masanin fannin da yake karantarwa, wannan kuwa na yiwuwa ne kawai ta hanyar zurfafa bincike da sabunta ilimin da malami ya ke da shi a wannan fannin. Ina baka shawara, kada ka kuskura ka tunkari ɗalibanka ba tare da ka waiwaici darasin da zaka koya musu ba, koda kuwa ta hanyar zama ne ba tare da takarda ba, ka tuna abubuwan da zaka karantar, ka tabbata sun zo maka a ka kafin shigarka aji.

  3. Dabarun Karantarwa: Sanin makama, salo, da kuma dabarun karantarwa su ne adon malami. Bayan malami ya zama masanin fanni, to abu na gaba kuma shi ne ya san salo da dabarun karantarwa. Wannan shi ne abin da zai baiwa malami damar cusa ilimin da ya ke son koyar da ɗalibansa cikin sauƙi kuma a marmarce. Shi kuwa salo ko dabarun karantarwa, shi ne abin da a Turance aka kira method of teaching. Akwai dabarun ko salo-salon karantarwa da dama, sannan kuma, muhallin karantarwa, nau’in ɗalibai, lokaci da kuma nau’in darasin da za a karantar da sauransu, su suke bayyana wanne irin salon karantarwa za a yi amfani da shi. Saboda haka, ya kai malami gareka, ka tashi kan san salo-salon karantarwa da dama.
  4. Sutura: Kyakkyawar shiga ta kamala, wacce ta dace da wata al’ada karɓaɓɓiya a idon jama’a, abu ne mai amfani ga mutuncin malami. Saboda haka malami ya kula sosai wajen yin shiga ta kamala. Wasu lokutan, al’adu kan yi tasiri a wasu guraren, ta yadda idan malami ya yi shigar da ta saɓa al’adar guri, to darajarsa takan ragu a idon masu kallonsa, waɗanda za su iya zamowa daga cikin ɗalibansa, abokan aikinsa da kuma iyayen yaran da yake karantarwa. Kar ka manta ya malam, kai fa abin koyi ne.
  5. Wani abu kuma shi ne cewa, ba a cika son suturar ta zamo mai tsada ba, saboda gudun koyar da yara rayuwa mai tsada. Baka sani ba wani yaron yana iya zuwa gida ya ce shi lallai sai an ɗinka masa irin kayan malam wane. E-mana, baka sani ba idan yara suka koma gida sai wani ya ce shi ne malam wane, kuma dukkan irin abubuwan da ka ke yi a makaranta haka ya ke maimaitawa a gida. Saboda haka babban abin da ake nema a wajneka shi ne saka suturar da ta dace da karɓaɓɓiyar al’ada a muhallin da ka ke.

  6. Tsafta: Tsafta, ita ce abokiyar ruɓin sutura. Malami ya zama mai tsaftar jiki da muhalli. Tsaftar jiki kuwa ta haɗa da ta gangar jiki da kuma sutura. Kar ka saka kayan da suka dace da karɓaɓɓiyar al’ada amma kuma su zama daƙan-daƙan. Assha! An yi ba a yi ba kenan. Wasu yaran idan suka koma gida suna bayar da labari, sai su ce mama, malam wane ƙazami ne, na ga miya a jikin rigarsa ko kuma manja a jikin zanenta.
  7. Iya Magana: Iya magana da ma’ana ta sanin kalmomin da ya dace a yi amfani da su wajen gudanar da darasi da kuma hira, bayar da umarni, da sauransu.
  8. Haƙuri: Halin mutum sai lillahi. Saboda haka haƙuri shi ne maganin zaman duniya. Malamin makaranta ya zama mai matuƙar haƙuri da halayen ɗalibansa, abokan aikinsa, iyayen yara da kuma sauran jama’ar da ya ke zaune da su. Idan wani ɗalibi ya aikata ba daidai ba, samo wata hanya ta cikin hikima da za ka yi masa gyara. Yawanci, kalmomin yabo ga wanda ya yi aiki mai kyau sukan kwaɗaitar da wasu su yi aiki irin nasa. Sannan kuma masu yin akasin haka sukan nisanci nasu halin.
  9. Sanin Buƙatun Ɗalibai: Sanin buƙatun ɗalibai, wani babban sinadari ne a harkar karantawa. Saboda yana taimakawa malami yin hukuncin da ya dace. Buƙatun yara, sun bambanta da na samari, buƙatun samari sun bambanta da na matasa, hakan nan kuma buƙatun masa sun bambanta da na manyan mutane.
  10. Misali, yara ƙanana, basa iya jure dogon zama, saboda haka ake haɗa karantarwarsu da nishaɗantarwa ta hanyar waƙa, da malami zai shiga ajin matasa ya takarkare yana koyar da su ta hanyar waƙa, ko kuma yana faɗi suna maimaitawa, suna fita daga ajin wani zai ce, wannan malamin bai san abin da yake yi ba, yaya zai riƙa yi mana waƙa a aji kamar wasu yara? Amma kuma fa duk da haka waƙar ma da nata muhallin.  

  11. Kyawawan Halaye: Nagarta, ƙusa ce a harkar karantarwa. Saboda haka malami ya zamo mai halaye ababen ambato kamar irin su sakin fuska, sauƙin hali ga ɗalibai, sauraron koken ɗalibai, taimaka musu wajen warware matsalolinsu na harkar karatu da ma na yau-da-kullum, suna ƙara danƙon zumunci tsakanin malami da ɗalibansa.
  12. Nazari: Dole malami ya zama manazarci, ya riƙa bibiyar abubuwan da ke faruwa yau-da-gobe. Kamar yadda aka ambata a mataki na farko. Idan malami ya sake ɗalibansa suka fi shi bincike, to tabbas raini zai shiga tsakani. Zan iya tunawa, akwai wani malamin wata babbar kwaleji, da ya shiga Intanet ya rarumo takardun darasin (lecture note) wata babbar jami’a a wata ƙasar da ta cigaba. Ya danƙarawa ɗalibansa ita ba canjin ko harafi, sannan dukkan tambayoyin jarabawar da suka fita a can da amsoshinsu, ya ɗebo tambayoyin ya lafta musu. Sai aka samu wani ɗalibi mai yawan bincike, ya shiga Intanet ya zaƙulo waɗannan takardu wa wannan malami nasu ya basu. To babbar matsalar ita ce, shi malamin bai tsaya ya karanta ba, bare ya tace na tacewa, ya bar na bari, sannan kuma da ya shiga aji sai ya kasa yi wa ɗaliban cikakken  bayanin abin da ke cikin takardun. Daga ƙarshe, sai raini ya shiga tsakanin ɗaliban da wannan malamin.
  13. Na kawo wannan labarin ne a matsayin misali. Saboda haka malamai a kiyaye. Intanet, kafa ce ta samu bayanai a dukkan fanni na rayuwa, amma yana da kyau idan malami ya shiga ya ɗebo ya tsaya ya karanta, ya tace na tacewa, ya ɗebi na ɗiba. Rashin yin haka, akwai matsaloli. Ana ma iya samun saɓani tsakanin abin da ka kwaso da kuma wanda ke cikin manhajar da ake son ka karantar da yaran.

  14. Juriya da Jajircewa: Ya malam, ka zama mai juriya game da dukkan abubuwan da za su fuskanto ka a wannan aiki naka na karantarwa. Daga ciki akwai jurewa wahalar aikin, jurewa zaman nazari, jajircewa a kan yin nazarin, da sauransu. Idan ka samu waɗannan halaye, tabbas nasara ce za ta biyo baya.

Hulɗa/Dangantaka

Wata gaɓa mai tarin fa’ida a harkar karantarwa ita ce hulɗa ko cuɗanya ko kuma dangantaka tsakanin malamin makaranta da sauran jama’a, a dunƙule, akwai dangantaka tsakanin:

  1. Malami da malami.
  2. Malami da ɗalibi.
  3. Malami da iyayen yara.
  4. Malami da sauran ma’aikata.
  5. Malami da sauran jama’ar da ke kewaye da makaranta.

Dukkan waɗannan, ababen lura ne da kuma baiwa kowa haƙƙinsa. Saboda haka ne ma zaka taras cewa, akwai wata ƙungiya da ake kafawa ta iyaye da malaman makaranta (PTA), wacce ke da manufa ta ƙarfafa zumunci tsakanin malamai da iyayen yaran da ke makaranta.

Manazarta:


Lauermann f. V. (2013). Teacher Responsibility: Its Meaning, Measure, and Educational Implications. The University of Michigan.

Missokia E. (2013). Who is a Teacher? Quality Teachers for Quality Education, Role/Responsibilities of a Teacher. HakiElimu Position Papers. Dar-es Salaam, Tanzania.

Wikipedia (2017). Teacher. https://en.m.wikipedia.org/wiki/teacher