Kyawawan Halaye

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kyawawan Halaye


Gabatarwa

Abin da muke son yi a wannan gaɓa shi ne kawo jerin sunaye kyawawan halaye ababen yabo da Bahaushe yake ɗora ɗansa a kai da kuma bayanai game da su bakin gwargwadon abin da ya samu.

Waɗannan kyawawan halaye da su Bahaushe yake yiwa ɗansa kwalliya. Idan ka kalli Bahaushe, za ka same shi mutum ne mai kawaici, karɓar baƙi, dogaro da kai, kunya, riƙon addini, gaskiya da riƙon amana, zumunci, taimakon juna, ƙaunar juna da sauransu. Idan ka samu Bahaushen asali, za kuwa ka same shi da waɗannan halaye.

Haƙuri

Haƙuri wadar mai shi. Mai haƙuri yakan dafa dutse ya sha romonsa. Haƙuri, shi ne kai zuciya nesa ko kuma danne zuciya daga bayyana fushi, kwaɗayi ko damuwa da sauransu. Hali ne na kirki mai tarin fa’ida a rayuwa. Haƙuri, yana da ‘ya’ya da yawa a cikin kyawawan halaye. Abin nufi, haƙuri yana haifar da wasu kyawawan halayen da dama.

Haƙuri yana hana ƙarya, cin zarafin wani, faɗa, hassada, sata, shaye-shaye da sauran miyagun halaye. Saboda haka haƙuri yana daga cikin manya-manyan halayen kirki da Bahaushe yake koyar da ɗansa. A duk lokacin da aka yi wa yaro abin da bai dace ba, iyayensa sukan rarrashe shi, sannan su ce da shi ya yi haƙuri. Saboda haka sai yaro ya danne zuciyarsa ya yi haƙuri bisa abin da aka yi masa ba tare da ɗaukar fansa ba.

Kuma da yake ba a raba rayuwar Bahaushe da addinisa na Musulunci, za mu kawo  hadisin da aka ruwaito daga Suhaibu, Allah ya yarda da shi da ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Mamaki ga al’amarin mumini, dukkan al’amuransa alheri ne a gare shi. Ba kowa ke samun wannan ba sai mumini. Idan farin ciki ya same shi sai ya gode, sai abin ya zama alheri a gare shi. Idan baƙin ciki ya same shi, sai ya yi haƙuri, sai ya zama alheri a gare shi”.

Yafiya/Afuwa

Yafiya ita ce idan mutum ya yi maka laifi ka ji cewa bai yi maka komai ba. Ka ƙyale shi kana mai nufin baka son a hukunta shi saboda wannan laifin ko kuma kai ka rama a gaba a bisa wannan laifi da ya yi maka. Wannan hali na yafiya kuwa, haƙuri ne ke haifar da shi.

Kawaici

Kawaici na nufin kawar da kai. Kawar da kai kuma a Hausance shi ne idan aka yi wa mutum laifi ka ƙi yin magana kuma ba tare da kana jin haushin wanda ya yi maka laifn ba. Misali, kamar a ce mutum ya zo gabanka ya aikata wani abu da ya san baka so, a nan sai ka yi kamar baka gan shi ba. Sannan kuma ya zama baka ji haushinsa ba, baka kuma ƙudurce cewa sai ka rama a gaba ba. Wannan shi ne kawaici. Shi ma wannan hali haƙuri ne yake haifar da shi.

Gaskiya

Gaskiya dokin ƙarfe, duk wanda ya hau ba zai zame ba. Shi kuwa Sa’adu Zungur cewa ya yi: “Idan za ka faɗi, faɗi gaskiya, komai taka ja maka ka biya”.

Gaskiya kuma ita ce aikata abu ko faɗin magana kamar yadda take, babu daɗi bare ragi. Faɗin gaskiya yana da matuƙar wahala ga mai faɗa da kuma mai sauraro.

Gaskiya, hali ce mai matuƙar muhimmanci, tana kare mutuncin mai faɗinta tare kuma da ɗaukaka darajarsa. Tana daga cikin siffofin da Bahaushe yake matuƙar mutunta mai ita.

An taɓa yin wani zamani da Bahaushe ya zama abin mutuntawa a duniya saboda faɗin gaskiya. A irin wannan lokaci har a garin Makkah Bahaushe yakan raba gardama ko faɗa a tsakanin Larabawa. Saboda haka gaskiya na daga cikin halayen da Bahaushe yake tarbiyantar da ɗansa.

Ga wani hadisi guda ɗaya da za mu yi wa mai karatu guzuri da shi a kan wannan gaɓa. Annabin Rahama (SAW) ya ce: “Haƙiƙa, gaskiya tana shiryatarwa zuwa ga biyayya, ita kuma biyayya tana shiryatarwa zuwa ga aljanna. Haƙiƙa mutum ba zai yi gaskiya ba, har sai an rubuta shi mai gaskiya a wajen Allah. Haƙiƙa ƙarya, tana shiryatarwa zuwa ga fajirci, ita kuwa fajirci tana shiryatarwa zuwa wuta. Mutum ba zai yi ƙarya ba, har sai an rubuta shi maƙaryaci a wajen Allah”. Bukhari da Muslimu ne suka ruwaito shi.

Riƙon Amana

Riƙon amana na nufin duk abin da aka bai wa mutum ajiya a same shi kamar yadda aka bashi ita. Wannan ita ce ƙololin riƙon amana.

Wannan halin idan aka ƙarfafe shi da faɗin gaskiya, suna saka mutum ya zama yardajje a cikin jama’a. Wato zai zama cikakken abin dogaro a wajen jama’a a cuɗanya da kuma magana. Zai zama ba za a ji tsoron yin hulɗa da shi ba saboda gudun cutarwa. Waɗannan halaye guda biyu kuwa, haƙuri ne mahaifinsu.

Ɗan Bahaushe, ana yi masa tarbiyya da riƙon amana. Bahaushe yana ce da ɗansa, idan mutum ya baka ajiyar kayansa, kar ka taɓa masa.

Tausayi

Tausayi na nufin jinƙan mai rauni, wanda kuma shi ne rashin jin daɗi a rai game da wani hali na rashin kyau da mai rauni ya shiga tare kuma da bayar da gudunmawar fitar da shi daga cikin wannan hali idan da damar yin hakan.

Raunana kuwa, su ne tsofaffi, yara, mata da sauran marasa hali ko masu tawayar wani sashen jiki.

A al’adance, Bahaushe yakan tausayawa babban mutum mai shekaru ya karɓi kayan da yake ɗauke da shi, ya kai masa gida domin shi dattijon ya samu hutu. Ko kuma idan ya ga wani ma tawayar wani sashen jiki kamar a ce makaho yana tafiya, sai ya kama sandarsa ya ɗora shi a kan hanyar da ba zai samu matsala ba. Ko kuma idan ya ga yaro yana tafiya har ta kai ga ya yi tuntuɓe ya faɗi, yakan je ya ɗaga shi sannan ya rarrashe shi.

Kunya

Kunya ita ce rashin aikata wani aiki ko faɗin wata magana a gaban wanda yin hakan zai haifar da raguwar daraja ko ma zubewarta baki ɗaya a gabansa.

Kunya, halayya ce mai matuƙar daraja. Da yake baka raba rayuwar Bahaushe da addini, ya zo a hadisi cewa: “Kunya tana daga imani”. Wato kenan, imani ne yake haifar da kunya. Idan ya zama mutum bashi da kunya, to imaninsa ya yi ƙaranci.

A Hausance kuma, ana cewa, kunya adon mata. Kenan idan aka samu macen da bata da kunya, komai haskenta a fuska  da kuma tsadar rigunan da ta saka, to a Hausance kuma a al’adance, bata iya kwalliya ba. Shi ya saka a lokutan baya, ba za ka taɓa ganin mata suna gaurayuwa da maza ba. Ko kuma daga nesa ka jiyo muryar mace. Ko kuma ka ga mace ta zo gaban maza tana cin abinci ko kuma ka ga mace ana ta kaura musu da ita da maza wai ita kallabi a tsakanin rawwuna da sauransu ba.

Kunya ce take saka mutum ƙin aikata aikin da idan ya keɓanta zai iya yi amma ya ƙi aikatawa, saboda jin kunyar gamuwarsa da Ubangiji Allah. Idan ma ya yi yunƙurin aikata aikin zai tuna cewa, Allah fa yana kallonsa, sannan kuma idan aka je lahira me zai ce? Ai da kunya. Wannan halayya kuwa, siffa ce ta mumini.

Kara

p>Kara ita ce aikata wani aiki da nufin taimako; aikin yana iya zama kyauta, yafiya, ko magana da sauransu. Shi kuwa taimakon yana iya zama har da kare mutunci. Mu ɗauki kara a matsayin kyauta ga misali. Bahaushe yana da al’ada ta yi wa mutum kyauta domin toshe masa wata kafar da za a iya hango gajiyawarsa ko kuma ya kunyata da sauransu.

Haka nan Bahaushe yakan yafe wa mutum bashi domin asirin wanda ake bi bashin ya rufu. Wannan kara ce.  Kara kuwa a cikin magana ita ce wani yana iya cin zarafin wani ta hanyar zagi, amma idan aka zo wajen sasanto, sai shi wanda aka zaga ɗin ya ɓoye zagin ya ƙi fito da shi fili domin kuɓutar da wanda ake tuhuma daga faɗawa halin wahala.

Kara a cikin aiki kuwa ita ce a riƙa taya juna aiki a lokutan ayyuka gayya. Haka nan kuma koda mutum bai je naka ba, kai sai ka daure ka yi masa kara ka je nasa.

Sadar da Zumunci

Sadar da zumunci a nan na nufin ziyarar ‘yan’uwa da abokan arziƙi. Bahaushe yana cewa: “Zumunci a ƙafa yake”.

Zumunci hali ne mai matuƙar muhimmanci a zamantakewar Bahaushe da kuma addininsa. A al’adance, ta hanyar zumunci ake samun cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. A zamanin baya, duk ayyukan da Bahaushe yake yi akwai zumunci a ciki. Kamawa daga ayyukan gona, gida, da kuma bukukuwa.

Misali, idan muka ɗauki aikin gida, a da can baya, idan Bahaushe zai yi danga a gida, ‘yan’uwa, maƙwabta da abokan arziƙi sukan zo su taya shi, masu haƙa/tono suna yi, masu ɗauko kara daga gona suna yi, masu kafa kara suna yi, masu tanka suna yi, da sauransu. Abin da kawai zai yi shi ne, shi zai dafa abincin da za a ci.

Zumunci, abu ne da ya samu ƙarfafuwa daga addini. Akwai wani hadisi da Annabi (SAW) ya ce: “Ni ne zumunci (Arrahmanu), Shi kuma (Allah), Shi ne Jinƙai (Arrahiimu). Duk wanda ya sadar da ita (Zumunci), zan sadar da shi (Zan sadar da shi da jinƙai). Duk wanda ya yanke ta (Zumunci), na yanke shi”. Baban Dawudu da Tirmizi suka ruwaito shi.

Wadatar Zuci

Wadatar zuci ita ce gamsuwa da abin da mutum yake da shi na dukiya. Abin nufi, mutum ya ji cewa, abin da ya mallaka ya ishe shi, sannan kuma yana buƙatunsa da su ba tare da tunanin cewa, sai ya samu mai yawa ba.

Wannan hali yana kare mutum daga hassada, ƙyashi, rowa sannan kuma ya zama mai kyauta. Haƙuri, shi ne ke haifar da wadatar zuci.

Ya zo hadisi cewa, Annabi (SAW) ya ce: “Yawan dukiya ba shi ne wadata ba. Sai dai, wadata ita ce wadatar zuci”. Abu Huraira ne ya ruwaito wannan hadisin.

Akwai hutu, kwanciyar hankali, rashin shiga rigingimun bashi, rashin cin haram, riƙon amana da sauransu a matsayin ribar ƙafa ga wadatar zuci.

Tawakkali

Tawakalli, ararriyar kalma ce daga Larabci, tushenta kuma shi ne Alƙur’ani. Duka ma’anarta ɗaya ce a Hausancen da kuma Larabcen. Abin da take nufi shi ne dogaro da Allah ko kuma miƙa dukkanin al’amari ga Allah. Da ma’ana ta cewa dukkan abin da ya samu mutum mai daɗi da maras daɗi ya san daga Allah ne.
Ƙasƙantar da kai, juriya, jarumtaka, sadaukar da kai, kyauta,dogaro da kai, ladabi da biyayya, tattali, tsafta, sauƙin kai, da sauransu, duk suna daga ciki kyawawan halaye ababen yabo da Bahaushe yake tarbiyyantar da ɗansa da su.

Manazarta:


Abu Hamza B.D. (2013). Jawabin Darasin Aji Biyu na Babbar Sakandare. Kulliyatul Mu’allim Luggatul Arabiyya, Keffi, Jahar Nassara, Najeriya.

Abu Zakariyya I. (2007). Riyadhus-Salihiina. Darel Fikr Printers, Publishers and Distributors. Beirut-Lebanon.

Ɗan’abubakar U. (Babu Shekara). Buguyatul Muslimina Wal Kifayatul Waa’iziina Wal Mutta’iziin. Maɗaba’ar Alƙali Sharfi Bala, Kano, Najeriya.

Mesel B.D. (2015). Wittengenstein, Meta-Ethics and the Subject Matter of Moral Philosphy Ethical Perspective 22, no 1 (2015): 69 – 98. Center for Ethics, KU Leuven.

Rayner S. (2005). Hume’s Moral Philosphy. Manchester Journal of Philosphy Vol. 14: 185 eu 1, Article 2. An ciro daga shafin http://digital commons.macalester.edu/philo/vol14/iss1/2

Sayyadi A. (2004). Mukhtaril hadithun-nabawi wal hikimatul Muhammadiyya. Maɗaba’ar Alƙali Sharif Bala. Kano, Najeriya.

Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantu 3. University Press PLC. Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Tarbiyya


  Ƙasar Hausa  Musulunci


  Zuwan Turawa


  Bukukuwa


  Wasanni


  Kayan Kiɗan Hausa  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub