Musulunci a Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Musulunci a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Babu wani takaimaman lokacin da za a iya bugun ƙirji a ce shi ne lokacin da Musulunci ya iso Ƙasar Hausa (Fago da Usman, 2010). Kasancewar Ƙasar Hausa yanki ne mai dausayi; yanki mai albarkatun ƙasa, yakan samu fatake masu zuwa kasuwanci daga sassan duniya. Mutanen da suka fi zuwa wannan yanki da nufin kasuwanci akwai Larabawa kuma Musulmi. Cuɗanya da waɗannan mutane da nufin kasuwanci, ta haifar da samuwar addinin Musulunci a wannan yanki ga ɗaiɗaikun mutane.

Yaɗuwar Addinin Musulunci a Ƙasar Hausa

A tsakiyar ƙarni na goma sha biyar kamar yadda ya zo a Fago da Usman (2010), shi ne lokacin da gobarar yaɗuwar addinin Musulunci ta kama a wannan yanki na Ƙasar Hausa; lokacin da sarakuna suka karɓi wannan addini na Musulunci sannan kuma suka saka shi ya zama tsarin gudanar da mulkinsu. A Katsina, sarki Muhammadu Korau, shi ne sarkin da ya fara karɓar addinin Musulunci a hannun Wangarawa sannan kuma ya saka su suka zama limaman masallatai da kuma alƙalan kotuna (Fago da Usman, 2010; Ingawa, 2006).

Sai dai, akwai saɓanin lokacin gudanar da mulki na shi Sarki Muhammadu Korau tsakanin Fago da Usman (2010) da suka ruwaito cewa ya yi mulkinsa ne tsakanin 1445 zuwa 1495 da kuma Kangiwa (2014), Ingawa (2006) da kuma takardar jerin sunayen sarakuna Katsina da muka samu a gidan dagacin Durɓi-ta-Kusheyi da suka kawo cewa Sarki Muhammadu Korau ya yi mulki ne tsakanin 1384 zuwa 1398. Amma duk sun haɗu a kan cewa a zamanin sarki Muhammadu Korau ne Musulunci ya zama addinin gwamnati wanda har ya kai ga gina masallacin da daga ƙarshe ya rikiɗe ya zama babbar jami’ar da take da dangantaka da Jami’ar Sankore ta ƙasar Mali wacce ta zauna a Unguwar Gobarau da ke cikin birnin Katsina.

Haka nan a Kano ma Fago da Usman (2010), sun nan cewa a zamanin sarki Muhammadu Rumfa ne Musulunci ya samu gagarumar ɗaukaka sakamakon zuwan Wangarwa garin na Kano. Sai dai tun kafin wannan lokacin, akwai Musulunci a garin na Kano tun zamanin Sarki Yaji Ɗantsamiya (1349 - 1385) kamar yadda  Wada (2011), Adamu (2007), da kuma NNPC (1979), suka tafi a kai.

A garin Zariya babban birnin masarautar Zazzau, Fago da Usman (2010), sun bayyana cewa Musulunci ya samu gindin zama ne a zamanin sarki Muhammad Rabo (1503-30), duka dai sakamakon bayyanar waɗannan mutane wato Wangarawa.

Tun daga wacan lokaci na shigowar addinin Musulunci da kuma samun karɓuwarsa a matsayin babban addini a Ƙasar Hausa, sai addini da al’adun mutanen wannan yanki na Ƙasar Hausa suka gauraya da na addinin Musulunci da kuma al’adun Larabawa saboda tasirin addinin na Musulunci a Ƙasar Hausa. Wannan magana kuma ta ya yi daidai da ra’ayin Farfesa Ɗangambo (1984), da ya yi maganar cewa harshe abu ne mai rai wanda ke girma da kuma yaɗuwa; yana rayuwa kuma yana mutuwa kwatankwacin yadda masu magana da shi suke rayuwa da kuma mutuwa. Ya ƙara da cewa idan mutane suka canja, to harshensu da al'adunsu ma suna canjawa.

Hakanan Fago da Usman (2010), sun bayyana Ƙasar Hausa da Hausawa a matsayin ƙasar da sauran ƙabilun Najeriya ke yiwa kallon ƙasar Musulunci shi kuma Bahaushe a matsayin Musulmi.

Shi kuwa Farfesa Jinju (1990), cewa ya yi, “Bayan ƙarni na bakwai, Abdulkarim Al-Maghili wanda ya rasu a 1503, ya ziyarci Nijar, da Kano da Katsina yana ta yin wa’azi kuma yana karantar da ‘yan ƙasa”.

Manazarta:


Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Government Press, Kano.

Bunza A.M. (2002). Rubutun Hausa, Yadda Yake da Yadda ake Yin sa don Masu Koyo da Koyarwa. Ibrash Islamic Publication Centre L.T.D., Suru-Lere, Lagos-Najeriya.

Ɗangambo A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancisa ga Rayuwar Hausawa. Maɗaba’ar Kamfanin ‘Triumph’ Gidan Sa’adu Zungur, Kano.

Fago S.I. da Usman Y.B. (2010). Issues in the Impact of Islam on Hausa Land in the 21st Century. The Nigerian Academic Forum Ɓolume 19 No. 2 Novɓember, 2010.

Jinju M.H. (1990). Garkuwar Hausa da Tafarkin Ci Gaba. Fisbas Media Services Publications, Kaduna-Najeriya.

Yahaya I.Y., Zariya M.S., Gusau S.M. da ‘Yar’aduwa T.M (1992). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Qananan Makarantun Sakandire, Littafi na Uku. University Press PLC, Ibadan-Nigeria.

Wada M. (2011). History of Imamship of Kano. Published by: Tunlad Prints & Publishing Coy, No. 27/32, Beirut Road, Kano.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Musulunci


    Ƙasar Hausa



    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub