Sana'ar Noma

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'ar Noma


Gabatarwa

Noma babbar sana’a ce a ƙasar Hausa (Madauci, Isa da Daura, 1968), ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba, Yakasai (1989). Sana'a ce da kowane gida ake yin ta musamman a karkara. Sana’a ce da ta girmi kowace irin sana’a a ƙasar Hausa da ma duniya baki ɗaya, saboda wannan dalilin ne ma ya saka masu iya magana suke yi wa sana’ar noma kirari da ‘Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras’. Asalin wannan sana’a yana komawa tun farkon samun halitta a doron wannan duniyar. Wato kenan ana iya cewa tun saukowar Adamu da Hauwa cikin duniya (Durumin Iya, 2006).

Alhassan, Musa, da Zarruƙ (1982), sun bayyana noma a matsayin tonon ƙasa a fitar da amfaninta ta hanyar zafe ta, da zankaɗe ta, da yin shuke-shuke a bayanta.

Huɗa Da Galma

Kayan Aiki

 1. Fartanya: fartanya ita ce babban makami ko kayan aikin gudanar da sana'ar noma, tana da matuƙar muhimmanci a wannan sana’a. Da ita ake bi kunya, kunya ana sare dukkan wata ciyawar da ba a buƙata a gona. Fartanya kala uku ce: hauya, dungura ƙota da kuma fartanya.

 2. Fartanya

 3. Sungumi: shi ne makamin da ake amfani da shi wajen saran shuka; wato da shi ake sara ramin da za a yi shuka. Yana da baki irin na magirbi, sai dai ƙotarsa doguwa ce wacce takusan tsayin mutum.
 4. Magirbi: magirbi da shi ake sassabe, da kuma girbin kayan amfanin gona kamar irin su dawa, gero, maiwa, da sauran dangoginsu waɗanda suke yin dogon kara a tsaye.

 5. Magirbi

 6. Gatari: Gatari shi ne makamin da ake amfani da shi wajen sare icen da ya girma a gona don samun filin gona.

 7. Gatari

 8. Adda: makami ce da ake amfani da ita wajen sara. Akan sare itatuwa ko ciyawa da ita, haka nan ma akan yi girbi da ita.

 9. Adda

 10. Lauje: ana amfani da lauje wajen shuci, wato yankan ciyawar da ke da tsayi. Sannan kuma da shi ake yankan shinkafa, alkama, da sauransu.

 11. Lauje

 12. Wuƙa: Ana amfani da wuƙa wajen yankan kayan amfani da suka haɗa da kuɓewa, yankan kan gero bayan an girbe, yankan kaba, da sauransu.
 13. Garma/Galma: Ana amfani da garma ko galma wajen yin huɗa.
 14. Ashasha: Nau’ i ce ta garma da ake amfani da ita wajen noma ta hanyar rage girman kunya, ita takan burkuce kwarin kunya ne, sannan kuma ta rage faɗin kunyar, ta yadda mai aiki zai ji sauƙin gudanar da noma. A wasu guraren ma sai dai kawai ya ɗaga ciyawar ya karkaɗe ƙasar jikinta.
 15. Manjagara: da shi ake sharar gona. Bayan an sassabe tushiya da sauran abubuwan da ba a so a lokacin rani kafin faɗuwar damina, to kuma sai a saka manjagara a share sararin gonar a ƙone.
 16. Igiya: Igiya ma ɗaya ce daga cikin kayan aikin gona wacce ake amfani da ita wajen ɗaure kayan amfanin gona da aka girba, kamar damin dawa, gero, da sauransu.

Noman Hauya

Kayan da ake Nomawa

Kayan Abinci:

Dawa, gero, maiwa, shinkafa, gyaɗa, auduga, wake, masara, alkama, acca, ibiro, riɗi, waken suya,  rogo, dankali, makani, da sauransu.


Gyaɗa Mai Ɓawo

Kayan Marmari:

Gwaba, gwanda, ayaba, rake, maruci, yalo, ɗata, gauta, mangwaro, kankana, dabino, da sauransu.


Gwanda

Kayan Miya:

Barkono, albasa, tumatir, citta, kabewa, gurji, kuɓewa, da sauransu.

Ganyayyaki:

Lamsir, rama, zogale, yakuwa, alayyahu, ayoyo, shuwaka, zogale da sauransu.

Girbi

Manazarta:


Alhassan A., Musa U.I., da Zarruƙ R.M. (1982). Zaman Hausawa Don Makarantun Gaba da Firmare. Northern Publishing Company, Zaria-Nigeria.

Durumin Iya M.A. (2006). Tasirin Kimiyya da Ƙere-Ƙeren Zamani a kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. KABS Printing Services (NIG), Durumin Iya, Kano-Nigeria.

Madauci I., Isa Y., da Daura B. (1968). Hausa Customs. Northern Publishing Company, Zaria-Nigeria.

Yakasai K. I. (Babu shekarar bugu). A San Mutum A Kan Cinikinsa (Babu sunan maɗaba’a).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub