Tarbiyya a Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko  

Tarbiyya a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Kalmar tarbiyya, ararriyar kalma ce daga Larabci (التربية aka Hausantar da ita. Kalma ce magamaiya, wacce ke iya ɗaukar ma’ana ta renon jikin yaro; hanyoyin kyautata ruhi da kuma koyar da kyakkyawar cuɗanya da jama’a. Abin da ake nufi a nan shi ne cewa, tarbiyya ta shafi gangar jiki, ruhi da kuma yadda mutum yake cuɗanya da sauran jama’a, a al’ummance da kuma ɗaiɗaiku.

Ƙololin buƙatar tarbiyya ita ce gina cikakken mutum mai amfanar da kansa da kuna waninsa.

Bisa la’akari da wannan faffaɗar ma’ana da wannan kalma take da ita, rubutun zai taƙaitu ne wajen yin magana a kan abin da ya shafi ruhi da kuma cuɗanya. Zai yi magana bakin gwargwado a kan ma’anar tarbiyya, manufarta, amfaninta, masu bayar da ita, jerin wasu kyawawan halaye da kuma yadda Bahaushe yake bayar da tasa tarbiyyar, da sauransu bakin gwargwadon iyawa.

Ma’anar Tarbiyya

Saboda zamowar kalmar tarbiyya mai tushe a Larabci, zan kawo ma’anarta a Larabce da cewa, “Ita ce ayyukan ɗaukakowar halittu, wato ƙarawa mutum mutumtaka domin ya samu kaiwa cikakkiyar daraja matabacciya a jiki da aiki da ruhi da kuma cuɗanya”, Abu Hamza (2013). Daga wannan ma’ana za mu iya fahimtar cewa, tarbiyya reno ce. Saboda dukkan abubuwan nan da aka ambata suna ƙunshe cikin reno. Shi kuwa reno ana yin sa ne mataki-mataki. Sai dai ya fi zafi a tsakanin ranar farko ta haihuwa zuwa shekara uku. A wannan tsakanin komai yi wa mutum ake yi.  Ɗawainiyoyin suna fara raguwa ne bayan an yaye mutum wato daga watanni 15 na haihuwa zuwa shekaru 2. Daga wannan mataki yawancin yara sukan fara yi wa kawukansu wasu abubuwan kamar ci da sha da sauran ƙananan abubuwan rayuwa.

Daga wannan mataki na yaye kuma, sai a shiga kiwonsa, da ma’ana ta lura da zirga-zirgarsa ƙut-da-ƙut har zuwa kamar shekaru 5 ko 6, idan zai kai kansa mahallaka ko dai a ce da shi bari, ko kuma a je a ɗauke shi ko a janye shi da sauransu.

Idan ya haura shida kuma, to ya fara kai wa matakin da zai fara cuɗanya da wajen gida, sai kuma ya shiga makaranta. A makarantar ma renonsa ake yi, saboda a koyar da shi ne alaƙoƙin da suka shafi rayuwarsa ta duniya da kuma ta lahira, iya tsawon karatunsa da ma rayuwar baki ɗaya.

Saboda haka idan muka koma kan waccar ma’ana ta tarbiyya muka ciro kalmomin cewa, ayyuka ne da ke ɗaukaka halitta, za mu gan su cikin wannan ɗan taƙaitaccen bayani game da reno da na yi.

Ana kuma iya cewa, tarbiyya ita ce horas da yaro kyawawan halaye domin ya zama mutum nagari. Ko kuma a ce, hanya ce ta nuna wa yaro yadda zai tashi da kyawawan halaye ababen yabo a cikin jama’a.

Manufar Tarbiyya

Babbar manufar tarbiyya ita ce samar da mutum mai kyawawan halaye ababen yabo domin ya zama mai amfanar da kansa da kuma waninsa.

Amfanin Tarbiyya

Amfanin tarbiyya ba zai ƙidayu ba, amfaninta na ƙarshe; wato maƙurar amfanin nata shi ne mutum ya samu kansa a gidan Aljana a lahira, a nan duniya kuma ya zama son kowa, ƙin wanda bai samu ba.

Waɗannan gajiyoyi da za a ci; duniya da lahira, su ne maƙura, sai kuma wasu ɗaiɗaikun abubuwa da zan lissafo kamar haka:

  1. Tsarkake Halaye: Tarbiyya tana tsarkake halayen mutum ya zama mai kyawawan halaye.
  2. Sauƙin Rayuwa: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya rayu, rayuwa mai sauƙi. Saboda zamowarsa mai wadatar zuci.
  3. Farin Ciki: Mutum mai cikakkiyar tarbiyya akan same shi cikin annashuwa a mafiya yawan lokutansa. Saboda koda wani abu can gefe ya ɓata masa rai, to yasan idan ya zo yin hulɗa da wani wanda abin bai shafe shi ba, sai ya danne wancan ɗacin a ransa shi kaɗai.
  4. Girma da Ɗaukaka: Kyakkyawar tarbiyya tana ɗaukaka darajar mutum a idon mutane a nan duniya, haka nan ma a wajen Ubangiji Mai Girma da Buwaya.
  5. Kwarjini: Kyakkyawar tarbiyya tana saka mutum ya zama mai kwarjini.

Matakan Bayar da Tarbiyya

Akwai matakai ko hanyoyi da ake bi wajen bayar da tarbiyya da suka haɗa da nuni, lura, umarni da kuma hani.

  1. Nuni: Abin da ake nufi da nuni a nan shi ne aikata aiki a aikace, wanda daga nan shi wanda ake tarbiyantarwa zai gani ya koya. Tirƙashi, masu iya magana sun ce; “Idan mutum ya ce zai baka riga, to duba ta jikinsa”. Wannan magana ta zo daidai da faɗin Larabawa cewa; “Maras abu baya bayar da shi”. Saboda haka dole ne mai bayar da tarbiyya ya zama mai tarbiyya.

    Wannan hanya ta bayar da tarbiyya ita ce mafi tasiri da kuma muhimmanci wajen bayar da tarbiyya. Saboda haka dole ne masu bayar da tarbiyya; iyaye, malaman makaranta da sauran jama’a suma su zama masu tarbiyya. Misali, dole iyaye su zama masu tsafta a aikace, kafin su dasa halin tsafta a zukatan ‘ya’yansu. Idan yaro ya tashi ya ga iyayensa suna share gida tsaf-tsaf, basa barin kwanon abinci da dauɗa, basa jefar da sutura ko’ina a ciki da wajen ɗaki, to a haka shi ma zai girma mai kula da tsafta. Kuma zai tashi shi tsafta ya sani bai san ƙazanta ba. Saboda haka da zarar ya fara zuwa makaranta malaman makaranta ba za su wahala da shi ba.

  2. Umarni da Hani (Kwaɓa): Umarni shi ne a riƙa gaya wa yaro yi kaza. Misali, idan yaro ya tsoma hannun hagu cikin kwanon abinci, ko ya riƙe abinci da hannun hagu zai kai bakinsa, sai a gaya masa cewa, wannan ba shi ne hannun cin abinci ba, ga na cin abinci nan. Da haka zai gane hannun dama dana hagu.
  3. Shi kuwa hani shi ne kore abu. A wannan gaɓar kuma yana nufin kare ko dakatar da yaro daga aikata aikin da ba mai kyau ba. A cikin wannan misalin dana kawo a sama, akwai gaurayen hani da kuma umarni. Yaro ya tsoma hannun hagu domin cin abinci, sai aka hana shi; wato aka dakatar da shi daga cigaba da amfani da hannun hagu. Sannan aka gaya masa; wato aka umarce shi da amfani da hannun dama.

  4. Lura/Kula: Lura ko kula, suna ɗaukar ma’anar saka ido a kan kai-komo na yaro; wato zirga-zirgar yara. Wannan hanya ta lura, cikamakonta shi ne kwaɓa. A nan, iyaye za su saka ido sosai game da zirga-zirgar ‘ya’yansu, duk lokacin da suka ga wata baƙuwar halayya maras kyau, sai su yi maza-maza su ɗauki matakin da ya dace tun kafin ta zama jiki.

    Da zarar yaro ya fara fita wajen gida domin zuwa makaranta; wato daga shekaru uku zuwa sama, to fa dole iyaye su riƙa lura da shi sosai, saboda yanzu kuma ya je ya gwamutsa da sauran yara daga gidaje barkatai. Saboda haka idan iyaye basu saka lura ba, to tarbiyyar ‘ya’yansu sai ta koma barkatai.

Manazarta:


Abu Hamza B.D. (2013). Jawabin Darasin Aji Biyu na Babbar Sakandare. Kulliyatul Mu’allim Luggatul Arabiyya, Keffi, Jahar Nassara, Najeriya.

Abu Zakariyya I. (2007). Riyadhus-Salihiina. Darel Fikr Printers, Publishers and Distributors. Beirut-Lebanon.

Ɗan’abubakar U. (Babu Shekara). Buguyatul Muslimina Wal Kifayatul Waa’iziina Wal Mutta’iziin. Maɗaba’ar Alƙali Sharfi Bala, Kano, Najeriya.

Mesel B.D. (2015). Wittengenstein, Meta-Ethics and the Subject Matter of Moral Philosphy Ethical Perspective 22, no 1 (2015): 69 – 98. Center for Ethics, KU Leuven.

Rayner S. (2005). Hume’s Moral Philosphy. Manchester Journal of Philosphy Vol. 14: 185 eu 1, Article 2. An ciro daga shafin http://digital commons.macalester.edu/philo/vol14/iss1/2

Sayyadi A. (2004). Mukhtaril hadithun-nabawi wal hikimatul Muhammadiyya. Maɗaba’ar Alƙali Sharif Bala. Kano, Najeriya.

Yahaya, Zariya, Gusau da ‘Yar’aduwa (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantu 3. University Press PLC. Ibadan-Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Tarbiyya


    Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub