Tsumburbura Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Bautar Tsumburbura a Kano


Gabatarwa

Tsumbubura suna ne na gunki; wata itaciya mai suna Shamus (NNPC, 2007). Shi kuwa Sallau (2013), cewa ya yi aljani ne. Wannan gunki ko aljani ya taɓa zama abin bauta a wajen Maguzawan da suka zauni Kano a can zamanin baya tun kafin zuwan Musulunci cikin Ƙasar Hausa baki ɗaya. labarin wannan bauta ya fara fitowa a zamanin Dala, wanda ya fara zama a kan Dutsen Dala shi da matansa da ‘ya’yansa. Sai dai, an fi sanin komai dangane da wannan bauta a zamanin Barbushe, wanda ya shugabanci wannan tsafi na tsawon lokaci wanda har ta kai ga yana da wakilai a Kano da kewaye.

Asali

Ana danganta asalin bautar Tsimbirbira da Dala. Saboda shi ne farkon wanda yake sanar da jama’a dukkan abubuwan da tsafin ya faɗa. Sannan kuma ta hanyarsa jama’a suke tsanantuwa zuwa ga wannan tsafi nasu.

Daga baya kuma; bayan mutuwar shi Dala, sai jikansa Barbushe ya gaje shi. Marubuta tarihin Kano sun nuna cewa duk wanda ya shiga wanann ɗaki na gunki a bayan mutuwar Dala da kuma kafin tasowar Barbushe mutuwa yake yi. Amma da abin ya zo kan Barbushe sais hi ya shiga, kuma ya dace tsafin ya karɓe shi. Saboda haka a tsawon zamanin Barbushe dukkan wasu abubuwa da suka dangancin wannan tsafi suka fi fitowa fili ga jama’a.

Dala da Barbushe dukkaninsu sun rayu a saman Dutsen dala, gurin da ɗakin wannan tsafi nasu yake. Kuma dukkansu basa saukowa ƙasan dutsen sai shekarar tsafinsu ta zagayo. Kenan, daga shekara sai shekara suke saukowa. Idan suka sauko sukan yi wa jama’ar da suka taru jagoranci zuwa ga ɗakin wannan tsafi a yi dukkan abubuwan da za a yi daga ƙarshe kuma kowa ya kama gabansa.

Gunkin Tsumburbura

Wannan gunki na Tsumburbura; wanda ka iya zama itaciya mai suna Shamus ko aljani ko kuma duka biyun, a kewaye yake cikin bukka a saman Dutsen Dala. Sannan kuma aka kawo wani mutum aka ajiye a ciki aka bashi jar macijiya yake riƙe da ita dimin-da’iman.

Wannan gunki shi Maguzawa suka bautawa. Sun yarda cewa shi yake arzuta su, yake kare su daga masifu sannan kuma yake sanar da su dukkan abubuwan da za su faru a shekara mai gabatowa alheri ko sharri.

Yadda Aka Bautawa Tsumburbura

Ana bautawa wannan gunki ta hanyar yanka na’ukan dabbobi da tsuntsaye baƙaƙe a matsayin hidima ga aljanun da ke tare da wannan itaciya ko kuma shi aljanin kai tsaye kamar yadda aka ambata da farko.

A duk shekarar bauta idan ta gewayo, mutanen da ke Kano da kewayenta sukan taru a gindin Dutsen Dala a iya tsawon rana har zuwa dare kwatankwacin sallar Lisha. Idan lokacin ya yi, sai shi Barbushe; wanda ya gaji Dala ya sauko daga saman Dutsen ya ce da mutanensa: “Babban Jimina aka sa mun gama karagaga laya Tsumburbura”. Su kuma mutanen sai su amsa masa da cewa:  “Ga Tsumburbura Kanawa, ga wajen Dala”. Kamar yadda ya zo a NNPC (2007).

Daga nan sai ya yi musu jagoranci su hau kan dutsen su tsaya a gindin bukkar da tsafin nasu yake ciki. Sannan su yayyanka abubuwan yankan da suka zo da su. Wasu su yanka baƙaƙen kaji, wasu baƙaƙen bunsuraye, wasu baƙaƙen jakai da sauransu. Daga nan kuma sai shi Barbushe ya shiga cikin ɗakin shi kaɗai; idan ban da shi babu wanda yake shiga cikin ɗakin. An ce duk wanda ya shiga mutuwa yake yi, sai shi kaɗai. Yana cikin ɗakin yana cewa: “Ni magajin Dala, da kun ƙi da kun so ku bini ba ra’ayi ba”. Sai su kuma su riƙa amsa masa da cewa: “Mai gida bisa dutse, ubangijin mama, bi mun bi ka ba ra’ayi”. Haka za su yi ta faɗin wannan kalmomi suna gewaya ɗakin har zuwa hudowar alfijir. Sannan kuma sai su tsaya su yi tsirara su ci abinci, NNPC (2007).

Daga ƙarshe sai Barbushe ya fito daga wannan ɗaki ya basu labarin duk abubuwan da za su gudana a shekara mai zuwa. Sai kuma kowa ya sauko daga kan dutsen ya kama gabansa sai kuma wata shekarar idan ta zagayo.

Wannan sha’anin bauta shi ne abin da yake haɗa Barbushe da jama’arsa a waje guda kuma a shekara-shekara. Amma duk da haka yana da wakilai a sauran sassan Kano da suka haɗa da: Gunzago ko Tungazu wanda ke wakiltar yankin Gwauron Dutse; Ɗanburu, wakilin Jigirya; Jandamisa, wakilin Magwan; Hamɓarau, wakilin Tanagar da kuma Gumburjado ko Gumbari Jada mai wakiltar Fanisau, shi ɗa ne ga Nisau (NNPC, 2007; Sallau, 2013).

Ƙarshen Bautar Tsumburbura

Tun wani lokacin can a baya, a ɗaya daga cikin irin wannan haɗuwa da Maguzawa suke yi a Dutsen Dala domin bauta wa Tsumburbura, shugabansu Dala ya sanar da su cewa, wani lokaci zai zo nan gaba, da wani mutum zai zo ya kawar da tarihinsu da gunkinsu. Wannan magana ta bai wa Maguzawa mamaki matuƙa, har suka kada baki suka ce: “Ashe yanzu akwai wani mutum da zai zo ya kawar da tarihinmu ya shimfiɗa nasa a wannan gari?” Dala ya amsa musu da cewa lallai haka ne kuma gunkinsu ya sanar da shi, babu makawa sai wannan abu ya faru ko a su, ko kuma a jikokinsu. Saboda haka suka yarda saboda dogaronsu da cewa gunkinsu baya ƙarya.

Zuwan Bagauda Kano, shi ne abin da ya kafa tubalin gusar da wannan bauta ta Tsumburbura. Shi kansa Bagauda ya fara kashe manya-manyan Maguzawa kamar irin su Jankare ko Jan-Kare.

Daga ƙarshe, sarkin Kano na tara, Tsamiya Ɗan Shekarau (1307 – 1348), shi ya yaƙi Maguzawa ya rushe gurin bautar tasu ya kuma sare bishiyar da ke ciki sannan ya kori mutumin da ke riƙe da jar macijiyar tsafin da ke riƙe a hannunsa.

Da hawansa sarauta ya aika musu saƙo cewa tsakaninsu da shi sai yaƙi. Aka ce hankalinsu ya yi matuƙar tashi. Suka nemi yin sulhu da shi ya ƙi. Suka nemi sani daga shugaban tsafinsu, ya sake jaddada musu maganar da Dala ya gaya wa kakanin-kakaninsu cewa, su za a rinjaya. Saboda haka dukkan Maguzawan da ke Kano da kewaye suka tattaru a gindin wannan dutse da kayan yaƙi iri-iri. Da sarki ya iso suka tare shi suka ce bai isa kai wa gindin wannan dutse ba. Sarki ya waiga ya kira sarkin yaƙinsa da cewa, “Ina Bajere”, da jin haka shi kuma Bajere ya yi kukan kura ya tsunduma cikin Maguzawa, ya hau su da sara da suka, yaƙi ya kaure, har sai da ya ratsa su ya kai ga wannan bukka, ya shiga cikinta, ya soke wannan mutumi mai riƙe da macijiya. Da mutumin nan ya ji sara sai ya ruga ihu, abin da ya sabauta fitar hayaƙi daga bakinsa; hayaƙin da sai da ya cika sararin samaniyar Kano (Ta wancan lokacin). Shi kuma mutumin ya fita da gudu ya nufi Ƙofar Ruwa, ya faɗa cikin ruwan. Sarki da tawagarsa suka bishi. Ya fita ta Ɗanƙwai. Su kuma sauran jama’ar suka tarwatse sai ɗan abin da ba za a rasa ba. Wannan shi ne abin da ya kawo ƙarshe waccar bauta ta Tsumburbura.

Manazarta:


Wazirin Kano A. A. (1978). Kano ta Dabo Cigari. The Northern Nigerian Publishing Company LTD, Zaria, Kaduna-Nigeria.

NNPC (2009). Hausawa da Maƙwabtansu. The Northern Nigerian Publishing Company LTD, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Sallau B. A. (2013). Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani. Ahmadu Bello University Press Limited, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Ƙasar Hausa  Musulunci


  Zuwan Turawa


  Tarbiyya


  Bukukuwa


  Wasanni


  Kayan Kiɗan Hausa  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub