Zamantakewa a Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zamantakewa a Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Zamantakewa a nan na nufin yanayi ko tsarin zaman Bahaushe a al’ummance. Wannan kan-jawabi, wato Zamantakewa, darasi ne mai faɗi, wanda ya tattaro dukkan wani abu da za a iya faɗa game da yanayi da kuma tsarin yadda Bahaushe yake zamansa na rayuwar yau-da-kullum da ya shafi jagoranci da kuma cuɗanya tun daga ƙaramin mataki har zuwa Babba.

Tsarin zaman Bahaushe, cike yake da jagoranci da taimakon juna tun daga gida har zuwa kan sarki. Mafi ƙanƙantar yanki na zaman Bahaushe shi ne gida zaman mutum ɗaya; wanda yake da miji da mata su ne masominsa.

Wannan rubutu da mai karatu yake karantawa, zai yi magana ne iya bakin ƙoƙari game da zaman Bahauhse ta fuskacin iyali, jagoranci da kuma cuɗanya ta hanyar jeranto matsayin da mutane suke da shi daga na ƙasa zuwa na sama, tare kuma da siffanta irin gidajen da Bahaushe yake da daga ƙarami zuwa babba, sannan kuma da siffanta irin cuɗanyar Bahaushe ta fuskacin taimakon juna.

Ƙaramin Gida

Ƙaramin gida, shi ne yanki mafi ƙanƙanta a yanayin zamantakewar Bahaushe, shi ne gidan da yake ɗauke da miji da mata kawai; waɗanda kuma su ne tushe ko tubalin gina iyali. Yawanci a Ƙasar Hausa a zamanin baya, ana samun irin waɗannan gidaje ne a cikin gandu.

Sannu a hankali irin wannan gida yake bunƙasa ya zama babban gida ko kuma gandu. Maigida, shi ne jagora a wannan gida.

Gandu

Gandu shi ne babban gida a Hausance. Shi kuwa babban gida shi ne gidaje a cikin gida. Gida ne makeke guda ɗaya wanda idan aka shiga cikinsa za a samu wasu gidajen, mafi ƙaranci guda biyu a cikinsa. Komai yawan jama’ar gandu, akan samu cewa tushensu ɗaya ne. Tushe a nan na nufin asali. Wato zuriya guda.

A irin waɗannan gidaje ake samun zuriya ko haula. Gida ne da ya tattara kaka, iyaye, baffani, yayye, ƙanne da kuma ‘ya’yan bafannin a guri guda.

Kowane gida guda ɗaya da yake cikin gandu, zaman kansa yake yi; da ma’ana ta yana da ɗakuna da kuma ban-ɗaki wasu lokutan ma da madafa a cikinsa. Kuma ana samun irin waɗannan gidaje a karkara har zuwa yau ɗin nan (28/9/2018) da nake yin wannan rubutun. Abin da kawai ya bambanta na daurin da kuma na wannan zamanin shi ne cewa, a yau za ka taras kowa a gidan gashin kansa yake ci. Amma da can baya kuwa, tukunya ɗaya ake ɗorawa.

Babban jagora a wanna gida shi ne namiji mafi yawan shekaru. Idan ya rasu; da ma’ana ta ya mutu, to mai binsa a shekaru, shi zai cigaba da jan ragamar gidan.

Dukkan sauran jama’ar gidan, sukan je gonar gandu su yi noma, sannan kuma su, mutanen gida, ana ware musu ranar Juma’a da kuma ƙarin wata rana wacce ita take zama ranar kasuwar garin, su riƙa zuwa tasu gonar suna noma wacce ake kiranta da gawaina/gayauna. Dukkan abubuwan da aka noma a gonar gandu, to shi za a riƙa dafawa a babbar tunkunyar gida. Idan aka samu tattaruwar irin waɗannan gidaje, sai su samar da unguwa.

Shi uban gandu, wato jagoran gida, shi ne alhakin kula da al’amuran ciki da wajen gida ya rataya a wuyansa. Shi ne mai bayar da aure a gidan sannan kuma shi ne mai karɓowa, shi ne mai sasanta tsakanin duk waɗanda suka samu saɓani a tsakani da sauransu. Maganarsa ita ce sama da maganar kowa a wannan gidan.

Unguwa

Haɗuwar ɗaiɗaikun gidaje waɗanda ka iya zama gandu ko kuma ƙaramin gida, da yawa a waje guda shi ke samar da unguwa. Yawancin unguwannin Bahaushe musamman a karkara, sukan kasance ‘yan’uwan juna ne. Koda tushe bai zama ɗaya ba, auratayya takan haɗa wannan gidan da wancan.

Mai Unguwa shi ne yake shugabancin unguwa. Ana kuma naɗa mai unguwa ne a sabuwar unguwa ta hanyar la’akari da namiji mafi dattako da shekaru a unguwa. Daga kansa kuma sai abin ya zama gado.

Dagaci ne yake naɗa mai unguwa. Amma kafin naɗin nasa sai ya tuntuɓi sauran dattawan unguwa. Daga lokacin da aka naɗa wannan mai unguwa, shi yake zama wakilin dagaci a wajen mutanensa. Sannan kuma dai shi ne idon hukuma a wannan unguwa. Duk wata hulɗa da kuma isar da saƙonni da hukuma take son yi da jama’ar wannan unguwa, to ta hannunsa za a yi.

Akwai kuma nau’in unguwannin da ake kira ƙauye. Irin waɗannan unguwanni su ne gidaje ɗai-ɗai da suke a cikin daji.

Gari

Haɗuwar unguwanni da yawa a waje guda shi yake samar da gari. Shi kuma gari, dagaci ne yake jagorancinsa. Matsayin dagaci shi ne kamar matsayin kansila a yanzu.

Ana naɗa dagaci ne a matakin farko ta hanyar samun dattijo mai hankali daga cikin dattijan gari, wanda kuma jama’ar garin suke girmamawa, mai haƙuri da kawaici a naɗa shi a matsayin dagaci tare da goyon bayan sauran dattawan da ke wannan gari. Idan kuma wannan dattijo ya rasu, to sai ‘ya’yansa su gaje shi idan akwai. Dagan sarautar ta zama gado.

Dagaci shi ne idon hukuma a garinsa. A duk lokacin da hukuma take son yin hulɗa da jama’ar garin baki ɗaya, to ta hannunsa ake bi, shi kuma sai ya miƙa saƙon zuwa ga masu unguwanninsa.

Gunduma

Gunduma yanki ce da ta tattara garuruwa, ƙauyuka da unguwanni daban-daban a ƙarƙashinta. Ana kiranta kuma da ƙasa, saboda kasancewarta yanki mai faɗi. Hakimi shi ne ke jagorancin gunduma. Gunduma ita ce kwatankwacin ƙaramar hukuma a yanzu. Matsayin hakimi kuma shi ne kamar matsayin shugaban ƙaramar hukuma wato ciyaman.

Wannan kujera ta hakimi kuwa ba a gadonta. Sarki ne yake naɗa wanda ya so daga cikin ‘ya’yansa da kuma makusantansa. Shi hakimi yana wakiltar sarki ne. Shi kuma dagaci ya wakilce shi, dagaci kuma ya wakiltar da mai unguwa.

Hakimi shi yake zama idon hukuma; wato wakilin sarki a gudunma. Dukkan wani saƙo da sarki yake son isarwa ga jama’a, zai fara tura shi zuwa ga hakimai, su kuma su turawa dagatai, dagatai kuma su turawa masu unguwanni, su kuma kodai su isar da shi kai tsaye ko kuma su isar da shi zuwa ga shuwagabannin gandu. Ya danganta da wane irin saƙo ne.

Masarauta

Masarauta babban yanki ce a ƙasar Hausa. Ana samun masarauta daga haɗakar gundumomi. Sarki, shi ne yake shugabantar masarauta. Ana iya misalta masarauta da jaha, shi kuma sarki kamar gwamna ne. Kyakkyawan misali a nan ita ce Masarautar Kano da ke Tarayyar Najeriya. Jahar Kano tana da ƙananan hukumomi arba’in da huɗu ƙarƙashin shugabancin ciyamomi araba’in da huɗu da gwamna ɗaya, haka ma Masarautar Kano tana da gundumomi arba’in da huɗu ƙarƙashin jagoranci hakimai arba’in da huɗu da kuma sarki guda ɗaya a sama.

Sai dai, Zuwan Turawa da kuma mulkin mallakar da suka gudanar, ya canja wannan tsari. A yanzu kana iya samun jaha guda da sarakuna masu yawa. Misali, idan muka ɗauki jahar Jigawa, tana da Masarautu guda huɗu. Sannan kuma idan muka ɗauki Masarautar Dutse daga cikinsu, za mu samu cewa akwai ƙaramar hukuma ɗaya mai gundumomi da yawa. Misali, ƙaramar hukumar Gwaram, a cikin Jahar Jigawa, tana da gundumomin hakimai sama da biyar a cikinta. Kamar irin su Sara, Gwaram, Fagam da sauransu.

Sarki, shi ne kankat a iya faɗin masarautarsa. Babu maganar wani a saman tasa, idan ya ce e, to e, ne haka ma kuma ‘a’a. Jarumtaka, ita ce ke bayar da wannan kujera ta sarauta daga baya kuma ta zama gado.

Masarauta tana kafuwa ne ta hanyar yaƙi. Sarkin wani gari ne yake fita ya yaƙi wani sarkin, da haka-da-haka har sai ya faɗaɗa ƙasarsa.

Daula

Daula, it ace yankin mafi girma a tsarin sarautar Ƙasar Hausa, kuma masarauta ce wacce take yi wa wasu masautun mulkin-mallaka. Idan ƙarfin masarauta ya kai a ƙarfin yaƙi, to sai ta tafi ta kai hari wasu masautun ta mamaye su ya zama dole su riƙa bata jiziya ko kuma amsa umarnin sarki domin zuwa a yi masa yaƙi a wasu lokutan.

Daular Gobir, ita ce fitacciyar tsohuwar daula a Ƙasar Hausa kafin daga baya Jihadin Shehu Ɗanfodiye ya haɗiye ta. Karyewar daular Gobir a yaƙin ƙarshe da sarkin Muslmi Muhammadu Ballo ya yi a cikin shekarar 1803, shi ne ya kawo sallamawar sauran masarautun da suke binta a wannan Ƙasa ta Hausa da kuma kafuwar sabuwar daular Musulunci ta Shehu Usmanu wacce ita ma Turawa suka danne ta a shekarar 1903.

Cuɗanya

Cuɗanya a nan tana nufin yadda wane da wane suke haɗuwa su gudanar da rayuwarsu ta fuskar mu’amala da ta shafi kamar cinikayya, zaman hira, auratayya, da saurnsu.

A gargajiyance kuma a Hausance, cuɗanyar Bahaushe, cuɗanya ce mai daɗi, wacce take cike da gaskiya da riƙon amana da kuma cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Wannan kalma kuwa ma’anarta ita ce, taimake-ni-in-taimake-ka ko kuma kai tsaye a ce taimakon juna.

Wannan magana kuwa, idan muka waiwaci tarihin rayuwar Bahaushe kafin zuwan Bature za mu ga wannan taimakekeniya a ciki. Misali, akwai wani abu da Bahaushe yake kira aikin gayya. Kai tun ma kafin mu je aikin gayya, idan muka kalli zaman gandu ai za mu ga taimakekeniya a ciki. Idan kuma muka zarce muka kalli aikin gayya, za mu ga cewa, salon aiki ne da ‘yan’uwa da abokan arziƙi ke haɗuwa su taya mutum aiki a gida ko a gona ba tare da ya biya kuɗi ba. Abin da kawai suke buƙata a wajensa shi ne abinci. Wannan kuma ana yinsa ne cikin nishaɗi da annashuwa ta hanyar wasan barkwanci.

Kuma har yanzu, ba a rasa sauran ƙauyuka da karkaru da ake gudanar da irin waɗannan ayyuka na taimakon juna a cikinsu. Wannan al’amari yana haifar da ƙaunar juna a tsakanin jama’a.

Haka nan idan muka ɗauki bikin suna ga misali, za mu ga shima a cike yake da wannan al’ada mai kyau ta taimakon juna a dukkan ɓangarori biyu; ɓangaren mata da kuma ɓangaren maza. A duk lokacin da Bahaushe zai yi sunan ɗansa; da ma’ana ta abin haihuwa mace ko namiji, za ka taras cewa, maza sukan dafa abinci ko kuma su samu ɗanyen abinci su aikawa da mai gida gudunmawarsu saboda sun san mata za su taru a wannan gidan wajen taya ‘yar’uwarsu mace murna. Irin wannan abinci da mazaje ke bayarwa da sunan gudunmawa, su ake dafawa kowa ya ci, ya yi tatul, har ma a bar saura. Haka nan kuma ta ɓangaren mata, suma za ka samu suna ta kai irin tasu gudunmawar da suka haɗa da kayan jarirai dana mai jego.

Idan ma kuma layi ka fito, haka za ka ga ɗan Bahaushe idan ya hangi wani mutum mai shekaru ɗauke da kaya, zai je ya karɓe shi ya kai masa gida domin shi wannan tsoho mai shekaru ya samu hutu da sauransu.

Wannan wata ‘yar walƙiya ce ta rayuwar Bahaushe kafin Bature ya ci shi da yaƙi na ɗan yi maka. Yanzu babu abin da ake gani sai ƙyashi, hassada, gaba, rowa da sauran abubuwan da ke haifar da ƙin juna a tsakanin Hausawa musamman ma a birane wai kuma da sunan cigaba.

Amma fa duk da haka, ko kuma na ce har yanzun, ba a rasa nagartattu kuma cikakkun Hausawa waɗanda ke riƙe da waccar tsohuwar kyakkyawar al’ada a birane da kuma karkarun Ƙasar Hausa a cikin Zamantakewarsu.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Zuwan Turawa


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub