Zuwan Turawa Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zuwan Turawa Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Ɗan'adam, halitta ce mai cuɗanya da juna ba tare da la'akari da yare, shekaru ko jinsi ba. Dalilai da dama sukan iya haifar da wannan cuɗanya. Akwai dalilai na cinikayya, ƙaura daga wannan gari zuwa wancan, mulkin mallaka da sauransu.

Ɓullar Turawa a Ƙasar Hausa, abu ne na lokaci mai tsawo. Saboda tun kafin shigowarsa da nufin mulkin mallaka, akwai cuɗanya tsakanin Turawa da mutanen Ƙasar Hausa a fannin cinikayya, cinikayyar kuma a ciki da wajen Ƙasar Hausa ta hanyar kasuwancin hamada, musamman a shahararriyar kasuwar nan ta duniya da aka fi sani da Gwanja, wacce take garin Salga a yankin Gwanja ta ƙasar Ghana da kuma ƙarin wasu ƙasashe a Afirka ta Arewa.

Wannan rubutu da mai karatu yake karantawa, zai taƙaita magana ne a iya lokacin da Turawa suka shigo Ƙasar ta Hausa da nufin mulkin mallaka bayan sun ci Daular Usmaniya da yaƙi.

Ina sa ran yin magana bakin gwargwado game da abubuwan da suka faru wajen ƙwace daular, cigaban da zuwan Turawa ya kawo da kuma koma-bayan da ya haifar.

Manazarta:


Abubakar A. Y. (2011). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello Uniɓersity Press, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Audu M. S. da Osuala U. S. (2015). The Biritish Conƙuest and Resistance of Sokoto Caliphate, 1897 – 1903: Crisis, Conflict and Resistance. Department of History and International Studies, Federal Uniɓersity Lokoja, Kogi State, Nigeria. Historical Research Letter. Ɓol. 22, 2015, ISSN 2224 – 3178.

Bala A. A. (2015). The Impact of Colonisation in Uprooting Islamic Ploity and Introducing Circularism in Northern Nigeria. Department of Islamic Studies, Faculty of Art and Islamic Studies, Usman Ɗanfodiyo Uniɓersity, Sokoto, Nigeria. E-Proceedings on Arabic Studies and Islamic Ciɓilization, iCASIC 2015 (E-ISBN 978-967-0792-02-6), 9 – 10 March 2015, Kuala Lumpur, Malaysia.

NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu (2). Northern Nigerian Publishing Company, Gaskiya Building, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N. M. (2009). Stories of Dutse Palace, 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.

Rodney W. (1973). How Europe Under Deɓeloped Africa. Bogle-L ‘Ouɓerture Publications, London and Tanzanian Publishing House, Dar-Es-Salam.

Yahaya I. Y., Zariya M. S., Gusau S. M. da ‘Yar’aduwa T. M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun akandire 3. Uniɓersity Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Zarruƙ R. M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B. S. Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Ɗaya. Uniɓersity Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Darrusan Hausa

  • Darrusan Hausa

  • Zuwan Turawa


    Ƙasar Hausa



    Musulunci


    Tarbiyya


    Bukukuwa


    Wasanni


    Kayan Kiɗan Hausa



    Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


    Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



    Sauran Shafukanmu:

    Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub