Ɓullar Turawa Ƙasar Hausa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ɓullar Turawa Ƙasar Hausa


Gabatarwa

Ɓullar Turawa a wannan rubutun tana nufin lokacin da aka ga wulgawar Bature a Ƙasar Hausa, sannan kuma aka tantance suna da kuma shekarar da wannan al'amari ya faru. Wannan kuma abu ne mawuyaci a iya haƙiƙance takamaiman lokacin da Turawan suka fara karakaina a wannan Ƙasa ta Hausa, saboda zamowarta mai albarkar ma'adanai, ingantaccen yanayin da jama'a ke bukata domin rayuwa da sauran abubuwan lura da ma shigowar addinin Musulunci da zuwan Hausawa aikin hajji duk suna daga cikin dalilan da suka janyo yaɗuwar labaran wanzuwar mutane a wannan yanki na Ƙasar Hausa da kuma kwararowar baƙin haure zuwan yankin saboda albarkar da ke malale a cikin ƙasar. Misali, an samu ɓullar Rumawa a cikin Birnin Kano tun kafin bayyanar Bagauda a matsayin sarkin Kano. Unguwar 'Yar'akwa da ke birnin Kano, unguwa ce da ake alaƙanta ta da Rumawa.

Audu da Osuala (2015), sun ruwaito cewa akwai Turawan da suka riƙa karakaina a Ƙasar Hausa tun cikin ƙarni na tara. Akwai kuma wani Bature mai suna Clapperton da ya zo fadar Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo a cikin shekarar 1824 domin ƙulla yarjejeniyar cinikayya a faɗin Daular Usmaniyya wacce duk girman ƙwaryar Ƙasar Hausa take a cikinta. Kamar yadda ya zo a ruwayar Bala (2015). Akwai kuma wani Baturen Jamus mai suna J.F. Schon, wanda shi kuma ya yi tasa dab-dalar a tsakanin 1833 zuwa 1885. Sannan kuma Bath, shima Bature ne daga Ingilishi da ya sake zuwa garin na Sakkwato a cikin shekarar 1853.

Farkon Turawan da suka zo Afirka ta Yamma su ne Fotugalawa, waɗanda suka fara fafutikarsu a shekarun ƙarshe na ƙarni na goma sha biyar. Ba jimawa Sifaniyawa suka biyo bayansu a cikin 1450 zuwa sama. Farfesa Boahen (1986). Ta Afirka ta Arewa Turawa suka san ingantacciyar jemammiyar, turarriyar fatar nan da aka fi sani da Fatar Maroko tun sama da ƙarnoni biyar da suka shuɗe (Tsakan-kanin 1573), wannan fata kuwa daga Hausa (Kano) da Mandiga da ke Arewacin Najeriya da Mali ake samar da ita. Rodney (1973).

Zuwan Abdurrahman Zaite Kano da tawagarsa a zamanin sarkin Kano Ali Yaji (1349 - 1385), suka kawo wannan sana'a ta jimar fata domin samawa ɗalibai hanyar samun abun masarufi.

Manazarta:


Abubakar A. Y. (2011). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello Uniɓersity Press, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Audu M. S. da Osuala U. S. (2015). The Biritish Conƙuest and Resistance of Sokoto Caliphate, 1897 – 1903: Crisis, Conflict and Resistance. Department of History and International Studies, Federal Uniɓersity Lokoja, Kogi State, Nigeria. Historical Research Letter. Ɓol. 22, 2015, ISSN 2224 – 3178.

Bala A. A. (2015). The Impact of Colonisation in Uprooting Islamic Ploity and Introducing Circularism in Northern Nigeria. Department of Islamic Studies, Faculty of Art and Islamic Studies, Usman Ɗanfodiyo Uniɓersity, Sokoto, Nigeria. E-Proceedings on Arabic Studies and Islamic Ciɓilization, iCASIC 2015 (E-ISBN 978-967-0792-02-6), 9 – 10 March 2015, Kuala Lumpur, Malaysia.

NNPC (2007). Hausawa da Maƙwabtansu (2). Northern Nigerian Publishing Company, Gaskiya Building, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Sanusi N. M. (2009). Stories of Dutse Palace, 1421 – 2009. Jigawa State Printing Press, Dutse, Jigawa State, Nigeria.

Rodney W. (1973). How Europe Under Deɓeloped Africa. Bogle-L ‘Ouɓerture Publications, London and Tanzanian Publishing House, Dar-Es-Salam.

Yahaya I. Y., Zariya M. S., Gusau S. M. da ‘Yar’aduwa T. M. (2006). Darrusan Hausa Don Manyan Makarantun akandire 3. Uniɓersity Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Zarruƙ R. M., Kafin Hausa A. A. da Alhassan B. S. Y. (2010). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandire, Littafi na Ɗaya. Uniɓersity Press PLC, Ibadan, Nigeria.

Darrusan Hausa

 • Darrusan Hausa

 • Zuwan Turawa


  Ƙasar Hausa  Musulunci


  Tarbiyya


  Bukukuwa


  Wasanni


  Kayan Kiɗan Hausa  Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


  Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin  Sauran Shafukanmu:

  Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub