Sana'o'in Cikin Kemistiri-Careers in Chmistry

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sana'o'in Cikin Kemistiri (Careers In Chemistry)


Gabatarwa

A darasin rassan kemistiri mun fahimci irin rassansa da kuma amfaninsu ta yadda har cikin harkokin lafiya, kimiyya da fasaha, kimiyyar binciken laifuffuka, da sauran fagagen ilimi masu tarin yawa kemistiri yana bayar da gudunmawa.

A wannan darasi za mu fahimci irin sana’o’in da fannin kemistiri yake samarwa. Darasin da zai bai wa masu tambayar irin ayyukan da za su yi idan suka karanci kemistiri amsa.

Haƙiƙa, kemistiri yana daga cikin darrusan da za a iya cewa da su alheri danƙo ne baya faɗuwa ƙasa banza. Matuƙar dai ɗalibi ya karanci wannan fanni na kemistiri, to ba zai rasa abin yi ba. Sai dai idan dama hasarar kuɗin tara aka yi.

Kalli Wannan bidiyon Domin Qarin haske

Kalmar career, kalmar Turanci ce wadda za a iya yi mata fassara da sana’a ko aikin da mutum ya riƙe a matsayin sana’arsa na lokaci mai tsawo ko kuma tsawon rayuwa baki ɗaya. Shi kuwa kemistiri mun san shi a matsayin fannin kimiyya. Saboda haka idan aka ce careers in chemistry, kamar yadda yake a wannan darasin, to ana nufin sana’o’in da za a iya yi bayan an samu horo a fannin kemistiri ko kuma guraben ayyukan yi da mai kemistiri yake da su a guraren aiki. Kwalejin Gordon da ke jahar Boston ta ƙasar Amurka ta wallafa a shafinta cewa: “Akwai guraben ayyukan yi masu tarin yawa a fannin kemistiri”. “Maganar gaskiya, zaɓuɓɓukan sana’o’i ba za su taɓa ƙarewa ba a fannin kemistiri, duk kuwa da cewa, gwargwadon zurfin karatunka, gwargwadon yawan albashinka. Mai difilomar shekara biyu zai samu kai ne kawai yana wanke-wanken mazubin sinadarai ko kuma tallafawa ɗalibai a ɗakin gwaje-gwaje…”, in ji Ba’amurkiya, Dakta Helmenstine wadda take ƙwararriya a fannin biomedical science.

Zan karkasa wannan darasi zuwa gida uku; da farko zan kawo nau’ukan digirorin da ake yi a fannin kemistiri; sana’o’in da ake yi da kemistiri da kuma rassan kemistiri da sana’o’in da suke koyarwa.

Digirorin Kemistiri

  • Agricultural Chemistry
  • Analytical Chemistry
  •     
  • Biochemistry
  • Biotechnology
  •                
  • Chemical Education
  •       
  • Chemical Engineering
  • Chemical Technology
  •    
  • Food Chemistry
  •            
  • Environmental Chemistry
  • Forensic Chemistry
  •        
  • Geochemistry
  •               
  • Inorganic Chemistry
  • Materials Science
  •           
  • Medicinal Chemistry
  •      
  • Organic Chemistry
  • Physical Chemistry
  •       
  • Oil and Petroleum
  •          
  • Consumer Product Chemistry
  • Polymer Chemistry
  •        
  • Textile Chemistry
  •                   
  • Pulp and Paper Chemistry
  • Water Chemistry
  •           
  • Catalysis
  •                       
  • Hazardous Waste Management

Sunayen Masu Sana'o'in Cikin Kemistry

  • Assayer
  • Astrophysicist
  •      
  • Ballistics Expert
  • Biochemist
  • Cardiologist
  • Chemical Analyst
  • Analytical Chemist
  •                
  • Clinical Chemist
  •         
  • Food Chemist
  • Industrial Chemist
  •                 
  • Inorganic Chemist
  •            
  • Organic Chemist
  • Pharmaceutical Chemist
  •                   
  • Physical Chemist
  •          
  • Police Chemist
  • Pollution Control Chemist
  •    
  • Polymer Chemist
  •                   
  • Production Chemist
  • Dentist
  •                                     
  • Quality Control Chemist
  • Quality Assurance Chemist
  • Research Chemist
  •                  
  • Crime Lab Analyst
  •                  
  • Criminologist
  • Dermatologist
  •                          
  • Dialysis Technician
  •        
  • Environmental Engineer
  • Food and Drug Inspector
  •                  
  • Food Technologist 
  •                  
  • Genetic Engineer
  • Geologist
  •                                
  • Gynecologist
  •                  
  • Hydrographer
  • Industrial Hygienist
  •                 
  • Instrument Designer
  •      
  • Laboratory Assistant
  • Patent Lawyer
  •                        
  • Microbiologist
  •              
  • Neurologist
  • Nanotechnologist
  •                    
  • Obstetrician 
  •                            
  • Opthalmologist
  • Osteopathic Physician
  •             
  • Otolaryngologist
  •            
  • Patent Evaminer
  • Pathologist
  •                              
  • Pediatrician
  •                    
  • Perfumer
  • Pharmacist 
  •                              
  • Pharmaceutical Retailer Pharmacologist
  • Physicist
  •                                  
  • Physician
  •                       
  • Physician, General Practice
  • Physician's Assistant
  •               
  • Proctologist 
  •                  
  • Quality Control Supervisor
  • Quality Assurance Manager 
  •     
  • Researcher    
  •                         
  • Chemical Sales
  • Pharmaceutical Sales
  •               
  • Sanitarian
  •                      
  • Sanitation Inspector
  • Soil Scientist
  •                           
  • Spectroscopist
  •               
  • Publications Supervisor
  • Surgeon Systems Analyst
  •                 
  • Chemistry Teacher
  •                  
  • Chemistry Lecturer
  • Technical Sales
  •                        
  • Technical Writer
  •            
  • Chemical Laboratory Technician
  • Dialysis Technician
  •               
  • Fingerprint Technician
  • Histologic Technician
  • Instrument Repair Technician
  •         
  • Medical Technician
  •      
  • Ophthalmic Laboratory Technician
  • Optical Laboratory Technician
  •       
  • X-ray Technician
  •          
  • Quality Control Technician
  • X-ray Technologist
  •                
  • Forest Products Technologist
  • Hematology Technologist
  • Medical Technologist
  •            
  • Scientific Documents Translator
  • Toxicologist
  •                                      
  • Urologist 
  •                       
  • Water Resources Specialist
  • Nuclear engineer 
  •                     
  • Patent attorney 
  •             
  • Chemistry lab facilitator
  • Surface Chemist
  •                    
  • Development Chemist
  • Synthetic Organic Chemist
  • Medicinal chemist
  •                            
  • organic growth manager
  • Senior scientist
  • Clinical Lab Scientist
  •               
  • Formulation chemist
  •       
  • Data scientist
  • Instruments scientist

Rassan Kemistiri da sana'o'insu

Yanzu za mu koma darasi na biyu mu ɗauko rassan kemistiri mu ga irin sana’’o’in da za a koya aƙarƙashin su

Analytical chemistry

Mendeley (2018); Raise Me (2019), sun bayyana masana wannan fanni na analitikal kemistiri (analytical chemistry), wato analitikal kemists (analytical chemists), a amtsayin mutanen da suke gano tsari (structure), yanayi (nature) da kuma sassan da ke cikin gamayya (composition), domin su tantace adadin kowane jinsin kowane sashe da kuma irin halayyar kowane sashe idan ya cuɗanya da waninsa. Wannan kuma ya haɗa har da magunguna, abinci, da sauran su domin su fahimci irin tasiri da kuma ingancin abun tare kuma da tabbatar da zamowarsa ingantacce domin amfanin ɗan'adam.

Guraren ayyuka: Analitikal kemist za su iya aiki a guraren da suka haɗa da ɗakunan gwaje-gwajen kimiyya; kamfanin harhaɗa magunguna; cibiyoyin tsaro; hukumomin kula da ingancin abinci; makarantu; gidajen abinci; kamfanonin samar da kayan ƙwalan da maƙulashe da sauran su.

Biochemistry

Wanda ya karanta wannan fanni shi ake kira bayokemist (biochemist), wanda kuma Sokanu (2020); New Scientist Jobs (2019); Environmental Science (2020); Biochemical Society (2020), suka siffanta shi a matsayin mutumin da yake nazarin abubuwan da ke faruwa da ƙwayoyin halitta (cells) ta fuskacin sauye-sauyen sinadarai (chemical process); yadda suke sadarwa a tsakanin su (how the cells communicate among themselves) musamman ta fuskacin yaƙi da cuta ko kuma haɓɓakar su; dangantar tsarin (structure) sassan ƙwayar halitta (molecule) da aikinta da kuma yadda ƙwayoyin halitta suke sarrafa abinci da iska da sauran su. 

Guraren Aiki: Bayokemist zai yi aiki a guraren da suka haɗa da fannin aikin gona (agriculture); guraren harkokin abinci (food institutes); fannin ilimi (education); fannin kayan gyara jiki (cosmetics); fannin kimiyyar nazarin laifuffuka (forensic crime research); fannin gano magunguna da haɓɓaka su (drug discovery and development) da sauran su.

Inoganik Kemistiri (Inorganic Chemistry)

State Hygienic Laboratory (2020); Speight (2017); Zip Recruiter (2020), sun siffata inoganik kemist (inorganic chemist) a matsayin mai nazartar ɗabi'un (properties) gaurayayyun sinadaran inoganik (inorganic chemical compound) da suka haɗa da ƙarafuna (metals) da kuma ma'adanai (minerals). Shi ne yake ɗaukar samfurin ma'adani ko ƙarfe ta hanyar amfani da na'urori na musamman sannan ya gudanar da bincike a kan su domin gano sassan sidanaran (molecules), abubuwa (substances) da kuma gaurayayyun abubuwan (mixture) da ke ƙunshe cikinsu.

Guraren Aiki: Kamfanonin haƙar ma’adanai (Mining, Ore, and Metals); kamfanin haɗa fenti (Paint, Pigment, and Coatings); kamfanonin samar da injinan na’urorin laturonics (Microchip); kamfanonin sarrafa roba (Fibers and Plastics) da sauransu.

Oganik Kemistiri (Organic chemistry)

Dakta Helmenstine (2019), ta siffata oganik kemist a matsayin mutumin da yake nazartar mafi ƙanƙantar ɓangaren ƙwayar halitta (molecule) wanda ke ɗauke da sinadarin kabon (carbon) a cikinsa.

Guraren Aiki: Kamfanonin samar da kayayyakin kiwon lafiya (health care companies); kamfanoni harhaɗa magunguna (pharmaceutical); kamfanoni samar da irin noma (crop production), fannin aikin gona (agriculture); kamfanin samar da sinadarai (chemical industries); kamfanonin samar da kayayyakin buƙatun yau-da-kullum (consumer goods) kamar irin su sabulu, kayan shafe-shafe, da saurnsu.

Fisikal Kemsitiri (Physical Chemistry)

Browne (2020), ya siffata masanin wannan fanni na fisikal kemistry (physical chemistry); wato fisikal kemist (physical chemist) a matsayin mutumin da yake da kyakkyawar fahimtar yadda halayen abubuwa suke (how materials behave) da kuma yadda gaurayuwar sinadarai (chemical reactions) take afkuwa (occur) tun daga matakin ɗaiɗaikun ƙwayar zarra da kuma ɓangare-ɓangare na abubuwa.

Guraren aiki: Ɗakunan gwaje-gwaje; kamfanonin samar da softuwayar kwamfuta da dangoginsu; ma’aikatun tsaro; cibiyoyin kare yaɗuwar cututtuka masu yaɗuwa (centres for diseases control and prevention); kamfonin harhaɗa sinadarai (chemical industries); kamfanonin harhaɗa magunguna (pharmaceuticals) da sauransu.

Manazarta:


ACS Chemistry for Life (2020). An ciro a shekarar 2020 dga shafin; https://www.acs.org/content/acs/en/careers/college-to-career/areas-of-chemistry/inorganic-chemistry.html

Biochemical Society (2020). What is biochemistry? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.biochemistry.org/education/careers/becoming-a-bioscientist/what-is-biochemistry/

Browne C. (2020). What Are the Duties of a Physical Chemist? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://work.chron.com/duties-physical-chemist-16755.html

Environmental Science (2020). What is a Biochemist? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.environmentalscience.org/career/biochemist

Gordon College (2020). Careers in Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin, https://www.gordon.edu/page.cfm?ipageid=991&icategoryid=73&

Helmenstine A. M. (2019). Check Out These Chemistry Career Options Before You Get a Degree. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.thoughtco.com/careers-in-chemistry-601963

Indeed (2020). Physical Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.indeed.com/q-Physical-Chemistry-jobs.html

Mendeley (2018). Top 10 Chemistry Jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.mendeley.com/careers/article/top-10-chemistry-jobs/

New Scientist Jobs (2020). Organic Chemistry jobs. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://jobs.newscientist.com/jobs

Ngcareers (2020). Job Prospects and Career Opportunities for Biochemistry Graduates in Nigeria. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://ngcareers.com/course/34/biochemistry

Raise Me (2019). Analytical chemists: Salary, career path, job outlook, education and more. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.raise.me/careers/life-physical-and-social-science/chemists-and-materials-scientists/analytical-chemists

Speight J. G (2017). Inorganic Chemistry. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.sciencedirect.com/topics/earth-and-planetary-sciences/inorganic-chemistry

Sokanu (2020). What does a biochemist do? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.careereɗplorer.com/careers/biochemist/

State Hygienic Laboratory (2020). Inorganic Chemistry. Iowa Laboratories Facility 2220 South Ankeny Boulevard Ankeny, Iowa. An ciro a shekarar 2020 daga shafin: http://www.shl.uiowa.edu/publications/annualreport/2015/ContentPage/ inorganic.xml

Zip Recruiter (2020). What Do Inorganic Chemists Do? An ciro a shekarar 2020 daga shafin: https://www.ziprecruiter.com/e/What-Do-Inorganic-Chemists-Do


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub