Fafutikar Kafa Masarautar Burumawa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Fafutikar Kafa Masarautar Burumawa


Gabatarwa

Yunƙurin danne ‘yanci da kuma binne tarihin Burmawa daga ɓangaren sarkin Kanam, Alhaji Muhammadu Ibrahim, shi ne abinda ya ƙyasta ashanar hura wutar wannan fafutika ta neman kafa masarautar Burum (Masarautar Bogghom), wacce ta fara daga shekarar 1982.

An ɗauki tsawon shekaru 35 (1982 – 2017), ana ɓarje gumi tsakanin ɓangarorin biyu; sarakunan Kanam da kuma Burmawa, ta hanyar amfani da ƙarfin faɗa-a-ji da kuma baje kolin hujjoji da kowane ɗaya daga cikinsu ya ke da su.

Wannan fafutika ta riƙa sauya salo daga wannan mataki zuwa wancan tsakanin masu danniya da kuma waɗanda ake son murƙushewa. Ta yadda a wani lokaci har sai da ta kai ga raunata wasu, salwantar da rayuwar wasu, da kuma ɓarnata dukiya.

Gwamnan Plateau, Solomon Baƙo Lalong, shi ya samu nasarar kawo ƙarshen wannan balahira tsakanin sarautar Kanam da Burumawa, bayan abin ya faskari gwamnonin da suka gabace shi ciki kuma har da sojoji.

Masomi

Shirye-shiryen bikin tabbatar da ƙarin girma da Mai Martaba Sarkin Kanam, Alhaji Muhammadu Ibrahim, OFR ya samu daga sarki mai daraja da biyu zuwa daraja ta ɗaya a shekarar 1982, shi ne masomin wannan fafutika.

Shi sarkin na Kanam, Alhaji Muhammadu Ibrahim, ya fito ne daga zuriyar Kh’n Nang, wacce Turawa suka jirkita ta koma Kanam. Wannan zuriya kuwa tushenta shi ne wani mutum mai suna Muhammadu Maki, wanda shi kuma asalinsa mutumin Kano ne.

Muhammadu Maki da jama’arsa suka je, suka samu Nimman a Dutsen Nimwang; wanda yanzu ya zama garin Namaran, suka zauna tare da shi. Domin a bambance zuriyar Muhammadu Maki da sauran haulolin da ya taras a gurin, sai aka riƙa kiransu da Kh’n Nang, wacce ke da ma’ana ta “daga arewa ci”, ko kuma mu ce “Mutanen arewa” kasantuwar daga arewa suka fito.  Sunan ya jirkice daga Kh’n Nang ya koma Kanam.

Da aka zo shirye-shiryen bikin ƙarin girma da sarkin Kanam ya samu, sai ya rubuta cewa dukkan jama’ar Burumawa da ke wannan yanki daga Kano suka je gurin, a jikin ajandar taro. Kasantuwar, daga cikin manyan baƙin da ya gayyata domin halartar wannan biki nasa akwai marigayi mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero. Sannan kuma ya sauya sunan taken sarautar tasa zuwa Emir, wanda masaratun daular Usmaniya ke amfani da shi. waccar gaɓa ta alaƙanta sauran Burumawa da Kano, ta jirkita tarihin Burumawa baki ɗaya, kasantuwar shi Nimman wanda ya kafa garin Namaran, daga Zinn ya ƙaura zuwa wannan dutse a yawonsa na harbi, ya zauna a gurin, sannu a hankali jama’a suna zuwa suna samunsa har gurin ya zama gari.

Saboda haka, ba tare da jinkiri ba, wasu daga cikin mambobin wannan kwamiti na shirye-shirye suka ƙalubalanci mayar da su Kanawa a tarihance. Dole aka sauya wannan ajandar taro da ta kore dukkan sauran haulolin Burmawa da dangantakar tarihi da Kano in banda tsurar su haular Kanam ɗin. Wannan cece-ku-ce ya faru a cikin watan Fabarairu na shekarar 1983. Shi kuma bikin an gudanar a shi a ranar 9 ga watan Afirilu na shekarar.

Bayan wasu ‘yan kwanaki da yin wannan biki na naɗi, sai wasu ƙusoshi masu kishin yaren Burma, ciki har da wasu tsofaffin ciyamomin ƙaramar hukumar ta Kanam, suka ziyarci sarki, domin yi masa murna da kuma jin yadda aka yi aka haihu a ragaya dangane da zamowarsu Kanawa da kuma yin amfani da taken sarautar Emir a masarautar Kanam wacce take ta Burmawa ce. Sannan kuma da duba yiwuwar shigar da zuriyar kh’an Bogghom da kh’n Tankwal cikin sarautar Kanam.

Wannan lamari ya fusata sarki, inda nan-take ya sheda musu cewa, kakaninsa ne suka ci ƙasar da yaƙi. Sannan kuma ya yi fatali da batun shigar da wata haula cikin majalisarsa tare kuma da jan-kunnensu cewa, maganar ta tsaya a iya nan.

Bayan fitowar wannan tawaga, sai lamari ya canza salo, inda suka je suka zaburantar da digatan zuriyar Burmawa da na Tankwal, suka haɗa ƙarfi da ƙarfe, suka sake komawa fadar sarki, aka sake yin wani zaman a zauren majalisar fadar sarkin. A wannan zama suka nemi ya yi musu bayanin yadda aka yi, aka ci su da yaƙi. Shi kuma sarki ya shaida musu cewa, kakansa mayaƙi ne, lokacin da ya zo ƙasar, sai ya riƙa ɗinkawa wasu ‘yan rawar gargajiya riguna domin alamta al’adunsu, ta haka ya mamaye ƙasar, ya kafa yankin da a yanzu ake kira Kanam. Nan-take suka ƙaryata shi, suka kuma gaya masa asalin kowace zuriya. Batun taken sarauta kuma ya amsa musu da cewa, zamowarsa musulmi ce ta saka ya yi amfani da wannan take na emir.

Daga ƙarshe, suka buƙaci cewa, koda ba zai yi wurgi da wancan taken ba, to ya dace ya mutumta sabuwar dokar ƙananan hukumomi da ta buƙaci kowace masarauta a faɗin Najeriya ta kafa majalisar zaɓen sarki. Sannan kuma, kasantuwar su duka; Kanam da sauransu duk Burumawa ne, ya kamata koda basu samu damar gadar wannan kujera ba, to su zama masu zaɓar sarki. Nan ma dai, sarki ya sake fatali da wannan buƙata, ya ƙuma ɗaga yin taro da su har sai baba-ta-gani.

Bayan wani lokaci, sai ɗaya daga cikin jajirtattun ‘ya’yan Burumawa ya gayawa sarkin Kanam saƙon baka cewa, “Allah ya ja zamanin sarki, ko ka amince da buƙatarmu, ko kar ka amince, mu ba za mu yi ƙasa a guiwa ba wajen neman adalcin kafa masarautar Burum. Koda kuwa wannan fafutika za ta ɗauke mu tsawon shekaru ɗari”. Wannan jawabi, shi ne tubalin kafa fafutikar neman samun masarautar Burumawa, ‘yantacciya daga Kanam.

Turakun Fafutika

Kasantuwar yanzu an shata layi tsakanin sarakunan Kanam da Burumawa, an kuma buɗe sabon shafin fafutikar kafuwar masarautar Bogghom; ‘yantacciya daga Kanam. To dole wannan fafutika ta samu wasu ginshiƙai masu ƙwari da za ta ɗoru a kansu. Waɗannan turaku na wannan fafutika guda uku ne:

  1. Ƙungiyar Cigaban Burumawa (Bogghom Development Association): ƙungiya ce da ta ɓalle daga Ƙungiyar Cigaban Kanam. Wannan ƙungiya ita ta haɗe dukkan Burumawa waje guda ba tare da bambamcin jinsi, shekaru ko matsayi ba. Ita ta fara batun Bikin Raya Al’adun Burumawa, ta kuma jagoranci kafa Masarautar Burum da dukkan abinda zai iya taimakawa a kai ga nasara.
  2. Ƙungiyar Matasan Burumawa (Bogghom Youth Movement): Ita kuma wannan ƙungiya ta samu ne sakamakon haramta ayyukan waccar babbar ƙungiya ta cigaban Burumawa. An kafa ta domin a cimma burin da aka saka a gaba na gudanar da bikin raya al’adun Burumawa a shekarar 1986. Bikin da Masarautar Kanam ta yiwa ƙafar ungulu, ta hanyar kai rahoton faruwar rikici ga jahar Plateau idan har aka bari bikin ya gudana. Amma bayan kafa kwamitin bincike da gwamnatin ta yi, daga ƙarshe sai ta bayar da umarni ga ƙaramar hukumar Kanam cewa, a ƙyale Burumawa su gudanar da bikin nasu. Amma duk da haka, sai da Masarautar ta Kanam ta tura zauna-gari-banza suka tarwatsa taron, tun a lokacin da ake kafe-kafen rumfunan manyan baƙi, daga ƙarshe kuma ‘yasanda suka yi awo gaba da wasu muhimman mutane daga cikin Burumawa kuma ja gaba a harkar wannan biki, waɗanda aka kulle su a ofishin ‘yansada na yanki da ke Lantang. Wannan ta faru a ranar 10 ga watan Afirilun 1986.
  3. Inuwar Digatan Burumawa (Forum of Bogghom Village Heads): Ƙungiya ce da ta tattara dukkan digatan Burumawa waje guda. Wannan ƙungiya ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen fafutikar neman kafuwar Masarautar Bogghom. Shugabanta na farko shi ne digacin Kunkyam, Malam Muhammadu Adamu, bayan rasuwarsa kuma, Alhaji Shehu Suleiman, digacin Namaran a lokacin, yanzu kuma Pankwal Bogghom ya gaje shi.

Shelar Bore

Biyowa bayan cin zarafin da aka yiwa Burumawa a yunƙurinsu na gudanar da bikin raya al’adunsu, sai suka yi wata ganawa a garin Fyel, cikin matsanancin sirri, a ranar 12 ga watan Afirilu na shekarar 1986, kasantuwar dukkan mahalarta taron, suna cikin hilar jami’an tsaron ƙaramar hukumar Kanam.

Taron, ya samu halatar dukkan wani mai faɗa-a-ji ɗan ƙabilar Burum. A wannan taro aka yanke cewa:

  1. Dole a ɗauki matakin dakatar da duk wani cin zarafin Burumawa da ake yi, a shara’ance.
  2. Al’ummar Burumawa ta yanke dukkan wata dangantakar sarauta da Masarautar Kanam. Sannan kuma dole a sanar da gwamnatin jaha game da wannan cigaba ta hannun shugaban ƙaramar hukumar Kanam.
  3. Burumawa su samu wata kafa ta sanar da duniya halin da suke ciki, tare kuma da nuna rashin amincewarsu game da duk wani tsoma baki da masarautar Kanam za ta yi a cikin harkokin Burumawa.

Taron ‘Yanjaridu na Duniya

A ranar 15 ga watan Afirilu na shekarar 1986, Burumawa suka gudanar da taron ‘yanjaridu a garin Jos, taron da ya samu halartar wakilan jaridu da gidajen radiyo da dama ciki har da na ƙasashen waje.

Bayan karanta tarkardar bayan taro da Mista Sallah Dashe ya yi a matsayinsa na shugaban Ƙungiyar Cigaban Burumawa, jawabin nasa ya samu yayatawar ‘yanjaridu sosai ciki har da gidan radiyo mallakar jahar Plateau, gidan talabijin na ƙasa reshen jon (NTA Jos), da sauransu.

Bayan faruwar dukkan waɗannan al’amura, sai Masarautar Kanam ta hanzarta mayar da martani game da wacan jawabi na Mr. Sallah, ita kuma gwamnatin Plateau a nata ɓangare ta dakatar da filin Burumwa mai suna Bogghom Magazine da ake gudanarwa a gidan radiyo mallakar jahar da ke garin Jos. Wannan shiri, na ɗaya daga cikin hanyoyin da ake jin muryar Burumawa. Haka nan ma cin zarafin da jami’an tsaron ƙaramar hukumar Kanam ke yiwa Burumawa ya cigaba.

Ƙawancen Burumawa da Jarawa

Wannan cin zarafi da ake yiwa Burumawa, ya saka sun samu tausayawa da kuma goyon baya daga wasu yarukan jahar ta Plateau, mafiya muhimmanci daga ciki su ne Jarawa, kasantuwar suma sun fuskaci irin wannan matsin lamba kafin su samu nasarar kafa tasu masarautar a shekarar 1983.

Wannan tausayawa ta Jarawa, ta kai har ga an kafa ƙungiyar haɗin guiwa tsakanin Burumawa da Jarawa, wacce ake sassauya shugabancinta a tsakanin ƙabilun biyu tun daga wancan lokacin har zuwa yau ɗin nan.

Shigowar Gwamnati Cikin Lamarin

Dukkan wannan balahira da ake yiwa Burumawa, ta gudana ne a zamanin gwamnatin kanal M.C. Alli, mutumin da ke da ra’ayin rarraba kan ƙabilun jahar Plateau. Ana tsaka da wannan hali, sai Allah ya kawo sauyin gwamnati, aka ɗauke kanal Alli daga jahar Plateau, aka kawo kanal Lawrance Onoja a cikin watan Agusta na shekarar 1986, wanda shi kuma yake da ra’ayin haɗa kan ƙabilun jahar ta Plateau tare kuma da gudanar da jagorancinsa bisa daidaito tsakanin jama’a.

Gwamnatin Onoja, ita ta gayyaci sassan biyu; sarkin Kanam da tawagarsa a ɓangare ɗaya, da kuma Burumawa a ɗaya gefen, zuwa taron sasanto a ofishin kwamishinan ƙananan hukumomi da harkokin masarautu (commissioner for local government and chieftaincy affairs).

An fara gudanar da wannan taro a garin Jos, a ofishin kwamishinan, har an saurari jawabin Burumawa, ɗaya ɓangaren ya fara bada nasa jawabin sai musu ya kaure. Hakan na faruwa, jami’an tsaron farin kaya suka gaggauta sanar da gwamna wanda shi kuma nan-take ya yi umarni da cewa taron ya koma ofishinsa. Wanda kuma hakan aka yi, aka wakilta mutane uku daga kowane ɓangare, suka rankaya tare da kwamishinan zuwa ofishin gwamnan.

Da isarsu ofishin gwamna, sai ya ji ta bakin sarkin Kanam. Bayan ya gama kora nasa jawabi, sai gwamnan ya ce, gaskiyar lamari, yana zargin sarki da rura wannan wutar rikici, kuma shi gwamna yana ɗora alhakin faruwar wani abu nan gaba a kan sarkin na Kanam. Sannan kuma ya ja wa sarkin kunne da cewa, shi gwamnatinsa ba za ta yarda da irin wannan cin kashin ba. Daga ƙarshe ya sallami tawagar bisa alƙawarin cewa, zai waiwaici maganar a lokacin da ya dace.

Tabbas, gwamna Onoja, ya yayyafawa wutar ruwa, kuma ta lafa. Sannan kuma ya mutumta Burumawa, domin ya yiwa ɗansu Baburme muƙamin sakataren din-din-din, daga baya kuma kwamishina, wanda shi ne muƙami mafi girma da Baburme ya riƙe a iya tsawon tarihin jahar ta Plateau, a karon farko, a wancan lokacin.

Bayan tafiyar Onoja, sai aka maye gurbinsa da kanal Habibu Shu’aibu (1996 – 1998), wanda shi kuma Bakano ne. Shima ya ɗora daga inda Onoja ya tsaya, har ta kai shi ga kafa kwamitin da ya waiwaici buƙatar kafa masarautu. Kwamitin da ya bashi rahoton buƙatuwar yin haka, shi kuma ya amince. Shirye-shirye sun yi nisa, ana gab da aiwatar da shirin sai sarkin Kanam ya garzaya Kano, ya kama ƙafa da Alhaji Ado Bayero, sarkin Kano, shi kuma ya tuntuɓi kanal Habibu, inda daga ƙarshe aka yi fatali da maganar kafa masarautar.

Yunƙurin Kisa

Da abubuwa suka zafafa, sai masarautar ta Kanam ta shirya kisa. Inda ta tsara cewa, za ta kashe wasu idon garin tafiyar, ciki har da Alhaji Shehu Suleiman.

Masarautar, ta yi amfani da rigingimun da suka faru a shekarar 2000 wajen kashe Mista J.T. Nimfa, Baburme, a gidan gonarsa na ƙauyen Kyamsangi tare kuma da ƙona masa gidansa da ke Dengi, wanda a cikin wannan gida ake gudanar da tarurrukan fafutikar.
Gari na wayewa, ranar Juma’a, Alhaji Shehu Suleiman ya fito daga gidansa domin tafiya Dengi, sai ya yi kiciɓis da makasa, makiyaya, sun tsaya da baburansu a bayan gidansa, suka tare shi, suka sanar da shi saƙon da suke tafe da shi, da kuma wanda ya basu saƙon. Alhaji Shehu ya rantse musu da Allah cewa, bai takawa kowa ba, ballantana ya zubar, saboda haka yana tare da Allah, babu abin da zai faru da shi sai alheri.

Nan take waɗannan makasa suka fara harbin Alhaji Shehu. Sai da suka harbe shi har sau uku bindigar taƙi tashi. Suka tsulawa bindiga fitsari, taƙi tashi. Daga ƙarshe sai suka ce, za su binciki gidansa, wai sun samu labari ya ajiye ‘yan ta’adda, sannan kuma babban ɗansa da ke aiki a Legas ya aiko masa da makamai.
Ana tsaka da faruwar wannan lamari, sai wani jami’in tsaron farin kaya na ƙaramar hukumar Kanam ya bayyana. Ya kuma gayyaci Alhaji Shehu zuwa ofishinsu. Bayan da suka sallame shi, sai ya tafi fadar Kanam domin bin bahasi, amma fir, suka nuna rashin masaniyarsu da faruwar wannan lamari, sannan kuma suka nuna masa cewa, ya bar abin a hannun Allah. Tun daga wannan rana har zuwa yau ɗin nan, ba amo-ba-labarin Mista Ninfa, ballatan a yi maganar kama waɗanda suka yi aika-aikar.

Haƙa ta Cimma Ruwa

A ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2002, gwamnan jahar Plateau, Joshua Chibi Dariye ya shelanta kafuwar Masarautar Burum, tare da ƙarin wasu masarautun guda goma. Wannan cigaban da Burumawa suka samu, bai yiwa sarakunan Kanam daɗi ba. Saboda haka suka gudanar da taron ‘yanjaridu, suka soke wannan cigaba da cewa, an ƙirƙiri masarautar ta Burum ne kawai domin a daɗaɗawa wasu ‘yan tsirarun Kiristoci rai. Ba tare da jinkiri ba, Ƙungiyar Cigaban Burumawa ta mayar musu da martani da cewa, digatan Burumawa goma sha huɗu daga cikin goma sha shida da suka zaɓin sabon sarkin sabuwar masarautar ta Burum duka Musulmi ne. Haka nan kuma shi kansa sarkin da aka zaɓa; Pankwal Bogghom, Alhaji Shehu Sueliman shima Musulmi ne. Saboda haka wannan suka ne kawai maras dalili.

Daga ƙarshe, bayan dukkan jinkiri da aka samu daga ɓangaren gwamnati, da kuma zagon-ƙasa mai zafi daga ɓangaren masarautar Kanam, babban ɗan sarki Shehu Suleiman ya yiwo takakkiya daga Vienna ta ƙasar Austria, ya samu gwamna Dariye, ya roƙe shi aka tabbatar da kafuwar wannan masarauta tare da kuma da naɗin mahaifinsa Alhaji Shehu Sueliman a matsayin sarkin Masarautar Burumawa na farko, mai daraja ta biyu, haɗe da naɗin jikan sarkin Kanam Alhaji Muhammadu Mu’azu Muhammadu II, a matsayin sabon sarkin Kanam, sakamakon rasuwar kakansa Alhaji Muhammadu Ibrahim, wanda ya shigewa Burumawa hanci da ƙudundune.

Tsohon sarkin ya rasu a ranar 24 ga watan Fabarairu na shekarar 2005. An kuma yi waɗannan naɗe-naɗe guda biyu a ranar 9 ga watan Afirilun 2005, zamanin gwamnan jahar Plateau, Joshua Chibi Dariye.

Ta-Leƙo-Ta-Koma

Bayan ƙarewar wa’adin mulkin Dariye a matsayin gwamnan jahar Plateau, sai aka zaɓi Jona Jang a matsayin sabon gwamna, ya maye gurbin Dariye a ƙarƙashin tutar jama’iyya guda, wato PDP. Shigar Jona Jang ofis ke da wuya, sai ya dakatar da dukkan waɗancan masarautu da Dariye ya ƙirƙira, a shekarar 2007, wanda wannan ya shafi Masarautar Burum, tare da sarkinta Alhaji Shehu Suleiman, Pankwal Bogghom.

Shigar da Ƙara

Gazawar gwamnatin Jona Jang wajen maido da waɗannan masaratu da ta dakatar, ya wajabtawa Ƙungiyar Cigaban Burumawa tare da haɗin guiwar Alhaji Shehu Suleiman garzayawa kotu, domin neman kotu ta maido da wannan masarauta tare da sarkinta karagar mulki haɗe kuma da biyansa albashinsa tun daga ranar da aka dakatar da masarautar har zuwa ranar da za a mayar da shi. An shigar da wannan ƙara a babbar kotun jahar Plateau.

Daga ƙarshe alƙalin wannan kotu, ya yanke shari’ar da cewa, lallai gwamnatin Plateau ta mayar da wannan masarauta ta Burum tare da sarkinta Alhaji Shehu Suleiman kan kujerarsa haɗe kuma da biyansa albashi na tsawon lokacin da ya yi a dakace, kamar yadda suka neman a cikin takardar shigar da ƙarar. Amma, fir, gwamna Jang, ya ƙi mutumta wannan umarni na kotu.

Maido da Masarautar Burum da Sarkinta

Sarki goma, zamani goma. Kafa sabuwar gwamnati a Plateau, ƙarƙashin gwamna Simon Baƙo Lalong, a shekarar 2015, shi ya sake baiwa Masarautar Burum damar komawa gidanta na tsamiya tare da sarkinta, Alhaji Shehu Suleiman.

Tun da farko, babban ɗan sarkin Burum, shi ya je yiwa Lalong murnar ɗarewa wannan babbar kujera lambar farko a faɗin wannan jaha ta Plateau. Bayan gama yi masa murna kuma sai ya shigar da buƙatar waiwaitar umarnin da babbar kotun jahar ta baiwa gwamnati mai baring gado amma ta ƙi bi, game da mayar da Masarautar Burum, da kuma sarkinta kan kujerarsa. Bayan ya gama, sai shi sabon gwamnan ya amsa da cewa, zai duba lamarin da idon rahama.

Kwanci-tashi, har aka samu shekaru biyu da yin waccar magana, saboda haka sai wannan ɗa na Alhaji Shehu ya sake komawa wajen gwamna, a wannan karon, sai ya tafi masa da takardar koke daga Ƙungiyar Cigaban Burumawa da ta nemi mutumta wacan umarni na babbar kotu, haɗe da kwafin umarnin, takardar da ke ɗauke da kwanan, 2 ga watan Janairu na 2017. Saboda haka nan take gwamnan ya amsa wannan buƙata. Ya mayar da wannan masarauta da sarkinta tare kuma da cika dukkan sharruɗan da kotun ta buƙaci a yi. An sake kafa wannan masarauta da sarkin nata a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2017.

Bayan wannan ma kuma, gwamnan ya samu halartar bikin raya al’adun Burumawa, abin da ya saka dangantarsa da Burumawa ta ƙarafafa, har ta kai ga an bashi sarauta mai taken “Jaroumin Bogghom”.

Wannan shi ne abinda ya gudana, sannan kuma ya zama sanadin kashe bakin wutar fafutikar da aka ƙyasta ashanarta ta riƙa ci tsawon shekaru talatin da biya (1982 – 2017).

Manazarta:


Shehu A.Y. (2018). Out of Mountain A Dynasty Is Born. Yaliam Press Limited (Babu adireshi).



Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub