Daura Gabatarwa
Shafin Farko

Gabatarwa

Tun farkon kafuwar masarautar Daura zuwa yau, ta yi sarakuna sittin (60), tun daga kan Abduldari, mutumin da ya taso daga Gabas ta tsakiya ya fara kafa ita masarautar ta Daura a wani Dausayi da ake kira 'Gigiɗo' kamar yadda ya zo a Littafin Taƙaitaccen Tarihin Daura wanda Fadar Mai Martaba Sarkin Daura ta wallafa. Sai dai, akwai wata matsala babba guda ɗaya ta rashin samu cikakken jerin sunayen sarakunan na Daura tun daga dauri zuwa yau. Saboda ko shi ma wakilin Tarihi malam Mamman Siya Abubakar cewa ya yi "…Ba mu da cikakken tarihin Daura daga lokacin kafuwar mulki, sai bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo da ya auku a farkon ƙarni na sha tara…" Saboda haka ga ɗan abin da ya samu dangane da jerin sunayen sarakunan Daura.

Rukunin Sarakunan Farko

 1. Abduldari
 2. Kufuru.
 3. Gino
 4. Yakumo
 5. Yakunya
 6. Walzamu
 7. Yanbamu
 8. Gizirgizir
 9. Innagari
 10. Daurama
 11. Gamata
 12. Shata
 13. Batatuma
 14. Sandamata
 15. Jamatu
 16. Hamata
 17. Zama
 18. Shawa
 19. Bawo

Rukunin Sarakuna na Biyu, Sarakunan Fulani

 1. Malam Isiyaku
 2. Malam Yusufu
 3. Malam Muhammadu Sani
 4. Malam Zubairu
 5. Malam Muhammadu Bello
 6. Malam Muhammadu Altine
 7. Malam Muhammadu Mai Gardo
 8. Buntarawa Sogiji
 9. Magajiya Murnai

Rukunin Sarakunan Haɓe,

Tun daga Masu gudun Hijira har zuwa yau

 1. Sarkin Gwari Abdu (Abdullahi)
 2. Sarki Lukudi ɗan Tsoho
 3. Sarki Nuhu ɗan Lukudi
 4. Sarki Mamman Sha ɗan Sarkin Gwari Abdu
 5. Sarki Haruna ɗan Sarki Lukudi
 6. Sarki Ɗan'aro ɗan Sarkin Gwari Abdu
 7. Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu
 8. Sarki Sulaiman ɗan Sarkin Gwari Abdu
 9. Sarki Yusufu ɗan Sarki Lukudi
 10. Sarki Tafida ɗan Sarki Nuhu (a Karo na biyu)
 11. Sarki Musa ɗan Sarki Nuhu
 12. Sarki Abdurrahman ɗan Sarki Musa
 13. Sarki Muhammadu Bashar
 14. Sarki Umar Faruq Umar

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Sai kuma tattaunawa da Wakilin Tarihin na Daura da kuma Dogarin Sarkin Daura mai suna Ɗandaushe, a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar 2016.

Babban Shafin Tarihi
Masarautr Daura

Sarakunan Daura


Ƙofofin Daura


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub