Zuwan Fulani Daura
Shafin Farko

Zuwan Fulani Daura


Gabatarwa

Tun daga zamanin da Sarauniya Daurama ta rasu, zuriyarta ke mulkin Daura har zuwa shekarar 1802 lokacin jahadin Shehu Ɗanfodiye. Bayan samun nasarar da Shehu Ɗanfodiye da almajiransa suka yi a yaƙin da suka yi na ƙarshe da ƙasar Gobir, sai aka samu almajiransa waɗanda suka karɓi tutocin jihadi zuwa garuruwan da suka taso. Daga cikin irin waɗannan almajirai na Shehu akwai Malam Isiyaku na Alƙalawa, wanda yake shi tun can dama Bafulatani ne mazaunin Daura, almajirci ya kai shi wajen Shehu Ɗanfodiye.

Bayan ƙarewar yaƙin Shehu da Ƙasar Gobir, sai shi Malam Isyaku na Alƙalawa ya zo Daura da tutar Jahadi. Da isowarsa Daura shi da jama’arsa sai suka yi wa Daura ƙawanya, suka datse duk wata hanya da ƙofar da ake shiga da fita garin Daura, suka hana dukkan masu shiga gari dan kai wa kayayyakin yau-da-kulllum da ake saya. Faruwar wannan lamari ta saka shi sarki Abdullahi yanke shawarar ya yi haƙuri ya fita salum-alum dan gudun kar a kashe rayukan jama’a da yawa. Saboda haka sai ya yi umarni aka je aka karya ganuwa aka samar da wata ƙofa da suka fita ta cikinta suna kaɗe-kaɗe. Wannan ƙofa ita aka yiwa laƙabi da ‘Ƙofar kiɗi da hauka’.

Manazarta:


Abubakar M.S. (2007). Taƙaitaccen Tarihin Daura. Majalisar Sarkin Daura. An buga a: Ammani Printing Press.

Babban Shafin Tarihi
Masarautr Daura

Sarakunan Daura


Ƙofofin Daura


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub