Me ka ke nema?


Shafin Farko

Jama'iyyar NPC


Gabatarwa

Jama’iyyar Northern People Congress, jama’iyyar siyasa ce a jamuhiryar farko a Nijeriya. Ita ce jama’iyyar da ta fara kafa gwamnatin da ta karɓi mulki a hannun Turawan Mulkin Mallaka. Jama’iya ce mai dogon tarihin kafuwa wadda ta fara daga ƙungiyar al’ada sannan kuma ta rikiɗe ta zama jama’iyar siyasa a shekarar 1951.

Firimiyan Arewa, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, shi ne shugabanta a siyasance wanda kuma Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa, shugaban ministocin Tarayyar Nijeriya ya yi wa mataimaki. Sun riƙe wannan jama’iyya iya tsawon rayuwarta ta shekaru 5 a duniya daga 1951 zuwa 1966 wadda aka kashe ta ta hanyar murɗe wuyan jamhuriyar siyasar farko da wasu sojojin Nijeriya suka yi a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966 abin da ya haifar da juyin Mulkin farko a na Soja a Nijeriya.

Kafuwa

Ɗaliban Tsohuwar Kwalejin Katsina (Katsina College), wadda makaranta ce ta horas da malaman makaranta, su suka fara kafa wata Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Kwalejin Katsina, wato Katsina College Old Boys Association wadda ta yi dogon harshen da ya kai ga kafuwar Jama’iyyar ta NPC. Muhammadu da Aliyu (2003).

Tun bayan rayuwar wannan ƙungiya ta tsofaffin ɗaliban Kwalejin Katsina, sai ‘yan bokon kowane lardi (Province) na Arewacin Nijeriya suka yi ta kakkafa ƙungiyoyin ci gaban lardunan nasu kuma ba tare da tuntuɓar juna ba.

A nasa yunƙurin na haɗa kan al’ummar Arewa waje guda, Malam Aminu Kano tare da haɗin Guiwar Malam Abubakar Tafawa Ɓalewa suka kafa Ƙungiyar Malaman Makaranta ‘Yan Arewa mai suna Northern Teachers Association (NTA) a Turance, wadda ta yi babban taronta na farko a cikin shekarar 1948 a garin Zariya (Muhammad da Aliyu, 2003), taron da ya tattaro kan dukkan ‘yan bokon Arewa musamman ma Malaman Makaranta (Abubakar, 2011).

Daga cikin ƙungiyoyin da suka samu halartar wannan taro akwai  Ƙungiyar Ci Gaban Mutanen Bauchi (Bauchi Discussion Cycle) wadda Malam Abubakar Tafawa Ɓalewa ya shugabanta; Ƙungiyar Harkokin Matasa ta Sakkwato (Youth Social Circle) ta Alhaji Shehu Shagari; Jama’iyyar Samarin Kano (Kano Youth Association) ta Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano; Mutanen Arewa A Yau (Northern People Today) ta Malam Yahaya Gusau daga Zariya; Jama’iyyar Mutanen Arewa (JMA) mai suna Northern People Congress a Turance (NPC) ta Dakta R.A.B. Dikko daga Kaduna (Abubakar, 2011; Muhammad da Aliyu, 2003).

Wanann taro na Ƙungiyar Malaman Makaranta ‘Yan Arewa ya tattara dukkan malaman makaranta na Lardunan Arewa, abin da ya jawo hankalin sauran ‘yan bokon Arewa waɗanda ba malaman makaranta ba suka ga cewa su babu su a cikin wannan tafiya duk da kwaɗayin da suke da shi na ganin an samar da dunƙulalliyar Arewa domin fuskantar ƙalubalen danniya da kuma na siyasa da yake fuskanto yankin daga takwarorin sun a Kudanci; Yankin Yamma da Yankin Gabas. Abubakar (2011) ya misalta cewa, sai mutane irin su Malam Abubakar Imam, Babban Jam’in Gyare-Gyare (Edita) na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da ke Kaduna; Dakta R.A.B. Dikko, likita ɗaya tilo sannan kuma ɗan Arewa kacal da yake da digiri a duk faɗin yankin; Malam Umaru Agaye da kuma Malam Makama ɗan Wazirin Kano na lokacin suka roƙi Malam Aminu da cewa ya kafa wata ƙungiyar da suma za ta basu damar shiga ciki tunda dai wannan ta malaman makaranta ce zalla waɗanda su kuma ba malaman makaranta ba ne.

Kafuwar JMA

Bayan kammala wancan taro na Birnin Zariya da kuma tasowar wannan buƙata ta waɗannan manyan ma’aikata, sai aka haɗu a kan kafa wata ƙungiya tare kuma da saka mata suna na wucin-gadi, Jama’iyyar Jama’ar Arewa (Northern People Union) da kuma saka watan Juli na shekarar 1949 a matsayin lokacin da za a sake taruwa a Kaduna domin ƙaddamar da wannan ƙungiya wanda kuma aka gudanar a Koren Otel (Green Hotel) da ke Kaduna. Abubakar (2011), ya ce a wajen wannan taron ne Malam Sa’adu Zungur ya raɗa wa wannan ƙungiya suna, Jama’iyyar Mutanen Arewa (JMA) wadda kuma ake kira Northern People Congress (NPC) a Turance.

Bayan an kafa wannan ƙungiya kuma sai aka taƙaita manufar ƙungiyar da abubuwan da suka shafi al’adu kawai. Wato ta zama babu ruwanta da siyasa tare kuma da haramta amfani da sunanta na Turanci saboda gudun faɗawa tarkon dokar G.O. 20 (B), dokar da haramtawa ma’aikatan gwamnati shiga harkokin siyasa. Manufofin ƙungiyar su ne; yaƙi da jahilci, zalunci da kuma lalaci.

An zaɓi Dakta R.A.B. Dikko a matsayin shugabanta na farko; Alhaji Sanda na Alhaji, hamshaƙin ɗan kasuwa kuma ya zama babban maitaimakin shugaba; Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, Muƙaddashin shugaba; Mista D.A. Rafi’a, wani ma’aikacin hukumar jirgin ƙasa a Zariya, ya zama mataimakin shugaba na biyu; Malam Umaru Agaye, daga Kamfanin Gaskiya na Zariya ya zama Sakatare; Malam Isa Wali, Kano, jami’in gudanarwa a sakatariyar gwamnati da ke Kaduna ya zama mataimakin sakatare; Malam Abubakar Imam, Babban Jami’in Gyare-Gyare na Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, Kaduna ya zama sakataren kuɗi; Mista Julde na Hukumar Kula da Ƙudan Tsando da Malam Aminu Kano suka zama jami’an bincike (Auditors) na ƙungiya, Abubakar (2011).

Bayan kafa wannan ƙungiya, sai Turawan Mulkin-Mallaka tare da haɗin guiwar Hukumar Gargajiya suka hana wannan ƙungiya rawar gaban hantsi suka kafa mata tankunkumin hana ta amfani da sunanta na Turanci; Northern People Congress (NPC), sai dai ta yi amfani da JMA kawai sannan kuma aka yi mata ƙaƙƙarfan turke da dokar G.O. 40 (B), dokar da ta haramtawa duk wani ma’aikacin gwanati shiga ƙungiyar siyasa domin haramtawa ƙungiyar saka rigar siyasa, (Abubakar 2011; Muhammad da Aliyu, 2003).

NPC a Siyasa

Gagarumar nasarar da Jama’iyyar NEPU ta samu a zaɓuɓɓukan fitar da gwani da aka yi a garuruwan Kano, Jos, Zariya, Minna, Maiduguri, Nguru da kuma Kaduna abin da ya bai wa jama’iyyar damar samun cin kujeru 17 daga cikin 26, shi ne abin da ya haska wa Turawa jar fitilar da suka hango suka gwammace kiɗa da karatu, suka rikiɗe tare da haɗin bakin Hukumar Gargajiya suka shawarci shugabannin Ƙungiyar Al’adu ta JMA da su mayar da wannan ƙungiya zuwa jama’iyyar siyasa kamar yadda Abubakar (2011) ya hakaito daga bakin Ɗanmasanin Kano.

Abubakar (2011) da Yakasai (2004) sun kafa hujjar cewa, saka hannun Turawan Mulkin-Mallaka a cikin lamarin kafa Jama’iyyar NPC ta bayyana ne a dalilin zuwan Babban Sakataren Gwamnatin Arewa, wani Baturen Ingila mai suna Mista Gobel gidan Malam Isa Wali wanda yake shi ne mataimakin sakataren JMA domin karɓar dukkan takardun ƙungiyar ta JMA wanda shi kuma Malam Isa Wali ya hana. Duk kuma da wannan hana takardu da Malam Isa wali ya yi, Yakasai (2004), ya ce basu fasa aiwatar da abin da suka yi niya ba ta yanda rana tsaka suka shelanta kafuwar jama’iyyar a jaridar Hausa mallakar gwamnati wato Gaskiya Ta Fi Kwabo. Wannan kuma ya biyo bayan taron gaggawa da ‘yan Majalisar Dokokin Kaduna suka gudanar a Zariya a ranar 29 ga watan Satumba na shekarar 1951 wanda suka cimma matsayar hanzarta mayar da ƙungiyar JMA ɗin zuwa jama’iyyar siyasa wadda suka tsundima cikinta a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1951 kamar yadda ya zo a jawabin Ɗanmasanin Kano da Abubakar (2011), ya ruwaito.

A sakamakon rikiɗewar wannan ƙungiya zuwa jama’iyyar siyasa mai suna NPC a taƙaice, ya zama dole a canja shugabancinta saboda kuɓutar da waɗanda suke shugabancin nata daga faɗawa tarkon dokar G.O. 40 (B). saboda haka aka maye gurbin shugaba Dakta R.A.B. Dikko da babban mataimakinsa Alhaji Na Alhaji. Muhammadu da Aliyu (2003).

Babban Taro

Jama’iyyar ta gudanar da babban taronta a cikin watan Afirilu na shekarar 1954 a garin Jos inda ta zaɓi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato sannan kuma Firimiyan Jahar Arewa a matsayin babban shugaba na ƙasa; Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa kuma a matsayin Babban mataimakin shugaba na ƙasa sai kuma Alhaji Inuwa Wada da ya zama sakatarenta.

Manazarta


Abubakar A. T. (2011). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello University Press, Zaria, Kaduna-Nigeria.

Muhammad da Isma'il. (2003). Tarihin Shehu Shagari. An buga a TPCS Ltd/Al-Rissalah Printing and Publishing Co. (Nig) Ltd. Domin M and I Essence Publi sher, Kaduna-Nigeria.

Yakasai T. (2004). Tanko Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Government Printers, Kano-Nigeria.



Koma Babban Shafin Tarihi
Babban Shafin Nijeriya

Tarihin Najeriya


Jama'iyyun Siyasa


Alamomi da Tambari

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin



Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub