Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sanata Ahmed Ibrahim LawanShugaban Majalisar Dattawa na 8
Sanata Ahmed Ibrahim Lawan

Gabatarwa


Ƙwararren malamin jami’a daga baya kuma fitaccen ɗan sisaya; Dakta, kuma sanata, Ahmed Ibrahim Lawan, yana daga cikin ‘yan Majalisun Tarayya mafiya daɗewa a zauren majalisar tarayyar Najeriya. Yana zauren majalisa tun farkon dawowar mulkin dimokuraɗiyya Najeriya a shekarar 1999. Abin da ya bashi damar samun cikakkun shekaru ashirin kenan cur (1999 zuwa 2019) a wannan zaure na majalisa tare kuma da samun gogayya a dukkan tagwayen zaurukan majalisar; zauren Majalisar Wakilai wanda ta nan ya fara kuma ya ɗauki shekaru takwas a ciki (1999 – 2007) da kuma zauren Majalisar Dattawa wadda yake shugabanta a yanzu inda a nan kuma ya ɗauki shekaru goma sha biyu a ciki (2007 – 2019).

Daktan boko da siyasa; masanin jogurafi sannan kuma masanin dimokuraɗiyya; ƙwararren malamin makaranta sannan kuma fitaccen, gogaggen ɗan siyasa. Shi ne na tara a jerin shugabannin Majalisar Dattawan Najeriya. Mutum ne shi mai biyayya ga na gaba da shi kodai a shekaru ko kuma ta fuskar aiki. Wannan gwarzon namiji, shi ne mutumin da wannan rubutu ya ƙuduri aniyar baku labarinsa. A yi karatu cikin nasara.

Haihuwa

An haifi Alhaji Dakta Ahmed Ibrahim Lawan a ranar 12 ga watan Janairu na shekarar 1959 a garin Gashua da ke cikin Jahar Yobe.

Karatu

Alhaji Dakta Ahmed Ibrahim Lawan ya yi karatu tun daga matakin firamare har zuwa kan digirin-digirgir; wato digiri na uku. Ya yi karatun firamare a makarantar firamare ta garin Gashua (Gashua Primary School) inda ya kammala a shekarar 1974. Bayan haka kuma ya samu nasarar shiga makarantar sikandiren gwamnati ta Gashua (Government Secondary School Gashua) wadda ya kamala a shekarar 1979.

Ya shiga Jami’ar Maiduguri inda ya samu digirin farko a fannin kimiyyar ƙasa wato jogurafi (Geography), karatun da ya kammala a shekarar 1984. Bayan gama digirinsa na farko, sai ya shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi karatunsa na digiri na biyu a fannin sannin halayya ko bayananniyar ɗabi’ar bigiren ƙasa, wato Remote Sensing a Turance. Karatun da ya kammala a shekarar 1990. Daga ƙarshe kuma ya faɗaɗa nazari, inda ya samu digirin-digigir a fannin sanin bayananniyar ɗabi’ar ƙasa da kuma kimiyyar adana bayanai a fannin jogurafi. Wato Remote sensing and Geographical Information Science (GIS) a Turance a jami’ar Cranfield University da ke Birtaniya a shekarar 1996.

Gogayyar Aiki

Dakta Ahmed Ibrahim Lawan, ƙwararre ne kuma gogaggen malamin makaranta. Tun bayan kammala digirinsa na farko yake karantarwa har tsawon shekaru goma sha biyu cur yana karantarwa (1985 – 1997). A shekarar 1985 zuwa 1986 ya yi aiki tare da hukumar ilimi ta tsohuwar jahar Borno. Sai kuma daga baya ya zama mataimakin malamin jami’a mai lamba ɗaya (Assistant Lecturer 1) a shekarar 1986. Aikin da ya riƙa ci gaba da yi tare da samun ƙarin girma har zuwa shekarar 1997.

Gogaggayar Siyasa

Fitacce ne shi kuma gogaggen ɗan siyasa wanda a nan ma ya ƙware a fannin majalisa.

Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, ya tsunduma harkokin siyasa tun bayan dawowar Najeriya turbar dimokuraɗiyya a cikin shekarar 1999. Inda ya samu nasarar shiga tare kuma da cin zaɓen ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a ƙarƙashin tutar jama’aiyyar APP (1999 – 2003) daga baya kuma ANPP (2003 – 2015).

Ya zauna a wannan majalisa ta wakilai tsawon shekaru takwas (1999 – 2007). Ya yi aiki a kwamatoci da dama na wannan majalisa tare da zamowa shugaban wasu kwamatocin. Fitattu daga cikin kwamatocin da ya shugabanta akwai kwamatin fannin gona (Committee on Agriculture) daga shekarar 2003 zuwa 2005 da kuma kwamatin ilimi (Education Committee) wanda shi kuma ya riƙe daga 2005 zuwa 2007.

A shekarar 2007, aka zaɓe shi a matsayin wakilin Mazaɓar Sanata ta Arewacin Yobe (Yobe North Senatorial District) a ƙarƙasin tutar jama’iyyar ANPP yanzu (2019) kuma APC. Kujerar da yake kai har zuwa yau (2019).

Shugaban Majalisar Dattawa

Tun kafin zamowar Dakta Ahmed Ibrahim Lawan shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, ya riƙe kujerar shugaban kwamatin kula da asusun Gwamnatin Tarayya na Majalisar Dattawa (Public Account Committee) a shekarar 2009.

Ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar Dattawa a shekarar 2017 biyowa bayan tumɓuke Sanata Ali Ndume da aka yi daga kan kujerar. Wannan kuma ya faru bayan rashin samun nasarar zamowa shugaban Majalisar Dattawan da shi Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya yi a shekarar 2015 duk da cewa shi ne yake da cikakken goyon bayan jama’iyya mai mulki a lokacin (2015); wato jama’iyyar APC.

Rashin samun nasarar tasa kuwa ta biyo bayan wata cuku-murɗa da aka yi ne a zaɓen sakamakon gudanar da zaɓe da aka yi a daidai lokacin da kusan mambobin majalisar 50 suke dakon isowar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari Zauren Taron Ƙasa-da-Ƙasa (International Conference Centre) da ke Abuja domin ganawa da shi.

An zaɓe shi a matsayin shugaban Majalisar Dattawa a ranar Talata 11 ga watan Juli (Tuesday, 11 June, 2019), kujerar da ya samu nasarar ɗarewa da ƙuri’u mafiya rinjaye da suka kai adadin 79 daga cikin ƙuri’a 107 da aka kaɗa a ranar waɗanda abokin karawarsa, Sanata Ali Ndume, duk daga jahar Yobe ya samu ƙuri’u 28.

Na gajarce muke zance, Dakta kuma Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, tsohon gogaggen malamin makaranta ne da ya samu tsawon shekaru goma sha biyu (1986 – 2007) yana karantarwa. Yana da digirin-digir. Gogaggen ɗan siyasa ne da ya ƙware a fannin majalisa wanda ya ɗauki shekaru 8 Majalisar Wakilai, yanzu kuma yake cikin shekara ta 12 (2007 – 2019) a Majalisar Dattawa. Kenan idan ka tara za ka samu cewa yana da shekaru 20 cur a Majalisar Tarayyar Najeriya. Yanzu haka (2019), shi ne shugaban Majalisar Dattawan Najeriya.

Manazarta

BBC Hausa (2019). Tarihin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.bbc.com/hausa/labarai-48597290

Busari K. (2019). PROFILE: Crossing many hurdles, Ahmed Lawan, former lecturer, becomes senate president. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/334495-profile-crossing-many-hurdles-ahmed-lawan-a-former-lecturer-emerges-as-nigerias-senate-president.html

Federal Republic of Nigeria (2019). Senate Leadership. An ciro a shekaar 2019 daga shafin: https://www.nassnig.org/mps/senators

Idris U. A. (2019). Najeriya ta yi sabbin shugabannin majalisu. An ciro a shekarar 2019 daga shafi: https://www.dw.com/ha/najeriya-ta-yi-sabbin-shugabannin-majalisu/a-49138504

Legit (2019). 5 facts about new senate president Ahmed Lawan. An ciro a shekarar 2019 daga sahfin: https://www.legit.ng/452349-5-facts-senate-president-ahmed-lawan.html.

Odunsi W. (2019). Ahmed Lawan: Profile of Nigeria’s new senate president. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://dailypost.ng/2019/06/11/ahmed-lawan-profile-nigerias-new-senate-president/

Wikipedia (2019). Ahmed Ibrahim Lawan. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Ahmed_Ibrahim_Lawan


Koma Babban Shafin Tarihi

Tarihin Najeriya


Majalisun Tarayya:

Shugabannin Majalisar Dattawa

 1. Ahmed Lawan
 2. Bukola Saraki
 3. David Mark
 4. Ken Nnamani
 5. Wabara
 6. Pius Anyim
 7. Okadigbo
 8. Evan Enwerem
 9. Ameh Ebute
 10. Iyorchia Ayu
 11. Joseph Wayas
 12. Nwafor Orizu
 13. Dennis Osadebay
 14. Nnamdi Azikiwe

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub