Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sanata Olubukola Ababakar Saraki, CON


Olubukola Abubakar Saraki, CON
Hoto daga etrepreneur.com

Gabatarwa

Likita, ɗan kasuwa, fitaccen ɗan siyasa sannan kuma Turakin Ilori; Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki. Magidanci mai shekaru 57 (1962 – 2019), mace ɗaya da ‘ya’ya huɗu; ɗa ne shi ga tsohon sanatan kwara a zamanin jamhuriya ta biyu, sannan kuma tsohon Wzirin Ilori; wato marigayi Alhaji Olusola Saraki.

Tsohon gwamnan jahar Kwara; tsohon shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya sannan kuma tsohon ɗan takarar kujerar nema zama shugaban Najeriya.

An haife shi a Ingila. Ya yi karatun firmare da sikandire a Lagos daga baya kuma ya kamala a Birtaniya. Ya karanta fannin likitanci a Birtaniya a matakin digiri. Bayani game da rayuwar wannan fitaccen mutum, shi ne manufar wannan rubutun.

Haihuwa

An haifi Olubukola Abubakar Saraki a garin London da ke ƙasar Birtaniya a ranar 19 ga watan Disambar shekarar 1962. Shi ɗa ne ga attajiri kuma gawurtaccen ɗan siya kuma basarake; tsohon shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawan Najeriya (1978 – 1983) a ƙarƙashin tutar jama’iyyar NPN, marigayi Alhaji Olusola Abubakar Saraki. Sunan mahaifiyarsa Florence Morenike Saraki.

Karatu

Sanata, Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki ya yi karatun firmare da sikandire a makarantun Corona School da ke Victoria Island da kuma Kings College a Lagos daga shekarar 1973 zuwa 1978 sannan ya ƙarasa a kwalejin Celtenham College da ke Birtaniya daga shekarar 1979 zuwa 1981.

Bayan samun takardar shedar babbar kwaleji mai suna high school certificate a Ingila, sai kuma ya tsundum jami’ar Londan, wato University of London inda ya karanta digiri a fannin lafiya (M.B.B.S.) a kwalejin horas da likitoci ta jami’ar Londan; wato London Hospital Medical College, University of London. Ya yi wannan karatu daga shekarar 1982 zuwa 1987.

Gogayyar Aiki

A matakin farko, bayan kammala karatunsa, Alhaji Dr. Olubukola Abubakar Saraki ya yi aiki na tsawon shekara guda (1988 – 1989) a matsayin ma’aikacin lafiya a wani asibiti mai suna Rush Green Hospital da ke birnin London. Daga nan kuma sai ya dawo gida Najeriya inda ya canja sheƙa ya tsunduma aikin banki gurin da ya yi aiki da wani banki mai suna Societe Generale Bank of Nigeria Limited har tsawon shekaru goma (1990 – 2000) har sai da ya kai matsayin Executive director na bankin.

Siyasa

Tubalin ginin siyasar Alhaji Olubukola Abubakar Saraki an dasa shi ne a shekarar 2000, inda shugaban ƙasar lokacin, Olusegun Obasanjo ya naɗa shi muƙamin mai bai wa shugaban ƙasa shawara a harkokin kasafin kuɗi (Special Assistant to the President on budget). Muƙamin da ya danƙara masa alhakin tsara kasafin kuɗin shekarar 2000 da kuma 2001 wanda kuma ya sauke cikin nasara.

Daga baya kuma aka sake ɗora masa nauyin zama mamba a kwamatin shiga-tsakani na tsara manufofin tattalin arziƙin ƙasa (Economic Policy Co-ordination Committee) wanda kuma a nan ma ya bayar da gudunmawar da ta dace.

Gwamnan Kwara

Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki ya samu nasarar zama gwamnan jahar Kwara a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP a zaɓen da aka gudanar a shekarar 2003 inda ya ƙwace goruba a hannun kuturu; abin nufi, ya samu nasara a kan gwamnan da ke kan kujera a zamanin. Haka nan kuma an sake zaɓensa a karo na biyu a zaɓen da aka gudanar a shekarar 2007. Abin da ya ba shi damar riƙe kujerar gwamnan jahar tasa na tsawon shekaru takwas.


Alhaji Dakta Bukola Saraki, CON

Sanatan Kwara ta Tsakiya

Bayan kammala wa’adin mulkinsa na gwamna har sau biyu a jere, Olubukola Abubakar Saraki ya sake samun sahalewar jama’ar jahar Kwara ta tsakiya (Kwara Central Senatorial District) domin ya wakilce su a zauren Majalisar Dattawa a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP.

Shi ne dai ya sake samun nasarar sake komawa kan wannan kujera ta wakilcin mazaɓar ɗan majalisar dattawa ta tsakiyar jahar Kwara (Kwara Central Senatorial District), sai dai wannan karon a ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC bayan da ya canja sheƙa ya koma jama’iyyar.

Shugaban Majalisar Dattawa

Bayan samun nasarar cin zaɓen zama mamba a wannan majalisa ta Dattawa da aka gudanar a shekarar 2015 a ƙarƙashin tutar jama’iyyar APC, Olubukola Abubakar Saraki ya tsaya takarar neman zama shugaban wannan majalisa inda ya samu nasarar ɗarewa wannan kujera bayan ya rinjayi abokin karawarsa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan daga Yobe wanda kuma shima daga baya a shekarar 2019 ya samu nasarar zamowa shugaban Majalisar ta Dattawa.


Shugaban Majalisar Dattawa (Bukola Saraki) tare da Shugaban Kasa (Muhammdu Buhari)

Takar Shugaban Ƙasa

Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki, ya yi mi-a-ra koma baya, inda ungulu ta koma gidanta na tsamiya. Abin nufi, a dab da kakar zaɓen shekarar 2019, Olubukola Abubakar Saraki ya sake komawa jama’iyyarsa ta PDP inda ya nemi sahalewar jama’iyyar na ta tsayar da shi takarar shugabancin ƙasa.

Bayan gudanar da zaɓen fidda-gwani na cikin gidan jama’iyyar ta PDP da aka yi, Alhaji Olubukola Abubakar Saraki bai yi nasarar cin wannan zaɓe ba. Amma dai shi ne ya zo na uku a yawan ƙuri’u. 

Rasa Kujerar Sanata

A babban zaɓen da aka gudanar a shekarar 2019, Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki ya faɗi zaɓe abin da ya kawo ƙarshen zamansa a kan kujerar mulki da kuma faɗuwa a zaɓe a karon farko tun shigowarsa siyasa a shekarar 2000. Kenan, ya ɗauki tsawon shekaru goma sha tara (2000 zuwa 2019) yana riƙe da muƙaman siyasa.

Sarauta

Turakin Ilorin, ita ce taken sarautar Mai Girma Olubukola Abubakar Saraki. Naɗin da sarkin Ilorin Alhaji Dakta Ibrahim Sulu Gambari ya yi masa a lokacin da yake kan kujerar gwamnan jahar Kwara.

Wazirin Ilorin na huɗu. A ranar Lahadi 21 ga watan Yuli na shekarar 2018, Mai Martaba sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari ya ɗaukaka darajar Mai girma Turaki zuwa Waziri biyowa bayan rasuwar mahaifinsa, Olusola Saraki. Naɗin da ya bashi damar zamowa na huɗu a cikin jerin Waziran garin Ilorin.


Naɗin Wazirin Ilorin, Alhaji Bukola Saraki

Gudunmawa

Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara, tsohon gwamna tsawon shekaru takwas sannan kuma tsohon shugaban majalisar Dattawa, mai shekaru takwas a wannan majalisa, ba zai rasa gudunmawar bayar wa ba.

A zamanin gwamnatinsa, Olubukola Saraki ya kafa tarihin cewa, jahar Kwara ce ta fara kammala shirin samar da wutar lantarki mai zaman kanta (Nigerian Independent Power Project) inda ya kafa Ganmo Power Station a Ilori wadda tashar samar da wutar lantarki ce mai zaman kana mallakin jahar Kwara (Proshare, 2018; Ojo, 2019). Ya kuma rarraba taransifomomi a dubbunnan garuruwa a cikin jahar (Ojo, 2019).

A fannin gona ma ya samar da shirin noma mai taken Shonga Farms Agricultural Programme. Abin da ya ɗaukaka darajar jahar daga mai shigo da abinci zuwa fitarwa (Proshare, 2018; Ojo, 2019).

Haka nan sauran fannonin rayuwa da suka haɗa da ilimi, lafiya, muhalli da sauran su duk ya taɓa su.

Zuwan sa Majalisar Dattawa ta Tarayya, ya bayar da gudunmawowin da suka inganta rayuwar talaka, musamman ƙwato haƙƙin talaka. Shi ne ya ƙarfafa dokar biyan fansa ga waɗanda ɗanyen mai ke malala a gonakinsu (National Oil Spill Detection and Response Agency Amendment Bill); kafa ƙungiyar GLOBE Nigeria wadda take a matsayin reshe ta Global Legislators Oganisation (GLOBE International); tabbatar da an yi adalci a matsalar haƙar ma’adanai ta jahar Zamfara (Lead Poisoning Crisis, Zamfara). Da sauran gudunmawowi da ya bayar masu tarin yawa.

Auratayya

Alhaji Dr. Olubukola Abubakar Saraki yana da mata ɗaya da kuma ‘ya’ya huɗu, namiji ɗaya da kuma mata uku. Sunan mai ɗakinsa Toyin Saraki. ‘Ya’ya kuma su ne Oluwaseni Saraki, Halimat Oluwatosin Saraki da kuma tagwaye; Teniola Saraki da Teniayo Saraki.


Dr Bukola Saraki Tare da Iyalinsa
Hoto daga Shafin Linda Ikeji's Blog

Lambobin Yabo/Kyaututtukan Girmamawa

Zamowar Alhaji Dr Olubukola Abubakar Saraki mutumin da ya bayar da gudunmawowi da dama a kuma matakai mabambanta, ya karɓi lambobin yabo da kuma kyaututtukan girmamawa da dama. Mafiya ƙololin daraja a cikin su akwai:

 • Lambar yabo ta CON da ya karɓa yana kan kujerar gwamna. Abin da ya bashi damar kafa tarihin cewa shi ne gwamna mai ci na farko da ya karɓi wannan lamba. Kenan, wasu gwamnonin sun karɓa amma ba lokacin da suke kan kujerar gwamna ba.
 • Digirin girmamawa da jami’r Calabar ta bashi a shekarar 2016.
 • Turakin Raya Ƙasar Nupe, shi ne taken sarautar girmamawa da Sarkin Nupe, Etsu Nupe, Alhaji Abubakar Yahaya ya yi masa a ranar Asabar 22 ga watan Juli na shekarar 2013.

Ojo (2019), ya lissafo waɗannan lambobin yabo da  Alhaji Dr Olubukola Abubakar Saraki ya karɓa kamar haka:

 • Governor of the Year, This Day Newspapers, 2004
 • Best Governor of the Year in Agricultural Development, City People KSNG, 2004/2005
 • Africa Club Award, Harvard Business School, 2005
 • Best Governor in Africa, Kenneth Kaunda Foundation, 2006
 • Man of the Year, Osun State Broadcast Corporation, 2006
 • Grand Patron, Nigeria Referee Association, 2007
 • Best Governor on Food Security, This Day Newspaper, 2008
 • Life Fellowship, All Nigeria Confederation of Principals of Secondary Schools (ANCOPPS), 2009
 • Outstanding Governor on Energy, Nigerian Compass Newspaper, 2009
 • Emerging Tiger of Nigeria (Leadership Award), This Day Newspaper, 2010
 • Award of Excellence, Chartered Accountants, 2010
 • Award of Excellence, College of Medicine, University of Lagos, 2012
 • Good Ambassador of North Central Zone, Radio Television, Theatre and Art Workers Union of Nigeria (RATTAWU), 2014
 • Man of the 21st Century, National Association of Nigerian Students (NANS), 2016
 • Outstanding Leadership Award, Governor of Kwara State, Abdulahmed Fatai, 2017
 • Award of Excellent Leadership, Association of Maritime Journalist of Nigeria (AMCON), 2018
 • Outstanding Politician of the Year, Sun Newspaper, 2018
 • Politician of the Year, New Telegraph Award, 2018

Waɗanann kaɗan ne daga cikin ɗimbin lambobin yabon da ya karɓa.

Wannan shi ne Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki. Likita, ɗan kasuwa, ɗan siyasa sannan kuma basarake.

Tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara (2000 – 2003); gwamnan jahar Kwara (2003 – 2011); ɗan Majalisar Dattawa (2011 – 2019); shugaban Majalisar Dattawa na 8 (2015 – 2019); ɗan takarar shugaban ƙasa (2019).

Turakin Ilori, Turakin Raya Ƙasar Nupe yanzu kuma Wazirin Garin Ilorin na 4. Magidanci mai mata ɗaya da ‘ya’ya huɗu wanda kuma yawan shekarunsa suka kai 57 (1962 – 2019).  Alhaji Dakta Olubukola Abubakar Saraki, CON.

Manazarta

Ahmad R.W. (2019). Saraki named Waziri Garin of Ilorin. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.dailytrust.com.ng/saraki-named-waziri-garin-of-ilorin-262175.html

All Africa (2016). Nigeria: Ita-Giwa, Saraki, Duke Bag Unical Honorary Doctorate. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://allafrica.com/stories/201603120148.html

Busari K. (2018). Saraki gets new traditional title (PHOTOS). An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.premiumtimesng.com/news/top-news/277365-saraki-gets-new-traditional-title-photos.html

Hamsat F. (2018). As Exclusively Reported By Global Excellence, Bukola Saraki Turbaned ‘Wazirin Ilorin’. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://globalexcellenceonline.com/as-exclusively-reported-by-global-excellence-bukola-saraki-turbaned-wazirin-ilorin/

Ilorin Info (2013). My turbaning as Turaki, a call to higher service - Saraki. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.ilorin.info/fullnews.php?id=5018

Nwogo S. (2018). Saraki steps into father’s shoes as Waziri Ilorin. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://punchng.com/saraki-steps-into-fathers-shoes-as-waziri-ilorin/

Ojo E. (2019). Saraki – Biography, Political History And Life Of Abubakar Bukola Saraki. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.entrepreneurs.ng/bukola-saraki-biography/

Ola S. (2018). Emir oF Ilorin Elevates Saraki From Turaki To Waziri Garin Of Ilorin. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: http://newstide247.com/emir-f-ilorin-elevates-saraki-from-turaki-to-waziri-garin-of-ilorin/

Saraki (2019). My Story. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: http://www.abubakarbukolasaraki.com/background/my-story/

Proshare (2019). #Election2019: Abubakar Bukola Saraki's Profile. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://www.proshareng.com/news/Politics/-Election2019--Abubakar-Bukola-Saraki-s-Profile/38724

Udeze C. (2019). Bukola Saraki Biography, Children, Wife, Education and Other Facts. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://buzznigeria.com/bukola-saraki/

Wikipedia (2019). Bukola Saraki. An ciro a shekarar 2019 dag shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Bukola_Saraki

Web Archive (2017). Senator (Dr.) Abubakar Bukola Saraki. An ciro a shekarar 2019 daga shafin: https://web.archive.org/web/20180813145649/http://senatepresident.gov.ng/ the-senate-president/


Koma Babban Shafin Tarihi

Tarihin Najeriya


Majalisun Tarayya:

Shugabannin Majalisar Dattawa

 • Ahmed Lawan
 • Bukola Saraki
 • David Mark
 • Ken Nnamani
 • Wabara
 • Pius Anyim
 • Okadigbo
 • Evan Enwerem
 • Ameh Ebute
 • Iyorchia Ayu
 • Joseph Wayas
 • Nwafor Orizu
 • Dennis Osadebay
 • Nnamdi Azikiwe

Shugabannin Ƙasa


Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub