Alhaji Atiku Abubakar

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Atiku Abubakar, GCONAlhaji Atiku Abubakar, GCON


Gabatarwa

Manomi, Ɗankasuwa, Kwastam, Ɗansiyasa, Basarake, kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya daga 1999 zuwa 2007. Alhaji Atiku Abubakar mutum ne jajirtacce, cikakke kuma fitaccen ɗan fafutikar neman ‘yanci. Ya yi fice ƙwarai wajen tallafa wa jama’a.

Ya rayu rayuwar aikin kwastam tsawon shekaru ishirin, ya fara aiki a garin Legas, garin da ya samu horonsa na kwastam, ya zauna a Kano, Maiduguri, Kaduna sannan ya sake komawa Legas. Ya yi aiki da shugabannin ƙasar najeriya har guda shida.

Manufar wannan rubutu ita ce, tsamowa mai karatu ɗan abin da ya sawwaƙa dangane da rayuwar wannan hamshaƙin attajiri, ɗan kasuwa, ɗan siyasa, kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, da nufin shi wannan rubutun ya zama wata fitila da zata haskakawa matasanmu irin ƙwazonsa dan a samu darrusan da za a iya ɗauka.

Haihuwa

Sunana Atiku Abubakar. An haife ni a ranar 25 ga watan Nuwamba na shekarar 1946 a garin Jada da ke cikin jahar Adamawa (Abubakar, 2013).

Salsalarsa

Atiku Abubakar bafullace ne, wanda ya samo asali daga garin Wurno ta Jahar Sokoto. Shi ɗa ne ga Garba, wanda shi kuma garba ɗa ne ga Atiku, shi kuma Atiku bafulatanin garin Wurno ne ta Jahar Sakkwato. Atiku malami ne, makiyayi kuma manomi. Ya baro garinsa na Wurno sanadiyyar wani abokinsa mai suna Arɗo Usman. Mahaifiyarsa kuma sunanta A’isha Kande, wacce ita kuma asalinta shi ne garin Dutsen Jahar Jigawa. Sunan mahaifinta Adamu Dutse.


Karatunsa

Kasantuwar Mahaifin Atiku Abubakar wato malam Garba Atikulƙadir Abdumalami, Atiku Abubakar ya taso da karatun addini tun yana ƙarami. Dalilin da ya jawo ɗan jinkirinsa wajen shiga makarantar boko saboda ƙin shi malam Garba da abin. Wannan ƙiyayyar karatun zamani da shi malam garba yake yi sai da ta kai har an kulle shi tare da kuma da biyan tara ta kuɗi.


Alhaji Atiku Abubakar ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamare ta Jada (Jada Primary School). An saka shi a wannan makaranta a watan Janairu na shekarar 1954 ya kuma kammala a shekarar 1960. Daga nan kuma sai Adamawa Proɓincial Secondary School wacce take a Yola a shekarar 1961 harnzuwan1966. Bayan kammala wannan makaranta kuma sai ya wuce Kaduna zuwa Makarantar ‘Nigerian Police Academy’ inda ya fara samun horo amma bai yi nisa bay a bari ya kama aiki da ma’aikatar kuɗi ta Arewacin Najeria a fannin tara haraji (Revenue Division of the Northern Regional Ministry of Finance). Bayan nan kuma dai a cikin wannan shekara ta 1966 ya samu nasarar shiga makarantar ‘School of Hygiene’ wacce yanzu ta koma ‘School of Health Technology’ a garin Kano. Ya yi karatunsa na difiloma a fannin ‘Royal Society of Health’. Bayan ya kammala wannan karatu kuma a shekarar 1967, sai ya sake neman gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da nufin yin wata difilomar a fannin doka (Diploma in Law).

Bayan kuma waɗannan karatuttuka da ya yi, Alhaji Atiuku Abubakar ya samu halartar horo na musamman na tsawon wata uku a ƙasar Finland a shekarar 1978. Haka nan kuma a lokacin da yake Legas ya sake samun dama ta zuwa horo na wata guda  a fannin ‘Drug Law and Enforcement’ a makarantar ‘Police Academy’ da ke Cairo ta ƙasar Masar (Egypt). A shekarar 1985, ya sake zuwa ƙasar Amurka, inda ya sake samun horo na tsawon wata biyu a fannin 'Drug Enforcement'.

Gogayyarsa ta Aiki

Alhaji Atiku Abubakar ya fara aiki na wucin-gadi tun yana ɗan shekara goma sha biyar a Hukumar Gargajiya (Ganye Native Authority) ta Ganye. Yakan yi wannan aiki ne lokacin da yake karatunsa na sikandire a garin Yola, duk lokacin da ya zo hutu sai ya yi wannan aiki.

A Watan Yuni na shekarar 1969, Alhaji Atiku Abubakar yana gab da gama karatunsa na difiloma a fannin doka, sai ɗaukar aiki daga Hukumar Ma’aikata ta Najeriya (Federal Civil Service Commission) suka je jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Zariya da nufin tantance waɗanda za a ɗauka aiki. A wannan gaɓa ce suka duba fayil ɗin ɗan makaranta Atiku Abubakar, suka taras cewa ya taɓa samu horon aikin ɗansanda kuma har an rubuta cewa ya cancanci aiki, saboda haka ba wata tababa, sai suka rubuta jawabin cewa ya cancanci zama kwastam a fannin (Department of Customs and Exercise). Tun sannan Alhaji Atiku Abubakar yake bada gudunmawa a wannan gida na kwastam har sai da ya yi aiki na tsawon shekaru ishirin (20), sannan ya bar aiki.

Bayan samu horo da ya yi na aikin kwastam, Alhaji Atiku Abubakar an tura shi zuwa iyakar Najeriya da ke Idi Iroko. A shekarar 1972 aka sake tura shi zuwa Filin Tashi da Saukar Jiragen sama na Ikeja ta Legas, daga baya kuma aka mayar da shi tashar jiragen ruwa ta Apapa a Legas. A tsakiyar shekarar 1975 aka ɗaukaka darajarsa zuwa muƙamin ‘Superintendent of Customs’ sannan kuma aka yi masa taransifa zuwa Kano a shekarar 1976, sannan aka sake yi masa taransifa zuwa Maiduguri a shekarar 1977 aka kuma ɗaukaka matsayinsa zuwa ‘Area Administrator’. A shekarar 1980 aka sake yi masa taransifa zuwa Kaduna. An sake ɗaukaka darajarsa zuwa ‘Assistant Area Administrator, a shekarar 1984. An sake mayar da shi Legas zuwa filin tashi da saukar jirage na Murtala Muhammed (Murtala Muhammed Airport) a shekarar a matsayin ‘Customs Area Administrator’. A shekarar 1987 aka yi masa muƙamin ‘Deputy Director of Customs and Exercise’ mai kula da ‘Enforcement and Drugs’. Alhaji Atiku Abubakar ya bar wannan aiki na kwastam a ranar 30 ga watan Afirul na shekarar 1989 da muƙamin ‘Deputy Director’, lokacin yana da shekaru 43 a duniya.

Harkar Iyali

Alhaji Atiku Abubakar, ya auri Titilayo Albert a matsayin matarsa ta farko a shekarar 1971 a garin Legas, bayan doguwar taƙaddama da suka sha sanadiyar rashin samun goyon baya daga ɓangaren mahaifiyar matar saboda dalilin bambanci yare. Sannan kuma ya auri Sa’adatu Ladi Yakubu a matsayin matarsa ta biyu a garin Kano. Sai kuma a cikin shekarar 1983 ya auri Gimbiya Rukaiyat wacce take 'ya ce ga Lamiɗon Adamawa, Lamiɗo Aliyu Musɗafa, a matsayin matarsa ta uku. Ya yi aurensa na huɗu a ranar 22 ga watan Yuni na shekarar 1986 inda ya auri Fatima Shettima wanda shi kuma aka ɗaura shi a Maiduguri. Sannan kuma a lokacin da yake gudun hijira a ƙasar Amurka, ya auri Jennifer Iwenjiora bayan ya saki Ladi, wanda hakan ne ya bashi damar yin wannan aure da Jennifer wacce daga baya ta canja sunanta zuwa Jamila Atiku Abubakar.

Kasuwanci

Babban ɗankasuwa, kuma hamshaƙin mai kuɗi, Alhaji Atiku Abubakar ya fara kasuwancinsa a shekarar 1974, ya fara ne da gina gida ya bayar da shi haya. Gidansa na farko da ya fara ginawa a 'Yola Government Reserved Area (GRA)', ya gina shi ne da rancen kuɗin gini da ya karɓa daga banki. Da ya gina wannan gida na farko sai ya bayar da shi haya inda ya karɓi kuɗin, ya kuma sake sayen wani filin ya gina, haka ya yi ta jujjuyawa har sai da takai ga ya gina gidaje takwas a cikin shekaru kaɗan.

Sannan kuma ya sake karɓar wannan bashi na banki a shekarar 1981, ya samu gona wacce ya yiwa suna da ‘Gesse Derdirace’ mai faɗin hekta 2,500 (2,500 hectres) a kan hanyar Yola zuwa Numan.

A shekarar 1982, Alhaji Atiku Abubakar tare da haɗin Guiwar wani Baturen Italiya mai suna 'Gabriel Volpi' suka haɗa hannu suka buɗe katafaren kamfanin hada-hadar Mai da Iskar Gas mai suna 'Nigeria Container Services (NICOTES)' wanda yanzu ya koma 'INTELS (Integrated and Logistics Services)' kamfanin da ya samar da guraben ayyukan da suka haura 15,000 a ciki da wajen Najeriya.

A shekrar 1998 ya kafa wani kamfani haɗin guiwa da matarsa ta biyu Ladi, kamfanin da aka yiwa suna da ABTI-ZARHAM, sunan da aka harharɗo daga sunayen ‘ya’yansa. ABTI na nufi Abba da Atiku, ZAHRAM kuma Zainab, Ruƙaiya, Hauwa da Maryam. Da sunan wannan kamfani aka kafa makarantar Naziri ta ‘ABTI Nursery and Primary School’ da ke Yola a shekarar 1992. Daga baya kuma aka sake faɗaɗa ta koma ‘ABTI Academy’, makarantar da ta shahara wajen bayar da ilimin sikandire. A ƙarshe kuma sai ta bunƙasa ta koma jami’ar ‘ABTI-American University’ wacce yanzu ake kira ‘American University of Nigeria, Yola’. Ya zuwa lokacin da muke wannan rubutu (2016), wannan Jami’a tana daga cikin sahun farko na gagarabadau ɗin jami’oin Najeriya.

Sarauta

Turakin Adamawa, shi ne muƙaminsa na sarauta. Wannan muƙami na Turaki muƙamin ne da sai ɗan asalin cikin gidan sarauta ake bai wa shi, saboda shi Turaki shi ne ke da alhakin kula da harkokin cikin gidan Sarki. Lamiɗon Adamawa Alhaji Aliyu Musɗafa shi ya yi wa Alhaji Atiku Abubakar wannan naɗi a ranar 19, ga watan Nuwamba na shekarar 1982.

Shigarsa Siyasa

Haka nan idan aka juya fannin siyasa, Alhaji Atiku Abubakar gawurtaccen ɗan siyasa ne. Tarihin siyasarsa yana komawa tun daga shekarunsa na karatun difiloma da ya yi a Kano, wato shekarar 1966 zuwa 1967 aka fara zaɓarsa muƙami na farko a matsayin shugaban ɗalibai.

Amma shigarsa siyasar mai ɗungurumgum, ya samo asali ne bayan haɗuwarsa da marigayi Shehu Musa ‘Yar’aduwa wanda shi ya gayyace shi zuwa harkar siyasa daga baya kuma ya zama ubangidansa a harkar siyasa.

Alhaji Atiku Abubakar su suka kafa jama’iyyar ‘People’s Front of Nigeria (PFN)’ tare da su marigayi Shehu Musa ‘Yar’aduwa a watan Mayu na shekarar 1989 bayan cire takunkumin kafa jama’iyyun siyasa da tsohon sugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi. Jama’iyyar da shi Alhaji Atiku Abubakar ya zamar mata ɗaya daga cikin ‘National Vice Chairmen’. Wannan jama’iyya tasu kamar sauran jama’iyyu, ta ci karo da waigin da shugaba Ibrahimi Badamasi Babaginda ya jefawa ƙungiyoyin siyasa a ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 1989 yana mai cewar gwamnatinsa ba za ta yi wa kowace ƙungiyar siyasa rijis ba, saboda tsofaffin ‘yan siyasa wanɗanda suka dagula lamura su ne suka sake haɗa waɗannan ƙungiyoyi, saboda haka duk ya rushes u ya kafa nasa guda biyu; ‘National Repubican Convention (NRC)’ da kuma ‘Social Democratic Party (SDP)’. Faruwar wannan al’amari bata karyawa Alhaji Atiku Abubakar da sauran mutane guiwa ba a kan aniyar su ta kawo ƙarshen mulkin soja da kuma ɗora ƙasar Najeriya a kan turbar dimokuraɗiyya.

Alhaji Atiku Abubakar da ubangidansa a siysasa marigayi Alhaji Shehu Musa ‘Yar’aduwa sai suka zaɓi su tsudunma cikin jama’iyyar SPD. To tun daga wannan lokaci har zuwa yau ɗin nan (2016) ake damawa da Alhaji Atiku Abubakar yake kuma bada muhimmiyar gudunmawa wajen ganin dimokuraɗiyya ta zauna da gindinta a Najeriya.

Takarar Siyasa

Alhaji Atiku Abubakar ya yi yunƙirin fitowa neman takarar gwamnan tsohuwar jahar Gwangola a shekarar 1990 a ƙarƙashin tutar jama’iyyar SDP, yana tsaka da wannan yunƙuiri nasa shugaba Ibrahim badamasi Babangida ya yanka jahar ta Gongola gida biyu inda aka yi sababbin jahohin Adama da Taraba, tsohon sunan Gongola kuma aka share shi. A shekarar 1991 Alhaji Atiku Abubakar ya yi takarar neman takarar gwamnan Adamawa, wanda bayan lashe zaɓen fitar da gwani da ya yi, ɗaya daga cikin abokan takararsa a wannan jama’iyya ta SDP ya ƙi yarda wanda wannan ta jawo soke wannan zaɓe nasa haɗe da wasu jahohi guda takwasa, da ma kuma hana su sake tsayawa takarar a wannan zaɓe da za a sake gudanarwa a karo na biyu.

A shekarar 1993, Alhaji Atiku Abubakar ya fito takarar neman takarar kujerar shugan ƙasa a ƙarƙashin tutar jama’iyyar SDP, ya samu nasarar lashe zaɓen matakin farko wanda ake gudanarwa a jaha, sannan kuma ya tura zuwa na ƙasa wanda aka gudanar a garin Jos. A wannan mataki Alhaji Aitu Abubakar sun yi yarjejeniya da Mashood Abiola cewa ya janye masa in yasao shi ya ɗauke shi a matsayin mataimaki, amma bayan cin nasarar shi Mashood Abiola sai ya juyawa Atiku baya ya ci amarasa, ya ɗauki Babagana Kingibe a matsayin mataimakin nasa.

Ya sake tsayawa takarar neman kujerar gwamnan Adamawa a shekarar 1998, wanda ya samu ansarar lashe zaɓen da aka gudanar a watan Disambar wannan shekarar.

Ya sake tsayawa takarar kujerar Shugan Ƙasa a shekarar 2006, takarar da ta gamu da cikas daga gwamnatin da take kan mulki ta wannan lokacin ƙarƙashin shugaba Obasanjo. Tangarɗar da aka samu ita ce ta cire sunansa daga jikin ƙuri’a, wanda bayan garzayawarsa kotu ya samu nasarar aka sake lanƙaya sunansa, sannan aka gudanar da zaɓe ya kuma yi nasarar zamowa na uku a zaɓen da aka kaɗa. Ya yi wannan takarar ne a ƙarƙashin tutar jama’iyyar ‘Action Congress of Nigeria (CAN)’.

Alhaji Atiku Abubakar ya sake yin takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2011 a ƙarƙashin tutar jama’iyyarsa ta asali, wato PDP, jama’iyyar da su suka kafa amma aka fattatke su daga cikinta. A zaɓen fitar da gwani da jama’iyyar ta gudanar a Abuja, da-ƙyar-da-jiɓin-goshi shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya samu nasara.

A shekarar 2015, Alhaji Atiku Abubakar ya sake tsayawa takarar kujerar shugabancin Najeriya wannan karo kuma a tutar jama’iyyar ‘All People’s Congress (APC)’ inda ya zo a uku a zaɓe fitar da gwani da aka gudanar.

Mataimakin Shugaban Ƙasa

A  zaɓen da ya tsaya a matsayinsa na gwamna, ya samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar a watan Disamba na shekarar 1998, wanda ya mai da shi gwamnan jahar Adama a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP. Bayan kammala wannan zaɓe kafin shigarsa wannan ofishi na gwamna, sai shugaba Obasanj ya zaɓe shi a matsayin mataimakinsa, saboda haka suka sake lashe wannan zaɓe na shugabancin Najeriya da aka gudanar a ranar 27 ga watan Fabarairu na shekarar 1999. Alhaji Atiku Abubakar ya zauna a kan wannan kujera ta mataimakin shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo tun daga 1999 har zuwa 2007.

Shugbannin Ƙasa da ya yi Aiki a Ƙarƙashinsu

Tun farko kama aikinsa a matsayin Kwastam, Alhaji Atiku ya yi aiki a ƙarƙashin shugabannin Najeriya guda shida, waɗanda suka haɗa da: General Yakubu Gowon, General Murtala Muhammed, General Olusegun Obasanjo, President Shehu Shagari, Major-General Muhammadu Buhari, General Ibrahim Badamasi Babangida.

Manazarta:


Abubakar A. (2013). My Life Atiku Abubakar. Published in Nigeria by Africana Legacy Press Abuja.

Atiku (2016). My Thoughts and Opinions. An ciro a shekarar (2016), daga shafin http://atiku.org/aa/

Nigerian Biographies (2015). Biography of Atiku Abubakar; Ex-vice President; Politician; Adamawa Sate Celebrity. An ciro a shekarar 2016, daga shafin, http://www.nigerianbiography.com/2015/05/biography-of- atiku-abubakar-ex-vice.html

Wikipedia (2016). Atiku Abubakar. An ciro a shekarar 2016, daga shafin https://en.wikipedia.org/wiki/Atiku_Abubakar.

Shafin Tarihi


Mashahuran MutaneTura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub