Williams Henry Bill Gates III

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Williams Henry Bill Gates IIIHoto: www.biography.com
William Henry Bill Gates III.


Gabatarwa

Bill Gates gagarabadau ne wajen shirya softuwayar kwamfuta (computer programming). Shi ne mutum ɗaya tilo da ya fi kowa kuɗi a duniya sanadiyar kamfanin shirya softuwaya mai suna Microsoft da suka kafa, shi da abokin karatunsa na babbar makaranta (High school) Paul Allen a shekara 1975. Mutumin Amurka ne wanda bayan ya kammala karatunsa na elimentare da kuma babbar makaranta (high school) kamar yadda aka saba, kuma ya samu nasarar shiga jami’ar Harvard da ke Cambridge, a cikin jahar Massachusetts, da ke Ƙasar Amurka. Amma daga ƙarshe ya gudu ya bar ladarsa. Wato kenan ya zama irin mutanen da ake kira “drop out” a Turance.

Tabbas, haka ne, Bill Gates ya gudu ya bar ladarsa a jami’ar Harvard da ke ƙasar Amurka ba dan bashi da ƙoƙari ba, ko kuma matsala irin ta biyan kuɗin makaranta. A’a, Bill Gates ya bar makaranta ne sakamakon aikin ƙirƙirar softuwaya da ya yi wa wani kamfanin kwamfuta da ke Mexico, kamar yadda ya faɗa a cikin ɗaya daga cikin irin jawaban da yake gabatarwa a duk shekara a lokacin yaye ɗalibai a Jami’ar ta Harvard. “…ɗaya daga cikin manyan abubuwan tarihina, ya faru a watan Janairu 1975, a lokacin da na yi kira daga ɗaki zuwa ga kamfani a Mexxico, waɗanda suka fara yin ‘personal computer’ ta farko a duniya. Na ce zan yi musu softwaya, su kuma suka amince. Suka ce a shirye muke, ka zo ka same mu bayan wata guda, amma ka zo da samfuri. Daga wannan lokaci, na fara aiki dare-da-rana a cikin wani  ‘SQL project’. Ƙarewar wannan watan shi ne ƙarshen karatuna na kwaleji, sannan kuma farkon tafiyata mai tarin muhimmanci tare da Microsoft…”. Kuma ma yakan faɗin wannan kalmar “Zan dawo na samu digirina” dan a yi dariya.

Wannan gagarabadau xin mai kuɗi mutum ne mai matuƙar taimako. Wannan ta tabbata da ya kafa wata gidauniya mai suna “Bill and Melinda Gates Foundation”. Babban aikin wannan gidauniya shi ne tallafawa duk wanda yake da buƙata, kamawa tun daga kan Nahiyoyi (continents), Tarayyoyi (Unions), Ƙasashe (countries), Jahohi (State), ƙananan hukumomi (Local Government), garuruwa (towns), qungiyoyi (groups) har zuwa ɗaiɗaikun mutane, a faɗin duniya baki ɗaya.

Bilgates yana jawabi

Haihuwarsa

An haifi William Henry Bill Gates III a ranar 28 ga watan Oktota na shekarar 1955 (28 October, 1955) a garin Seattle, da ke Jahar Washington, a Ƙasar Amurka.

Tasowarsa/Karatunsa


Hoto: https://en. wikipedia.org
Bill Gates da Matarsa Mellinda

Williams Henry Gates III ya halarci makarantar gwamnati (public school) tun daga gired na ɗaya har zuwa na shida. Daga nan kuma ya samu nasarar komawa makaranta mai zaman kanta mai suna Seattle’s exclusive Lakeside School wanda a nan ya haɗu da Paul Allen.

An fara sanar da shi kwamfuta da shriya softuwaya a shekarar 1968 a lokacin yana gired na takwas a makaranta. Lokacin yana ɗan shekara 13 a duniya (Encarta, 2009; Wikipedia, 2016). Bayan da makarantar su ta sayi wata nau’in kwamfutar da ake jona ta da Mainfirem. Tun daga wannan lokaci Bill Gates ya ke ninƙaya a cikin harkar kwamfuta da shirya softuware tare da wannan abokin nasa Paul Allen har zuwa lokacin da shi Bill Gates ya ƙirƙiri wata softuwaya ta wasannin mai suna tic-tac-toe.

A cikin shekarar 1972, lokacin Bill Gates yana ɗan shekara 17. Bill Gates da abokinsa Paul Allen suka kafa wani kamfani mai suna Traf-O-Data. Kamfanin da ya ƙirƙiri na’urar kwamfutar da ke ƙirga adadin motoci saboda bincike akan abin da ya shafi cunkoson motoci a cikin shekarar 1975, lokacin da suke jami’ar Harvard da ke Cambridge, a jahar Massachusetts ta ƙasar Amurka, Bill Gates ɗan shekara 20 shi da abokinsa Paul Allen suka shirya wani nau’i na softuwayar BASIC dan amfanin wata kwamfuta mai suna Altair 8800 wacce ita ce ƙaramar kwamfuta (personal computer) ta farko a duniya. Sun sayar da wannan softwaya ga wani kamfani mai suna Micro Instrumentation and Telemetry Systems (MITS), wanda shi ya ƙirƙiri wannan kwamfuta. Wannan softwaya ta BASIC da suka yi ita kuma ta sake basu dama suka sake shirya wata dan amfanin sauran kamfanoni makamantan wannan. Saboda wannan dalili sai ayyuka suka yi musu yawa a wannan kamfani da suka kafa mai suna Microsoft shi da abokinsa. Dan haka shi Bill Gates sai ya yanke shawarar barin karatunsa na jami’a dan mayar da hankali kan harkokin da za su bunƙasa wannan kamfani nasu na Microsoft.

Loakcin da Bill Gates ya kai shekaru 25 da haihuwa, wato a cikin shekarar 1980, sun samu nasarar ƙulla yarjejeniya da kamfanin International Business Machines Corporation (IBM), kan su shirya masa jigon softwaya (operating system) da zai yi aiki a kan ƙaramar kwamfuta ta IBM (IMP PC), kuma a wannan yarjejniya an yarda cewa Microsoft ke da haƙƙin mallaka na wannan softuwaya.

Bayan kammala wannan jigon softwaya mai suna MS-DOS, sai suka mai da shi ya zama gama-gari, ma’ana zai iya hawa dukkan wata ƙaramar kwamfuta ba wai sai lallai ta IBM ba. Wannan ya matuƙar haɓɓaka kuɗaɗen shiga na wannan kamfanin a shekarar 1986 – 1987 wanda kuma a wannan lokacin Bill Gates yana da shekara 31 da haihuwa. Wannan kuma ita ce ta maida Bill Gates matashin da yafi kowane matashi da ya nemi kuɗi da guminsa kuɗi a duniya.

Tun daga wannan lokaci Bill Gates ya ci gaba da fafatawa yana ninɓaya a cikin harkar shirya softwaya yana kuma ɓara faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shigarsa ta hanyar raba hannu ya saka jari a wasu kamfanoni da ba nasa ba. Misali, a shekarar 1989 ya kafa kamfanin Corbis Corporation.

Manazarta:


Biographies. (2016). Bill Gates Biography, Business Leader, Entrepreneur, Philanthropist (1955–). An ciro daga: http://www.biography.com/people/bill-gates-9307520#early-career

Youtube. (2016). Motivational - Bill Gates Speech at Harvard. An ciro daga: https://www.youtube.com/watch?v=wq-gba5nMrc

Wikipedia. (2016). Bills Gates. Wikipedia, the free encyclopedia. An ciro daga: https://en.wikipedia.org/wiki/Bill_Gates.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub