Yusuf Maitama Sule Danmasanin Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Yusuf Maitama Sule Ɗanmasanin Kano



Hoto, Daily TrustYusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano


Gabatarwa

Sanin mutum sai Allah! Daga cikin mutane, akwai waɗanda Allah ke yi wa baiwar da bayyana ta ke da matuƙar wahala. Irin waɗannan mutane, rayuwarsu cike ta ke da darrusan da za a iya koya. Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, ɗaya ne daga cikin irin waɗannan mutane. Mutum ne mai ilimin addini da kuma na zamani.

Allah ya yi masa baiwa da haƙuri, gaskiya, riƙon amana, cika alƙawari, sada zumunci, yafiya, barkwanci, dogaro da kai, da kuma sadaukar da kai. Mutum ne ɗan kishin ƙasa, mai son ganin jama’a sun ci gaba, mai son zaman lafiya da haɗin kai, ga kuma uwa-uba, abin da ya zama gagarabadau a kai, wato fasahar zance da kuma iya magana.

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, malamin makaranta ne, ɗan siyasa sannan kuma basarake. Tabbas, Alhaji Yusuf Maimata Sule, Ɗanmasanin Kano, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ciyar da ɗaiɗaikun mutane gaba har zuwa kan gwamnatin tarayya. Da shi aka yi fafutikar ƙwatar ‘yanci da kuma ganin yunƙurin tabbatar da haɗin kan ƙasa da ɗorewar zamanta a matsayin ƙasa guda.

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, ya yi aiki da sarakunan Kano biyar, da kuma gwamnan Kano Audu Baƙo, sannan kuma ya yi aiki da shugabannin Najeriya tun daga kan Dr. Nmandi Azikwe, har zuwa hawan shugaba Buhari na biyu (2017), wasu lokutan kai tsaye ta hanyar riƙe wani muƙami a cikin gwamnati, wasu lokutan kuma a bayan fage kamar yadda ta faru a zamanin Janar Muhammadu Sani Abacha. Haka nan kuma a dimokuraɗiyyance, da shi aka kafa jamhuriyyar farko, ta biyu, ta uku, da ta huɗu da mu ke ciki a yanzu. Yana da ƙwarewa a fannin siyasa ta gida da kuma wajen Najeriya.

Haƙiƙa, na san wannan teku, duk wanda ya shige ta, zai kamfacin ruwan da zai ya sha ya yi wanka. Ina taya mai karatu murnar shiga wannan makaranta da za a kwashi darrusan rayuwa a ɓagas. A sha karatu lafiya.

Haihuwa da Salsalarsa

An haife shi a garin Kano cikin unguwar Yola, a shekarar 1929. Sunansa na yanka shi ne Yusuf, sunan da Madawakin Kano Mahmudu ya buƙaci a saka masa domin ya maye gurbin sunan mahaifinsa da shi. Madawaki Mahmudu, ya riƙa kiran sa da suna Abbana. Su kuwa sauran jama’ar fada, suna kiransa da suna Maitama, saboda al-kunya, don gujewa kiran sunan mahaifin Madawaki Mahmudu kai tsaye. Wannan suna kuma na Maitama, ya samo asali ne daga Galadiman Kano Yusuf, wanda a lokacin da yake kan kujerar Galadiman Kano, an yi yaƙin da ya sabauta yawan amfani da makaman da aka samar daga tama; ita kuwa tama, sidanari ce da ake haɗa ƙarfe da ita. Saboda haka, sai aka riƙa kiran shi Galadima da sunan Maitama. Da aka samu Yusufu, sai kuma aka sake ara masa wancan suna. Saboda haka, sai sunansa ya zama Yusuf Maitama. Sunan mahaifnsa kuma Sule, saboda haka cikakken sunansa shi ne Yusuf Maitama Sule.

Mahaifin Yusuf Maitama, wato Sule, ɗa ne ga Ahmadu, wanda shi kuma Ahmadu Bafulatani ne daga garin Maraɗi da ke cikin Nijar a yau. Ana zaton cewa ko dai an kamo shi Ahmadu ne a lokacin yaƙi, ko kuma an sayo shi ne aka kawo garin Kano. Ahmadu ya kasance makusanci ga Madawaki Ƙwairanga (1894); wato Madakin Sarkin Kano Aliyu ɗan Abdullahi (Alu mai Sango) 1894 – 1903. Ahmadu da Ƙwairanga aminan juna ne tun kafin zamowar shi Ƙwairanga Madawaki. Duk gurin da aka ga zara, to a ga wata. Ko a fagen daga suna tare. Haka nan kakarsa mai suna Hadiza, mutumiyar Ningi ce da mahara suka kamo ta zuwa Kano, a lokacin suna tsaka da bikin wata ƙawarsu.

A lokacin gudun hijira zuwa Dutsin Bima, Sule yana goye aka yi wannan hijira da shi. Shi Ahmadu, mahaifin Sule, wato kakan Yusufu ta wajen mahaifinsa, shi ne Wazirin Madawakin Kano Ƙwairanga. Shi kuma Sule, wato mahaifin Yusufu, shi ne Ɗanmurin Madawakin Kano Mahmuda, daga baya kuma ya zama Turakin Yola a zamanin Madawaki Shehu.

Sunan mahaifiyarsa Hauwa, wacce ita kuma ‘ya ce a wajen Isyaku. Shi kuma Isyaku, shuwa ne daga Chadi. Shi ma dai kamo shi aka yi a lokacin farmakin Barno, da aka yi a cikin shekarar 1890, daga nan aka kawo shi garin Ƙunci, daga baya kuma ya tsinci kansa cikin ayarin bayin Madawakin Kano wanda ya zamar wa Madawaki Hussaini Babban Zagi, har zuwa zamanin Madawaki Mahmudu. Ita kuwa kakarsa ta wajen mahaifiya, ‘ya ce a wajen limamin Dawakin Tofa, gundumar da a koda wane lokaci ta ke ƙarƙashin hakimcin Madawakin Kano.

Karatunsa

Tun tasowarsa, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya fara karatun Alƙur’ani a makarantar Malam Rabi’u. Hakanan kuma ta fuskacin karatun ilimi, Maitama ya yi karatunsa a hannun limamin Yola.

1937 – 1939: Makarantar Elimantare ta Shahuci. A cikin shekarar 1937, Madawakin Kano Mahmudu ya saka Ɗanmasani a makarantar Elimantare ta Shahuci (Shahuci Elementary School). A yadda aka saba, ɗalibi kan ɗauki tsawon shekaru huɗu kafin kammala karatu a wannan mataki na elimantare. Amma ta ɓangaren Ɗanmasani ba haka aka yi ba, saboda zamowarsa ɗalibi mai kaifin basira, da ya samu shekaru biyu a makarantar, sai aka bashi dama ya rubuta jarabawa zuwa mataki na gaba kuma ya samu nasarar shiga makaranta ta gaba wato makarantar midil (middle school).

1940 – 1943: Makarantar midil (middle school) ta Kano, wacce yanzu ta koma kwalejin Rumfa (Rumfa College). Shigar Ɗanmasani wannan makaranta ke da wuya, ya samu karɓuwa a gurin malamai da ɗalibai saboda ƙwazonsa da kuma son jama’a da ya ke da shi. Shi ne ɗalibin da ya fi kowa ƙwazo a darasin Turanci da kuma na addini Musulunci. A wannan mataki na tsakiya; wato midil, ɗalibi zai yi karatu na tsawon shekaru biyar. A wannan matakin ma, kaifin basirar Maitama ta ba shi damar rubuta jarabawar zuwa makaranta ta gaba, bayan zaman shekara uku da ya yi a makarantar. Wanda kuma bayan sun rubuta jarabawa suka samu nasara su huɗu.

Sai dai, wannan nasara tasa ta so ta gamu da cikas, saboda a wancan lokacin ana raba guraben karatun ne zuwa lardunan (provinces) Arewa, inda a wannan shekarar yankin Kano ya samu guraben ɗalibai biyu kacal. Wajen rabon waɗannan gurabe, sai umarni ya zo daga gidan sarki cewa ‘ya’yan gidan kawai za a ɗiba, wanda shi kuma shugaban makarantar a ta nasa ɓangaren yana ganin kamata ya yi a raba, kujera ɗaya ga gidan sarki, ɗayar kuma gidan Madawaki. Ana cikin haka sai aka samu Isa Wali, ɗaya daga cikin yaran gidan sarki ya ce shi baya son zuwa kwaleji, ya fi son ya tafi makarantar koyon shari’a, saboda shi Arabiyya ya ke son karantawa. Wannan ce ta baiwa Maitama damar samun wannan gurbi a bayan cin jarabawa da ya yi zuwa Kwalejin Kaduna.

1943 – 1947: Kwalejin Kaduna (Kaduna College). Maitama, ya shiga wannan makaranta lokacin yana da shekaru goma sha uku a duniya. A wannan mataki kusan dukkan waɗancan siffofi da aka ambata da farko nasa, suka fara bayyana.

Maitama, a zamansa na wannan makaranta ya shiga ƙungiyar wasan kwaikwayo, ƙungiyar da ya riƙe shugabancinta har na tsawon shekaru biyu. Shi ne ladanin makaranta a lokaci guda kuma mataimakin liman. Ya riƙe muƙamin mai unguwa (prefect). Yana daga cikin ɗaliban da aka riƙa ɗiba suna fita zuwa wasu garuruwa domin karantar da jama’a, a ƙarƙashin tsarin nan na yaƙi-da-jahilci.

Zamowarsa mai unguwa, abu ne da ya ke da nasaba da zamowarsa mutumin jama’a kuma mai barkwanci. Kamar yadda aka saba, a duk shekara, shugaban makaranta yakan zaɓi wasu ɗalibai ya naɗa su muƙamai da yawa da za su riƙa taimakawa wajen gudanar da sabgogin ɗalibai. A irin wannan halin ne wata rana da safe, a lokacin taruwar ɗalibai a filin taron tattaunawar safe (assembly ground), ranar da za a naɗa sababbin shugabannin ɗalibai, sai Maitama ya yi wata shigar da za ta bada dariya. Ya samu gwadonsa ne, ya ɗinke bakin ya mayar da shi alkyabba, sannan ya kawo wani ƙaton carbin aduwa, ya riƙe yana ja. Da dosowarsa filin taron sai ɗalibai ‘yan’uwansa suka riƙa ihu, suna tafi suna cewa, “Rika riko malam Yusufu, yau namu ya samu!” Shi kuma ya shige gaban taro ya tsaya.

Bayan wani lokaci sai shugaban makaranta ya fara kiran sunayen shugabannin ɗalibai, ɗalibai sun yi shiru suna ji, ba su ji an kira sunan Maitama ba, can da aka zo ɗaki na ƙarshe, kuma shi ne ɗakin da Maitama ya ke, da aka kira sunan ɗakin, kafin shugaban makaranta ya furta sunan mai unguwar, sai ɗalibai caraf suka cafke, “Malam Yusufu!”, shugaban makaranta ya umarci ɗalibai da su yi shiru, ya kuma sake ambatar wannan suna na ɗaki, ɗalibai suka sake amsawa da cewa, “Malam Yusufu! Malam Yusufu!”, har sai da shugaban makaranta ya haƙura ya damƙa wannan ɗaki a hannun Maitama. Ai kuwa yana faɗin sunan Maitama a matsayin mai unguwar wannan ɗaki, sai ɗalibai suka kama ihu, kaɗe-kaɗe, da tafi. Abin da ya kawo ƙarshen wannan taro kenan na wannan rana.

Haka Maitama ya zauna a matsayin mai unguwar wannan ɗaki. Ya kuma ɗaukaka darajar wannan ɗaki har sai da ya zamo ɗaki mafi tsafta a dukkan faɗin makarantar. A lokacin shugabancinsa a wannan ɗaki, bai sha wahala da jama’a ba, saboda dama shi mutumin mutane ne.

A shekarar su ta fita, suka rubuta jarabawar kammala sikandire mai suna “Cambridge School Certificate Examination”. Amma cikin rashin sa’a, wasanni da sauran abubuwan ƙuruciya, su suka shagaltar da Maitama bai samu nasarar cin wannan jarabawa duka ba, ta yadda har zai samu fita zuwa Ingila dan ƙaro karatu, ba wai domin bashi da ƙoƙari ba. Ganin haka, sai malaminsa na Turanci, ya bashi shawarar shiga Babbar kwalejin elimantaren horas da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria).

1947 – 1948: Babbar kwalejin elimantaren horas da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria). Shigar Maitama wannan makaranta, ya riga ya samu darasi daga abubuwan da suka gabata, saboda haka sai ya riƙe wuta har sai da ya fita da kyakkyawan sakamako daga wannan makaranta, wanda kuma hakan ce ta saka aka tura shi garin Kano domin zamowa malami a tsohuwar makarantar sa ta farko.

 Gogayyar Aiki

1948 - 1953: Malamin Makaranta a Makarantar Tsakiya ta Kano (Kano Middle School), wacce yanzu ta zama Kwalejin Rumfa (Rumfa College). Bayan kammala karatunsa na Babbar kwalejin elimantaren horas da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria), sai aka tura shi zuwa makarantar midil ta Kano domin zamowa malami a can. A zamanin mulkin Turawa, ƙarƙashin Hukumar Gargajiya ta Kano.

Shigarsa wannan makaranta, Maitama ya bayar da gagarumar gudunmawa da suka haɗa da, koyarwa a aji, kafa ƙungiyar wasan kwaikwayo ta makaranta, da sauransu.

A wannan fanni na karantarwa, sai da ya kai matsayin mai duba malaman Grade II (Grade II visiting teacher), muƙamin da aka naɗa shi a shekarar 1953.

1954: Ɗan majalisar wakilai ta tarayya, mai wakiltar yankin Birnin Kano. a zamanin mulkin Turawa.

1954: Jami’in yaɗa labarai na hukumar gargajiya ta Kano (Information Officer, Kano Native Authority).

1959 – 1964: Ɗanmajalisar Wakilai ta Tarayya, mai wakiltar yankin Dawakin Tofa. Mazaɓar Ɗan majalisa mafi girma a Najeriya a wancan lokacin. Wannan kuma, saboda zamowar wannan mazaɓa mafi girma a cikin lardi (province) mafi girma a Najeriya, wato yankin Kano (Kano Province). Zamanin mulkin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.

1964 – 1966: An sake zaɓensa a karo na biyu a kan wannan kujera da ƙuri’ar da yawanta ya kai 14,256, adadin da ya bashi damar yi wa abokin takararsa Alhaji Sani Kanta daga jama’iyyar adawa ta NEPU kayen raba gardama. Wanda shi ya samu ƙuri’ar da adadinta ya kai 1,237. Zamanin mulkin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.

1964 - 1966: Ministan Ma’aikatar Tama, Ƙarafa da kuma Makamashi (Minister of Federal Ministry of Mining and Power). Zamanin mulkin Sir Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Haƙiƙa, sabon minister, Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, ya bar tarihi a wannan ma’aikata ta hanyar bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawo sauyi mai amfani a wannan ma’aikata. Tun da farko, zuwansa ma’aikatar, ya taras da kamfani ɗaya tilo, Shell BP, da ke da ruwa da tsaki a cikin harkar manfetur. Saboda haka, sai ya yi ƙoƙari aka samawa wannan kamfani abokan gasa. A yunƙurin kawo wasu kamfanoni, sai ta bayyana cewa, dukkan kamfanonin da suka nuna buƙata, ƙawaye ne na wancan kamfani na farko, kamfanonin da suka haɗa da Esso, Mobil Texaco, da Kuma Elf. Saboda haka sai ya sake baiwa kamfanin Eni (Agip) dama ya zo shi ma aka buga da shi.

Har yau dai, haƙa bata cimma ruwa ba, saboda haka a hangen nesa irin nasa, sai ya ga cewa akwai buƙatar samar da wani kamfani na gwamnati, wanda zai riƙa saka ido a harkar hadahadar manfetur ɗin Najeriya, sannan kuma ya riƙa baiwa gwamnati bahasi. A kan haka ya samar da kamfanin National Oil Corporation (NOP), wanda daga baya ya koma NNPC har zuwa yau ɗin nan (2017).

1966: Jami’in Hulɗa da Jama’a na taron tsarin mulkin ƙasa na wucin-gadi (Ad-hoc Constitutional Public Relations Coordinator). Zamanin Mulkin Yakubu Gowon.

Ayykun da aka ɗora masa ta bakin gwamnan Lardin Arewa (Northern Region), Manjo Hassan Usman Katsina, su ne, tuntuɓar manyan mutane daga dukkan ɓangarorin Najeriya, yaɗa labaran ayyukan taron, wayar da kan jama’a game da haɗin kan ƙasa, da sauransu. Daga cikin manya-manyan nasarorin da wannan ofishi nasa ya samu, akwai rarrashin Cif Awolowo da ya yi, ya saka shi ya janye daga barazanar ɓallewa da yankin yammaci ya ke yi, da ma yardarsa ya shiga cikin gwamnatin shugaba Yakubu Gawon ta hanyar karɓar muƙamin kwamishinan (kwatankwacin misinta a yanzu) kuɗi a lokaci guda kuma mataimakin shugaban hukumar zaɓaɓɓu ta ƙasa. Muƙaman da shi Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya sa aka yi wa Cif Awolowo.

1968: Kwamishina a Jahar Kano. Farko, kwamishinan ma’aikatar ƙananan hukumomi (commissioner, ministry for local government, Kano State), sannan aka mai da shi ma’aikatar gandun daji da ci gaban karkara (Ministry of forestry and community deevlopment), daga ƙarshe kuma kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai, harkokin matasa, wasanni da kuma al’adu (ministry of information, youth, sport and culture). Zamanin mulkin Gwamnan Kano Audu Baƙo.

Daga cikin abubuwan ambato da Alhaji Yusuf Maitama Sule ya bari a faɗin jahar Kano, a lokacin da ya riƙe ma’aikatar gandun da ji da ci gaban karkara (ma’aikatar da ya fi daɗewa a cikinta), akwai dashen bishiyoyi da ya ƙirƙiro, wanda aka yi a faɗin jahar Kano, idan aka shiga lunguna da saƙo-saƙo na faɗin tsohuwar jahar Kano, za a iya cin karo da bishiyoyi kamar maina/darbejiya, da kuma maɗaci, wannan, Ɗanmasani ne tushen aikin. Sai kuma katafaren gidan namun daji na Kano (Kano Zoo), shi ma, aikinsa ne.

1972: Ya zama shugaban Majalisar Harkokin Al’adu ta Najeriya. Wannan majalisa, ƙungiya ce mai zaman kanta. Kuma ya bayar da gagarumar gudunmawar da ta kamata. Daga cikin irin wannan gudunmawa da ya bayar akwai, assasa taron shekara-shekara na bukukuwa da wasannin gargajiya (Annual National Festival of Art and Culture) da ya yi, wanda aka fara shi a garin Kaduna a cikin shekarar1972. Sai kuma buƙatar samar da Hukumar Al’adu da Jagoranci ta Ƙasa (Ministry for Culture and National Guidance) da ya miƙa wa gwamnatin Najeriya a shekarar 1973, daga baya, gwamnati ta mayar da wannan majalisa ta zama reshen gwamnati, inda aka canja mata suna ya koma Majalisar Harkokin Al’adu ta Ƙasa (National Council for Art and Culture). A shekarar 1975, Maitama, shi ya zama Ciyaman na hukumar. Zamanin Mulkin Janar Yakubu Gowon.

1975: Ciyaman na riƙo (Part Time Chairman) na Majalisar Harkokin Al’adu ta Ƙasa (National Council for Art and Culture). Sannan kuma a lokaci guda, tabbataccen ciyaman (full time chairman) na kwamatin shirye-shiryen halartar taron duniya karo na biyu, na bukukuwan wasannin gargajiya da al’adu na baƙaƙen fatar Afirka (Second World Black and African Festivals of Arts and Culture). Wannan naɗin nasa ya biyo bayan karɓar majalisar da gwamnatin tarayya ta yi a matsayin wani reshe na hukumar yaɗa labarai ta Najeriya (Federal Ministry of Information). Zamanin Mulkin Janar Yakubu Gowon.

1975 - 1978: Babban Kwamishinan Ma’aikatar Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a (Chief Commssioner Public Complaint Commssion), ma’aikatar da shugaban Najeriya, Janar Muratala Ramat Muhammed ya ƙirƙira saboda shi, sannan kuma daga baya ta zama ɗaya daga cikin dalilan da waɗanda suka kashe Janar Murtala suka zayyana, kamar yadda aka gani a cikin rubutaccen jawabin da Dimka ya ƙuduri aniyar yi bayan ya zama shugaban Najeriya. A jikin jawabin nasa, ya zayyana cewa, daga cikin dalilan da suka saka su yin juyin mulki, akwai wata ma’aikatar da aka ƙirƙira wacce kuma ba a buƙatar ta, wato ma’aikatar sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a, sannan kuma shugabanta, wato Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, ya ke karɓar albashin da ya fi na kowa a faɗin ƙasa, duk da cewa shi ba soja ba ne. Wannan, su a ganinsu, yunƙuri ne na tallafawa shi Ɗanmasani ya cimma manufarsa ta siyasa.

Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya bar wannan ma’aikata a shekarar 1978, da nufin shiga takara a zaɓen da za a gudanar na gaba.

1979 – 1983:  Wakilin Najeriya na Dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya (Nigeri’s Permanent Representative to the United Nation). Zamanin Mulkin Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.

A zamansa a wannan majalisa, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kawo cigaba, musamman zamowarsa ciyaman na Kwamatin Musamman na Majalisar Ɗinki Duniya kan Yaƙi da Wariyar Launin Fata (Chairman United Nations Special Commity Against Apartheid). Kusan abu ne mai wahala a samu wata ƙasa a duniya, da Alhaji Yusuf Maitama Sule, bai je ya gabatar da jawabi kan wannan batu na wariyar launin fata ba.

1983: Ministan Ma’aikatar Jagoranci ta Ƙasa (Ministry of National Guidance), wacce babbar manufarta ita ce, dasa halayen ɗa’a a zukatan ‘yan Najeriya, yaƙi da rashin ɗa’a, da kuma haɓɓaƙa kyawawan halaye. Zamanin Mulkin Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.

1992: Shugaban Hukumar Gudanarwar Cibiyar Nazarin Harkokin Siyasa (Chairman Governing Council for Centre for Democratic Studies). A zamanin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.


Hoto, UN
Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano

Gudunmawa Domin Kawo Cigaba

1948: Ya kafa ƙungiyar wasan kwaikwayo ta Kano, ƙungiyar da ta samu nasarar zama reshen fim na Hukumar Gargajiya ta Kano (Kano N.A. Film Unit).

1947: Ya gudanar da wasan kwaikwayo ta gidan radiyon Kano. Shirin da ya samu karɓuwa sosai a wajen jama’ar jahar Kano har ta kai ga samun kyauta daga mai marata sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayero.

1948: Ya gudanar da darasin koyar da Turanci ta gidan radio (English by Radio), domin ilimantar da jama’ar Kano.

1948: Ya buɗe makarantar yaƙi da jahilci. Makarantar da ta fara daga soro/zauren gidansu zuwa makarantar Shahuci bayan bunƙasarta. Daga cikin ɗaliban wannan makaranta akwai Alhaji Mudi Sifikin, Alhaji Tanko Yakasai (wanda ya zama mai baiwa shugaban ƙasa shawara a gwamnatin Alhaji Shehu Shagari), Abdulƙadir na Adamu Ɗanjaji, Baballiya Manajan Banki, Umaru Ɗangwauron Duma, da kuma Alhaji Sabo Bakin Zuwo (wanda ya zama gwamnan Kano – 1983).

1948: Ya kafa ƙungiya mai suna Jama’iyyar Samarin Kano. Daga cikin mambobin wannan ƙungiya akwai Alhajo (Dr.) Ado Bayero (wanda ya yi sarautar Kano daga 1963 – 2014), Alhaji Sani Darma, Alhaji Maje Abdullahi, Alhaji Sharu Uba, da sauran mutanen da daga baya suka zama shuwagabanni a jahar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Babbar manufar wannan ƙungiya ita ce samar da haɗin kai, abokantaka, zaman lafiya da kuma taimakon juna a tsakanin samarin masarautar Kano waɗanda suke a rarrabe sakamakon matsayin da kowane ke da shi. Wato akwai samarin Hayewar Fulani waɗanda su ke su ne sarakuna. Akwai kuma samarin Hayewar Bakin Kasuwa, waɗanda su ke su ne talakawa. Shi Maitama, zamowarsa ɗan Hayewar Bakin Kasuwa, yana cuɗanya da samarin Hayewar Fulani saboda zamowarsa abokin karatunsu, sannan kuma mai sarauta wanda ya fito daga gidan Madawakin Kano. Wannan ƙungiya ta cimma burinta, inda a karo na farko, samarin waɗannan ɓangarori guda biyu suka haɗu a taron bikin Maitama da aka yi na aurensa da Goggo Shatu a shekarar 1948. Daga nan kuma abun ya ci gaba, har ya zama al’ada da aka sakawa suna Zaman Ajo.

1948: Ya yi sanadin buɗe ɓangaren Hausa a jaridar Daily Commet ta Nmandi Azikwe. Ɓangaren da aka yi wa suna da Hantsi Leƙa Gidan Kowa. Abin da ya tayarwa da Turawan mulkin mallaka hankali.

1949: Ya bayar da gudunmawa wajen kafa ƙungiyar malaman makaranta ta Arewa (Northern Teachers Association), ƙungiyar da ta zama tubalin kafuwar dukkan wasu ƙungiyoyi da jama’iyyun fafutikar ‘yanci a Arewacin Najeriya da ma ƙasa baki ɗaya.

1949: Da shi aka kafa Ƙungiyar Mutanen Arewa. Ƙungiyar da aka kafa ta da manufa ta yaƙar jahilci, zalunci da lalaci, wacce shi Maitama ya zamar mata Babban Mataimakin Shugaba na farko. Duk da cewa, daga baya ya bar wannan ƙungiya saboda dabaibayin da aka yi mata na rashin tsoma baki a harkokin siyasa.

Ɗanmasanin Kano

A cikin shekarar 1954, bayan zamowar Alhaji Yusuf Maitama Sule, jami’in yaɗa labarai na hukumar gargajiya ta Kano, sarkin Kano Muhammadu Sanusi na farko (1953 – 1963), ya buƙaci Alhaji Yusuf Maitama Sule, da ya zaɓi dukkan sarautar da ya ke so a naɗa shi, ba tare da ya nema ba.

Bayan samun wannan tayi da Alhaji Yusuf Maitama Sule ya yi daga wajen sarki, sai ya nemi shawara daga Malam Ahmad Mettidan, wanda shi kuma a lokacin ma’aikaci ne a gidan radiyon tarayya (Nigerian Broadcasting Corporation). Inda ya ba bashi shawara cewa, ya zaɓi sarautar Ɗanmasani, wacce ita kuma wannan sarauta ta Ɗanmasani, asalin ta daga Katsina ne. Tun da farko akwai wani waliyyi daga cikin waliyyan Katsina guda huɗu mai wannan sunan. Shi Wali Ɗanmasani, aikin sa a fadar Katsina shi ne jagorantar sarki da masarautar Katsina a kan al’amuran addini. Bayan rasuwar wannan waliyi kuma, sai sunan ya zama sarauta, aka naɗa ɗansa a kan wannan kujera, sannan aka ci gaba da kiransa da malam Ɗanmasani.

Wannan sarauta ita ce ta farko a Kano, kuma har yanzu (2017), shi Alhaji Yusuf Maitama, shi ke riƙe da wannan sarauta; kenan tun daga 1984 zuwa 2017, ya samu shekaru 63 yana riƙe da wannan sarauta. Ya yi aki tare da wanda ya naɗa shi, marigayi sarki Muhammadu Sanus I (1953 – 2017). Sai kuma sarkin Kano Muhammadu Inuwa Abbas (1963). Sai marigayi sarkin Kano Alhaji (Dr.) Ado Bayero (1963 – 2014), wanda shi kuma aboki ne ma a wajen Alhaji Yusuf Maitama Sule. Yanzu kuma yana tare da sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda ya fara daga 2014 zuwa yau (2017), duk a matsayin mai riƙe da wannan sarauta ta Ɗanmasanin Kano.

Gwagwarmayar Siyasa da Fafutikar ‘Yanci

Tun lokacin da ya ke karatu a Kwaleji, Alhaji Yusuf Maitama Sule, yana da ra’ayin baiwa jama’arsa da ƙasarsa gudunmawa, amma sai dai, ba shi da cikakkiyar masaniya game da harkar siyasa. Har sai a cikin shekarar 1948, a lokacin dawowarsa gida daga Legas, bayan zuwansu ziyara tare da sauran ɗaliban Babbar kwalejin elimantaren horas da malamai da ke Zariya (Higher Elementary Teachers College, Zaria), ya haɗu da shugaban Najeriya na farko, Dr. Nmandi Azikwe a jirgi, wanda suka tattauna da shi kan abubuwan da suka shafi siyasa. Wannan tattaunawa, ita ce farkon abin da ya fara jan hankalin Maitama zuwa harkokin siyasa. Tun daga wannan lokaci, ake ta fafatawa da shi.

A cikin shekarar 1950, su biyu; Alhaji Yusuf Maitama Sule, da Malam Bello Ijumu, suka kafa Ƙungiyar Siyasa ta NEPU. Wannan kuma ya biyo bayan tuntuɓarsa da  Malam Bello Ijumu ya yi, a gidansu da ke Yola, kan dacewar samar da wata jama’iyyar siyasa a daidai wannan lokacin. Sannan kuma shi malam Bello Ijumu, wanda ya ke Bayarabe ne a ƙabila, kuma mazaunin Sabon Garin Kano, ya buƙaci Maitama da ya saka wa wannan jama’iyya suna. Shi kuma ta nasa ɓangaren, Maitama sai ya ɗauko tsohon sunan rusasshiyar ƙungiyar siyasa ta su shi Malam Bello Ijumu, wato NEPA, ya cire harafin ƙarshe na A, ya maye gurbinsa da U.  Saboda haka sai sunan ya tashi daga NEPA mai ma’ana ta Northern Elements Progressive Association, ya koma NEPU da ma’ana ta Northern Elements Progressive Union. Jama’iyyar da daga baya ta zama cikakkiyar jama’iyyar adawa, wacce ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafuwar jamhuriya ta farko da kuma samun ‘yancin Najeriya daga hannun Turawa.

Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya taka muhimmiyar rawa wajen kafuwar wannan ƙungiya, duk da matsin lamba, musgunawa, muzantawa, da tozartawa da suka fuskanta daga ɓangaren sarakuna da kuma Turawan mulkin mallaka, Maitama, bai gajiya ba wajen zazzaga rubutun da ke tayar wa da shugabanni hankali, a cikin jaridar nan ta ‘Daily Commet’. Ya fuskanci barazanoni da dama, ciki har da kora daga aiki, amma cikin taimakon Allah, haƙa bata cimma ruwa ba.

Daga cikin irin waɗannan rubututtuka da ya yi, akwai wani da ya yi a cikin shekarar 1952, wanda ya yi wa wando ƙarfe isgilanci, saboda kiran Babban Residan (Senior Resident) na Kano da ake yi da Mai Wandon Ƙarfe. Haƙiƙa, wannan rubutu na Maitama ya yi matuƙar tayar da hazo daga dukkan ɓangarori guda biyu; Masarauta, da kuma ɓangaren Turawa, ta yadda sai da ta kai ga an rubuta takardar neman korar Maitama daga aiki aka tura zuwa Kaduna, don neman amincewa daga ofishin gwamnan lardin Arewa baki ɗaya. Amma, saboda zamowar Maitama, ya fito daga gidan Madawaki, sai ya zama yana da uwa a gidin murhu, saboda haka, korar, sai ta gagara. Amma fa da ƙyar ya sha.

Dukkan waɗannan abubuwa da ke faruwa, tsakanin Maitama, masarauta, da kuma Turawan mulkin mallaka, sam, bai shafi dangantakar da ke akwai tsakanin masarauta da mahaifin Maitama ba, wato Alhaji Sule, Ɗanmurin Madawakin Kano. A maimakon haka ma, sai ƙarin girma ya ke samu (Abba Sule), ta yadda sai da ta kai jallin an bashi riƙon gudunmar Dutse, a lokacin da hakimin Dutse, Suleimanu ɗan Nuhu (1923 – 1960), ya yi wata tafiya, sai Sarkin Kano Abdullahi Bayero (1926 – 1953), ya tura Abba Sule ya je garin Dutse ya riƙe garin, kafin dawowar hakimi Suleimanu ɗan Nuhu.

Jama’iyyu/Takarkarun Siyasa

1953 – 1966: Jamhuriyya ta farko, a wannan jamhuriyya, Alhaji Yusuf Maitama Sule, su biyu da Malam Bello Ijumu, suka kafa jama’iyyar siyasa ta NEPU, kamar yadda bayani ya gabata a sama. Sannan kuma daga baya, aka mayar da shi jama’iyyar NPC, aka kuma bashi takara cikin hikima da kuma sa’a, Allah ya bashi nasara ya ci zaɓensa na farko a matsayin Ɗanmajalisar Wakilai mai Wakiltar mazaɓar Birnin Kano.

A zaɓe na biyu na wannan jamhuriyya ta farko, ya sake tsayawa takarar Majalisar Wakilai ta tarayya, wannan karon kuma a mazaɓar Dawakin Tofa, nan ma cikin sa’a, ya samu nasara.

Sannan a shekarar 1949, ya sake tsayawa zaɓen a karon na uku, nan ma dai a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Mazaɓar Dawakin Tofa. A wannan zaɓe ma ya sake samun nasara.

1978 – 19853: Jamhuriyya ta biyu, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ya shiga jama’iyyar NPN, jama’iyyar da ya tsaya neman takarar kujerar shugabancin ƙasa. Amma aka roƙe shi ya janye wa shugaba Alhaji Shehu Shagari ba tare da sharaɗi ba.

1992: Ya shiga jama’iyyar NRC.

Siyasar Duniya

Alhaji Yusuf Maitama Sule, mutum ne masanin siyasar duniya, kamar yadda ya gabata, a zamanin da ya ke shugabancin kwamatin musamman na majalisar ɗinkin duniya kan yaƙi da wariyar launin fata, kusan ba bu wata ƙasa da bai taka ba. Tun kafin sannan, tun zamanin firimiya Abubakar Tafawa Ɓalewa, Maitama ya ke wakiltar Najeriya a wasu tarurruka, da kuma shiga tsakanin ƙasashe domin kawo sasanto ko kuma wasu ‘yan siyasa da suka gaza fahimtar junansu a ciki da wajen Najeriya. Bari mu ɗan gutsuro kaɗan daga ciki.

A zamanin shugabancin Firimiya Abubakar Tafawa Ɓalewa, Alhaji Yusuf Maitama, ya samu halartar taron da aka gabatar a garin Konakire (Conkery), ƙasar Gini (Gunea), a matsayin wakilin Firimiya Tafawa Ɓalewa. A wannan taro, ya yi gogayya da shugabanni irin su Kwame Nkruma na Ghana, Leopold Songhor na Senigal, da kuma Modibo Keita na Mali. Sai kuma taron Inuwar Afrika (All African Forum), wanda aka gabatar a cikin watan Juli (June) na shekarar 1960, a Adis Ababa.

Bayan wannan kuma, da shi aka je Majalisar Ɗinkin Duniya ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 1960. Wato kwana ɗaya kenan bayan samun ‘yancin kan ƙasa.

A zamanin mulkin Shehu Shagari (1979), Maitama ya wakilci Najeriya a Taron Tsarin Mulkin Ƙasar Zimbabuwe, wanda aka yi a Ɗakin Taro na Lankasta (Lancaster House), a garin Landan. Tabbas Ɗanmasani ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen sasanta tsakanin ɓangarori biyu masu rigima da juna, da ita Firimiyar Ingila ta wannan lokacin. Da zuwan Ɗanmasani wajen wannan taro, sai ya taras ita Firimiya ta harzuƙa har ma ta bayar da umarnin dakatar da gudanar da taron, saboda matsalar rashin amincewa da juna da su ɓangarorin biyu su ke nunawa. Farkon abin da ya fara yi a nan shi ne tabbatar da ci gaban taron, sannan kuma daga baya ya shiga tsakanin ɓangarori biyu da suka ƙi yarda da juna. Wato Robert Mugabe na jama’iyyar ZANU da kuma Joshua Nkomo na ZAPU. Sannan kuma dai a wannan shekarar ya jogaranci wata tawagar Najeriya zuwa sassanta rigimar cikin gida da ta ɓarke tsakanin shuwagabannin Kamaru.

Haka wannan ƙoƙarin nasa na kyautata dangantakar Najeriya da sauran ƙasashen duniya da ma shiga tsakanin riginginmun siyasar cikin gidan wasu ƙasashen ya ci gaba musamman ma lokacin Janar Muhammadu Sani Abacha, ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita dangantakar Najeriya da ƙasashen duniya musamman ma Amurka, da kuma maƙwabtan Najeriyar kamar irin su Nijar, Chadi, Kamaru, Benin, da sauransu.


Hoto, NDA Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, Tare da Shugaba Buhari a Bashi Digirin Girin Girmamawa (Dr.), daga NDA, Kaduna.

Ɗauraya

Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano. Haifaffen cikin Unguwar Yola ne, wacce ke tsakiyar ƙwaryar Birnin Kano. Mutum ne da Allah ya yi wa baiwa da kaifin basira, haƙuri, juriya, kawaici, gaskiya, riƙon amana, sadaukar da kai, da kuma fasaha da ƙwarewa wajen magana.

Ya bada gagarumar gudunmawa wajen kafuwa da kuma ɗorewar zaman lafiya a Najeriya, tun daga fafutikar ‘yancin kai har zuwa ɗorewarta a matsayin ƙasa guda.

Malamin makaranta ne da ya koyar a makarantar Midil; wato kwalejin Rumfa (Rumfa College) ta yanzu da ke garin Kano. Ɗansiyasa ne da ya fara siyasa tun lokacin Turawa, su suka kafa jama’iyyar talakawa ta NEPU. Tun sannan ya ke siyasa har zuwa jamhuriya ta huɗu.

Ɗan kishin ƙasa ne da ya yi aiki tare da sarakunan Kano da suka haɗa da Abdullahi Bayero, Muhammadu Sanusi I, Muhammadu Inuwa, Alhaji Ado Bayero, da kuma wanda yanzu ya ke kai, Muhammadu Sanusi II. Da shi aka kafa gwamnatin gwamnan farko na Kano, gwamna Audu Baƙo, ya kuma cigaba da baiwa sauran gwamnoni gudunmawa har zuwa kan na Yanzu, wanda shi ne cimakon na 18, a jerin gwamnonin da suka riƙe Kano.

Da shi aka fara gudanar da gwamnatin Najeriya ta farko, wacce ke da shugaban ƙasa da kuma firimiya, wato ya yi aiki da gwamnatin Zik da Tafawa Ɓalewa, Janar Yakubu Gowon, Janar Murtala Ramat Muhammed, Janar Olusegun Obasanjo, Alhaji Shehu Shagari, Janar Babangida da kuma Janar Muhammadu Sani Abacha, duk da cewa, dukkan gwamnatocin da aka yi a Najeriya, a gabansa aka yi su.

Ɗan siyasa ne shi a gida da wajen Najeriya. Ya bayar da gudunmawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al’ummu, garuruwa, ƙasashe a faɗin duniya.

Tabbas, wannan shi ne Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano. Malamin makaranta, Ɗansiyasa, kuma basarake. Sanin Mutum sai Allah.

Manazarta:


Abubakar A. T.  (2001). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello University Press, Zaria-Nigeria.

Northern Nigerian Publishing Company Ltd. (1979). Hausawa da Maƙwabtansu, Littafi na Biyu. Gaskiya Corporation, Zaria.

Sanusi N. M. (2009). Stories of Dutse Palace 1421 – 2009. An buga wannan littafi a maɗaba’ar jahar Jigawa.

The NEWS (2015). In Pictures NDA honours Alani Akinrinade, Maitama Sule. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: http://thenewsnigeria.com.ng/2015/09/in-pictures-nda-honours-alani-akinrinade-maitama-sule/

Wikipedia (2017). Maitama Sule. An ciro a shekarar 2017, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Maitama_Sule


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub