Janaral Olusegun Obasanjo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Janaral Olusegun Obasanjo, GCFRJanar Olusegun Obasanjo

Gabatarwa

Shugaba Olusegun Obasanjo, janaral ɗin sojan Najeriya ne mai ritaya kuma ɗan siyasa, sannan kuma manomi wanda ke da katafariyar gonar kiwon kaji. Ya yi shugabancin Najeriya har karo biyu. Karo na farko a matsayin shugaban soja wanda ya yi daga shekarar 1976 zuwa 1979. Sannan kuma a karo na biyu a matsayin shugaban farar hula daga 1999 har zuwa 2007.

Shugaba Obasanjo mutum ne mai son barkwanci, saboda haka kullum yana cikin wasa da dariya da mutane. Mutum ne mai matuƙar son ci gaban Najeriya. Yana riƙe da muƙaman sarautar Yarabawa masu taken ‘Balogun of the Owu’ da kuma ‘Ekerin Balogun’ na ƙabilar Egba daga cikin dangin Yarabawa.

Haihuwarsa

An haifi shugaba Obasanjo a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1937 a garin Abekuta ta jahar Ogun da ke tarayyar Najeriya. Ask Naija (2014), da Gistus (2014) sun ruwaito cewa Obasanjo ya girma a garin Owu. Gistus (2014), da PDP (2015), sun ruwaito cewa cikakken sunansa shi ne Olusegun Mathew Okikiola Aremu Obasanjo. Sunansa na farko ‘Olusegun’ yana nufin “Ubangiji shi ke da nasara”.

Olesegun Obasanjo bayarabe ne; wato kenan ƙabilar ‘Yoruba’ ne shi, wanda tana daga cikin manyan ƙabilun Najeriya guda uku wanda ake yiwa laƙabi da WAZOBIA.

Karatunsa

Britannica (2016), sun wallafa cewa, shugaba Olusegun Obasanjo ya yi karatunsa na firamare a ‘Baptist Boys’ High School’ da ke garin Abeokuta, a kudu maso yamman Najeriya, karatun da ya tsaya iya haka nan ba tare da samun damar shiga jami’a ba.

Shigarsa Aikin Soja

Tun gama karatunsa na firamare da sikandire da ya yi, shugaba Obasanjo ya ɗan yi aikin karatarwa kafin daga bisani ya tsunduma aikin soja a cikin shekarar 1958 lokacin da yake ɗan shekaru 21. Shugaba Obasanjo ya samu gajeren horo na tsawon wata shida a ƙasar Ingila (6-month Short Service Commission training at Mons Officer Cadet School in Aldershot in England), horon da bayan ya kammala shi aka ƙaddamar da shi a matsayin ofisa a rundunar soja ta Najeriya.

Sannan kuma ya sake samun wani horon a ƙasar Indiya a makarantar ‘Defence Services Staff College’, da ke Wellington da kuma ‘Indian Army School of Engineering’ duk a ƙasar ta Indiya. Ya riƙe ‘1 Area Command’ da ke Kaduna. sannan an yi masa ƙarin girma zuwa ‘Chief Army Engineer’, sai kuma aka yi masa kwamanda na yanki na biyu  (commander of 2 Area Command) muƙamin da ya riƙe a watan Yuli na shekarar 1967, sannan kuma ya sake samun wani horon a ‘DSSC, Wellington’.
A lokacin yaƙin basasa shugaba Obasanjo ya riƙe muƙamin kwamanda na rundunar soja ta 3 wanda aka tura shi zuwa Ower (commanded the Army’s 3 Marine Commando Division), wannan runduna ita ta yi nasarar kawo ƙarshen wannan yaƙi na basasa, inda su ‘yan tawaye suka zo suka miƙa wuya a hannunsa a cikin watan Janairun shekarar 1970 kamar yadda ya zo a (Britannica, 2016; PDP, 2015; Wikipedia, 2016).

Haka nan a shekarar 1975 ya riƙe muƙamin da ya yi daidai da na ministan ma’aikar ayyuka da gidaje (works and housing minister), daga baya kuma ya zama shugaban ma’aika na cibiyar majalisar ƙoli ta soja (chief of staff, supreme headƙuarters) kamar yadda ya zo a Ali-Dinnar (1999).

Zamowarsa Mataimakin Shugabansa Ƙasa

A shekarar 1975, shugaba Obasanjo ya zamo mataimakin shugaban soja na Najeriya, a lokacin yana da muƙamin birgediya janaral (Brigadier General) a soja. Zamowarsa mataimakin shugaban soja na Najeriya ya biyo bayan nasarar juyin mulkin da marigayi Murtala Mohammed ya yi a wannan shekarar.

Zamowarsa Shugaban Mulkin Soja

A ranar 13 ga watan Fabarairu na shekarar 1976, wani juyin mulkin da bai yi nasara ba shi ya kawo rasuwar shugaban soja marigayi Murtala Mohammed. Duk da cewa shi shugaba Obasanjo ya tsallake wannan rintsin duk da cewar yana daga cikin waɗanda aka yi nufin hallakawa a wannan lokacin.

Wannan rasuwa ta shugaba Murtala Mohammed, ita ta kawo yarjewar majalisar ƙoli ta sojan Najeriya (Supreme Military Council) suka naɗa shugaba Obasanjo a matsayin sabon shugaban mulkin soja. A tsawon mulkin da ya gudanar daga 1976 zuwa 1979, shugaba Obasanjo ya kafa tarihin cewa shi ne shugaban ƙasar da ya fara shirya zaɓe ya gudanar sannan kuma ya miƙa mulki a hannun farar hula a duk faɗin Afirka. Wannan abu da ya , ya ɗaukaka shi a ciki da wajen Najeriya.

Shigarsa Siyasa

Shugaba Olusegun Obasanjo, ya shiga siya tsundum a shekarar 1999, bayan fitowarsa daga gidan jarum, gidan da ya shiga sakamakon zarginsa da gwamnatin marigayi shugaban mulkin soja Muhammadu Sani Abacha ya yi masa na hannu a cikin yunƙurin aiwatar da juyin mulki.

Zamowarsa Shugaban Mulkin Farar Hula


Olusegun Obasanjo, GCFR

Shugaba Obasanjo ya jagoranci gwamnatin farar hula a Najeriya tun daga shekarar 1999 har zuwa 2007, baya cin zave da ya yi a ƙarƙashin tutar jama’iyyar PDP, wanda ya samu nasarar lashe zaɓen da aka gudanar da ƙuri’a mafi rinjaye wacce yawanta ya kai kashi sittin da biyu da ɗigo shida cikin ɗari na yawan ƙuri’un da aka kaɗa (62.6%) kamar yadda PDP (2015), ta ruwaito.

Haka nan kuma an sake zaɓensa a karo na biyu a shekarar 2003, zaɓen da shima ya ci da yawan ƙuri’un da suka kai miliyan goma sha ɗaya, kamar yadda ya zo a PDP (2015).

Lambobin Yabo da Girmamawa

Lambobin yabo da girmamawa da shugaba Obasanjo ya karɓa suna da yawa, amma dai muna iya ɗan tsakuro kaɗan daga ciki, waɗanda suka haɗa da:

  • Lambar yabo ta ‘GCFR’ (Grand Commander of the Order of the Federal Republic) wacce ita ce lambar yabo mafi girma a najeriya. Shugaba Obasanjo ya karɓi wannan lamba ta yabo a ranar 23 ga watan Satumba na shekarar 1981, kyautar shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari ya basu su biyu rak! Shi da Marigayi Nmadi Azikwe (Onlinenigeria, 2012).
  • Naijaurban (2012), sun ruwaito cewa Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta karrama shugaba Obasanjo da lambar yabo ta Jagorancin Duniya (Global Leadership Award) a shekarar 2012, a New York ta ƙasar Amurka.
  • Hakana nan gwamnatin tarayyar Najeriya ta karrama shugaba Obasanjo da lambar yabo ta ‘Outstanding Promoters Of Unity, Patriotism And National Development’ a shekarar 2014 kamar yadda Odunsi (2014), ya ruwaito.
  • Ya samu lambar yabo ta Uban Ƙasa (Father of the Nation Award), kyautar da ƙungiyar mata ‘yan jarida (NAWOJ) suka bashi a ranar 5 ga watan Nuwamba 2014, Ojetola (2014).
  • Kyautar yabo da gwamnatin jahar Ogun ta bashi kasancewar sa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi tsayin daka wajen ganin an samar da wannan Jahar. An bashi wannan kyauta a ranar 3 ga watan Fabarairun 2016 (Nwokolo, 2016).

Manazarta:


Ali-Dinar A.B. (1999). Obasanjo Biography. UNIVERSITY OF PENNSYLVANIA - AFRICAN STUDIES CENTER. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.africa.upenn.edu/Newsletters/irinw52799 .html

Ask Naija (2014). Who is Olusegun Obasanjo. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://ask.naij.com/politics/whoiso basanjo-i23799.html

Britannica (2016). Olusegun Obasanjo, President of Nigeria. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://www.britannica.com/biography/Olusegun-Obasanjo

Gistus (2014). Chief Olusegun Obasanjo (GCFR) – Biography. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.gistus.com/39739/chief-olusegun-obasanjo-gcfr-biography

Madukovich (2014). Nigeria: The Road To Centenary (8) – As Obasanjo Turns 77. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://madukovich.wordpress.com/tag/general-olusegun-obasanjo/

Naijaurban (2014). UN Honours Obasanjo With Global Leadership Award. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.naijaurban.com/un- honours-obasanjo-with-global-leadership-award/

Nwakolo E. (2016). Ogun honours Obasanjo, Afonja, others. Jaridar The Nation. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://thenationonlineng.net/ogun-honours-obasanjo-afonja-others/

Odunsi W. (2014). Outstanding Promoters of Unity, Patriotism and National Development. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.dailypost.ng/2014/02/24/centenary-fg-honour-100-nigerians-abacha-obasanjo-ojukwu-make-list-see-list/

Ojetola B. (2014). NAWOJ Honours Olusegun Obasanjo with Father of the Nation Award. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://nigerianecho.com/nawoj-honours-olusegun-obasanjo-with-father-of-the-nation-award/

Onlinenigeria (2012). National Honour. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.onlinenigeria.com/links/LinksReadPrint. asp?blurb=71

PDP (2015). Profile of Chief Olusegun Obasanjo, GCFR. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://peoplesdemocraticparty.com.ng/?page_id=439

T.I.N MAGAZINE (2016). General Olusegun Obasanjo Full Biography. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: http://www.takemetonaija.com/2015/01/eɗ-president-general-olusegun-obasanjo.html

Wikipedia (2016). Olusegun Obasanjo. An ciro a shekarar 2016, daga shafin: https://en.wikipedia.org/wiki/Olusegun_Obasanjo


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub