Alhaji Shehu Shagari

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Alhaji Shehu ShagariAlhaji Shehu Shagari

Gabatarwa

Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, mutum ne mai basira, haƙuri, sadaukar da kai, ƙasƙantar da kai, mai son jama’a, sannan kuma mai gaskiya da riƙon amana. Gogaggen ma’aikacin gwamnati ne wanda ya fara tun daga karantarwa a aji har zamowarsa shugaban ƙasa. Yakana, da kuma iya tafikar da al’amuran jama’a, suna daga cikin halayensa.

Ya fara aikin gwamnati da siyasa tun zamanin Turawa, da shi aka karɓi ‘yancin kai, da shi aka tsara kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1979; tsarin mulkin da ya juyar da akalar mulkin Nijeriya daga bin tsarin siyasar Ingila zuwa na Amurka, tsarin mulkin da ya baiwa shugaba cikakken iko. Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, cikin hukuncin Allah shi ne ya fara ɗare wannan kujera ta shugabancin Nijeriya ƙarƙashin wancan sabon kundin tsarin mulki. Saboda haka, a tarihin Nijeriya shi ne farkon wanda ya fara zama shugaban Nijeriya mai cikakken iko.

Ya yi aiki da salon tsarin mulkin Ingila (parliamentary system), ya yi aiki da gwamnatin soja, sannan kuma shi ya jagoranci aiki da sabon tsarin dimokuraɗiyya na shugaba mai cikakken iko (presidential system).

Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, malamin makaranta ne, sannan ma’aikacin gwamnati, ɗan siyasa, manomi, kuma basarake.

Haihuwa da Salsala

An haifi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a ranar 25 ga watana Fabarairu na shekarar 1925 a garin Shagari, ta Jahar Sakkwato a Nijeriya.

Sunan mahaifinsa, Malam Aliyu Shagari; Magajin Shagari na tara, wanda shi kuma ɗa ne ga Malam Ahmadu Rufa’i Magajin Shagari, shi kuma ɗan Malam Usman, shi kuma ɗan Malam Shekarau Magajin Shagari, shi kuma ɗan Malam Usman ƙanin Malam Muhammadu Shagari, wanda ya sari garin Shagari bisa umarnin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a shekara ta 1807 bayan nasarar jihadin Musulunci da Shehu Ɗanfodiyo ya jagoranta. Dukkansu Fulani ne daga ƙabilar Alibawa. Sannan kuma shi malam Muhammadu Shagari, wanda ya kafa garin Shagarin, da kuma ƙaninsa Malam Usman, dukkansu almajiran Shehu Ɗanfodiyo ne.

Mahaifyarsa kuwa mai suna Maryamu, ‘ya ce ga Sarkin Kabin Yabo Muhammadu Riskuwa, Hakimin Yabo. Ita ma mahaifiyar Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari Bafilatanar Yabo ce daga ƙabilar Fulani ta Wolorbawa.

Cikakken sunansa shi ne Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, Turakin Sakkwato. Ya gaji wannan suna ne na Usman daga kakan-kakan-kakansa, wato Malam Usmanu ƙanin malam Muhammadu Shagari. Asalin sunan kuwa, sunan sahabin Annabi Muhammadu (SAW) ne, kuma halifan Musulmi na huɗu. Sannan kuma daɗi a kan wannan, sunan mujadaddadi ne, wato Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.

Shagari kuma sunan garinsu ne, wanda shi kuma ya shigo cikin sunansa ne a lokacin da ya ke makarantar Elimantare aka saka masa shi, domin rarrabe tsakaninsa da wani malaminsa.

Turaki kuwa, muƙami ne na sarautar gargajiya. Saboda haka sai sunansa ya zama Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, Turakin Sakkwato.

Karatu

Tun kafin saka shi a makarantar allo, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya fara karatu a gidansu, abin da ake cewa, da karatu ya buɗi baki. Wannan kuwa saboda zamowar gidansu gidan malamai ne ga kuma sarauta. Amma tun yana ɗan shekaru huɗu da haihuwa aka saka shi a makarantar allo a garin na shagari.

 • 1931 – 1935: Makarantar Elimantare ta Yabo. Ya shiga wannan makaranta da nufin yin shekaru huɗu amma ya ƙare a cikin shekaru uku. Yadda abin ya faru kuwa shi ne cewa, bayan sun kammala zangon karatu na farko (aji ɗaya), sun yi jarabawar canjin aji (promotional examination), Alhaji Shehu Shagari ya samu nasarar cin jarabawar da za ta bashi damar shiga aji biyu. Amma saboda ƙanƙantarsa a lokacin, sai malamansa suka bar shi ya cigaba da zama a wannan aji don jikinsa ya ƙara girma, su kuma sauran ‘yan ajinsu sai suka ci gaba. Saboda haka sai ya zama shi yana aji ɗaya, sauran ‘yan ajinsu kuma sun ci gaba sun bar shi. Ana wannan mataki sai wani jam’in duba makarantu ya zo ziyarar aiki wannan makaranta, ya kuma shiga ajin da Shagari ya ke, da ya gwada shi sai ya ga yana da ƙwazo, kuma ga shi a aji ɗaya, sai ya ɗauki wani littafi mai suna Labarin Hausawa da Maƙwabtansu ya ba shi ya karanta. Da ya ga Shagari ya karanta wannan littafi kamar yadda ake so, sai kawai ya ɗauke shi ya mayar da shi aji uku.
 • 1935 – 1941: Makarantar Midil ta Sakkwato. Bayan kammala karatunsa na elimantare da ke Yabo, sai kuma ya samu nasarar cin jarabawar shiga makarantar Midil da ke Sakkwato.

  Abubuwa da dama sun faru a wannan makaranta ta Midil a tsawon zaman karatunsa. Daga ciki akwai canja masa suna daga Shehu Yabo, sunan da ya samo asali daga zamansa na Yabo, zuwa Shehu Shagari wanda shi ne asalin garinsu. Wannan kuma ta faru sakamakon dacewar sunan da na wani malaminsu mai suna Shehu Yabo, wanda shi kuma ɗan asalin garin Yabo ne. Saboda haka sai Malam Shehu Yabo ya sa aka canja suna, ya koma Shehu Shagari.

  A wannan makaranta ta Midil, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya yi karatu tare da fitattun mutane irin su Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Sheikh Halliru Binji, Ali Aƙilu, M. Bello Gusau, da sauransu.

 • 1941 – 1944: Kwalejin Gwamnati ta Kaduna. Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari ya samu nasarar shiga wannan makaranta ta Kwalejin Gwamnati ta Kaduna bayan cin jarabawa da ya yi daga makarantar Midil ta Sakkwato. Ɗalibai biyu ne kacal, suka samu nasarar cin wannan jarabawa ta zuwa wannan makaranta shi kansa da kuma Yusuf Kaduna.

  Bayan samun wannan nasara ta cin Jarabawa, Shehu Shagari sai ya ce shi fa alambaran, ba zai je wannan makaranta ba, wanda hakan ta kai ga malaminsu na Turanci, Mr. Shillington ya yi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin ya shawo kan Shehu Shagari amma ya gagara. Daga baya, malam Shehu Yabo da shugaban Makarantar Alhaji Dingyaɗi suma suka yi iya ka iyawarsu, amma Shehu Shagari ya ƙi fir. Daga ƙarshe dai, aka je aka sanar da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Abubakar III halin da ake ciki, wanda shi kuma ya sa aka kai masa Shehu Shagari, ya rarrashe ya nuna masa cewa zuwa wannan makaranta zai zamar masa alheri ga shi kansa da kuma jama’arsa.

  Babban dalilin ƙin amincewar Shehu Shagari na zuwa waccar makaranta ta Kwalejin Kaduna shi ne jin tsoron gurɓacewar tarbiyyar Musulunci da Imani kamar yadda ya faru da wasu daga cikin ɗaliban da suka gabace su, inda a ƙarshe suka fito suna tuhuma dangane da addinin Musulunci da sauran addinai. Su kuma ta nasu ɓangaren waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen ganin cewa Shehu Shagari ya je wannan makaranta shi ne cewa suna ganinsa a matsayin ɗalibi mai kaifin ƙwaƙwalwa, basira da kuma hazaƙa.

  Daga ƙarshe dai, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III, shi ya ɗauki Shehu Shagari da kansa ya kai shi Kaduna. Tafiyar da aka yi ta cikin kwana guda, inda suka yada zango suka kwana a garin Gusau. Bayan isar su Kaduna kuma suka sauka a Unguwar Sarki, inda daga baya aka saka dogarin Sarkin Musulmi ya raka Shehu Shagari zuwa makarantar.

  Yaƙin duniya na biyu, wani abu ne da ya yi matuƙar tasiri a duniya baki ɗaya, musamman ta fuskacin mayar da hannun agogo baya a dukkan ƙasashen da wannan faɗa ya shafa. Ƙasashen da Ingila ke yi wa mulkin mallaka a wannan lokacin, sun fuskanci koma baya ta kowa ce fuska, kamawa tun daga tafiyar hawainiya da ci gaban ilimi, walwala, ayyukan raya karkara da sauran su. Shehu Shagari, yana ɗaya daga cikin waɗanda wannan abu ya jefa cikin tasku. A wannan lokaci suna makaranta, wahalar da suka fuskanta ta haɗa da ƙarancin malamai Turawa, saboda ƙauracewarsu daga ajujuwan bayar da darasi zuwa ga  filin yaƙi, ƙaranci abinci, abin da ya haifar da makaranta ta gaza ba su abincin sai dai miya kawai, da sauran abubuwa makamantan wannan.

  Bayan jurewa dukkan irin wahalhalun da suka faru a wannan mataki na karatu da Shehu Shagari ya yi, ya samu nasarar rubuta jarabawarsa ta ƙarshe a wannan makaranta a cikin shekarar 1944.

 • 1944 – 1945: Kwalejin Horas da Malami ta Zariya. Bayan kammala karatunsa da kuma samun kyakkyawan sakamako a jarabawarsa ta ƙarshe a makarantar Kwalejin Kaduna, sai kuma ya ɗan fara samun horo na musamman a fannin kimiyya don bashi damar karantar da kimiyyar a nan gaba. Yana cikin wannan zama a wannan makaranta, sai kuma aka tura shi makarantar Midil ta Zariya don ya karantar da darasin kimiyya sannan a lokaci guda ɗalibi a Kwalejin Horas da Malamai ta Zariya. A wannan mataki ya samu horo a kan ilimin karantarwa tare da sauran ɗalibai, sannan kuma aka ci gaba da ba shi horo na musamman a fannin kimiyya.

Kwasakwasai

 • A cikin shekarar 1948, ya halarci kwas na musamman da aka shirya a Zariya domin malamai masu karantar da darrusan labarin ƙasa da tarihi.
 • A cikin shekarar 1952, ya samu zuwa garin Bauchi domin halartar kwas na musamman da ake shiryawa don ƙara horas da manyan malamai masu duba makarantu.
 • 1953, ya samu halartar wani kwas na musamman da aka shirya don horas da malamai a Ƙasar Ingila

Alhaji Shehu Shagari

Gogayyar Aiki

 • 1944 – 1945: Malamin Makaranta a Midil ta Zariya. Karantarwa, ita ce farkon aikin da Alhai Shehu Usman Aliyu Shagari ya fara. Bayan kammala karatunsa a Kwalejin Kaduna, sai aka tura shi Makarantar Midil ta Zariya don maye gurbin malamin da ya ke koyar da darasin kimiyya a makarantar, aikin da ya haɗa shi da ɗalibta a Kwalejin Horas da Malamai da ke Zariya.
 • 1945 – 1951: Malamin Makaranta a Midil ta Sakkwato. Bayan kammala samun horo a kan karantarwa da kuma kimiyya na tsawon shekara ɗaya da ya yi, an tura Shehu Shagari domin zamowa malami mai koyar da darasin kimiyya a makarantar Midil ta Sakkwato.

  Malam Shehu Shagari, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen haɓɓaka ilimin kimiyya a wannan makaranta. Ya ɗauki tsawon shekaru biyu yana koyar da wannan darasi na kimiyya kafin daga baya Turawan mulkin mallaka suka soke koyar da darasin kimiyya a duk faɗin Arewacin Nijeriya, abin da shi Malam Shehu Shagari ya ƙalubalanta kuma, ya haifar da dalilinsa na rage sha’awar ci gaba da karantarwa ya kuma rubuta takardar neman aiki da kamfanin Gaskiya wanda bayan ya samu nasara an ɗauke shi, hukumar gargajiya (NA) ta Sakkwato ta hana shi zuwa.

 • 1951 – 1954: Shugaban Makarantar Midil ta Argugun. Yana tsaka da aikinsa na karantarwa, wata rana cikin sherar 1951, sai Sir Ahmadu Bello Sardauna, lokacin yana kansilan Ilimi na Sakkwato ya aiko masa da ya je. Zuwansa wajen Sardauna sai ya shedawa Malam Shehu Shagari cewa, zai je makarantar Midil ya riƙe ta a matsayin shugaban makaranta na aro. Saboda rashin cin jarabawar da wanda ake sa ran ya zama shugaban ya yi. Sannan Sardauna ya umarci malam Shehu Shagari da ya je ya sanar da Sarkin Musulmi Abubakar III.

  Bisa bin umarni, sai malam Shehu Shagari ya tafi fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya sanar da shi. Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III ya yi matuƙar farin ciki da jin wannan magana, saboda haka ya yi wa malam Shehu Shagari addu’a sannan kuma ya buƙace shi da zamowa wakili na gari. Bayan komawarsa wajen Sardauna, sai shi Sardauna ya cire rawanin da ke kansa ya baiwa tela ya tsaga shi biyu, ya ɗauki ɗayan ya naɗa wa malam Shehu Shagari ya ce da shi ya tafi Argungun ya naɗa shi shugaban makarantar midil ta garin.

  Haƙiƙa malam Shehu Shagari ya bayar da gagarumar gudunmawa ta kowace fuska wajen ciyar da wannan makaranta gaba. Shi ne ya gina masallaci a wannan makaranta kuma ya zama limami. Sannan kuma a wannan makaranta ya fara rubuta waƙarsa ta farko mai taken Waƙar Haƙuri, sakamakon wani yanayi da ya samu kansa a ciki.

 • 1954 – 1958: Babban Malamin Duba Makarantun Lardin Sakkwato. Wannan muƙami ne da, wanda ke riƙe da shi alhakin kula da dukkan abubuwan da suka shafi makarantun lardin Sakkwato kamawa daga duba ɗalibai, malamai, da gine-ginen makarantu, da harkokin ilimi da na mulki su ke ƙarƙashinsa. Lokacin da Malam Shehu Shagari ke riƙe da wannan muƙami ya taka rawar da ta da ce.

  Wannan aiki nasa sai da ya haɗe da aikinsa na majalisa, saboda a wancan lokacin, an yardar wa dukkan ‘yan majalisun wakilan tarayyar Nijeriya su riƙe aikinsu na malinta da koma wane irin aikin ne, sannan kuma su riƙa zuwa Legas domin halartar zaman majalisa a lokacin da buƙatar zaman ta so.

 • 1954 – 1958: Majalisar Wakilai ta Nijeriya. An zaɓi Malam Shehu Shagari a matsayin ɗanmajalisar dokoki ta tarayya mai wakiltar Sokoto ta Kudu Maso-Yamma. Ƙarƙashin jama'iyyar mutanen arewa (JMA), A Turance kuma Northern Peoples Congress (NPC).
 • 1958 - 1966, Sakataren Firimiyan Tarayya a Majalisa. Lokacin da ya ke riƙe da wannan muƙami ne ya tsara dokokin da suka dace da zaman mutun ɗan ƙasa. Ya yi wannan aiki ƙarƙashin ofishin Sakataren Gwamnati Mr. Peter Stallard, tun kafin samun 'yancin kan Nijeriya. Ya kuma cigaba da wannan aiki har bayan samun 'yanci da shekaru shida.
 • 1958 Ɗanmajalisar Tarayya
 • 1959 - 1960, Ministan Ma'aikar Bunƙasa tattalin arziƙi.
 • 1960 Ministan Ɗaukar Ma'aikta da Horaswa.
 •  1962, Ministan harkokin cikin gida
 •  1965 - 1966, Ministan Ayyuka.
 • 1968, Jakadan Zaman Lafiya a Zamanin Yaƙin Basasa a ƙasashen Faransa, Italiya da Siwizlan. Waɗannan ƙasashe uku da aka ambata sun baiwa 'yan tawayen Biyafara gagarumar gudunmawa. Faransa, ita ce kanwa-uwar-gami da ke baiwa 'yan tawayen makamai da kuma sojojin haya. Italiya ma saboda zamowarta uwa ta addinin Kirista na Ɗariƙar Katolika, ta basu goyon baya da kuma tallafi. Haka ma Ƙasar Siwizlan. Saboda haka Najeriya ta wakilta Alhaji Shehu Shagari ya ziyarci waɗannan ƙasashe ya wayar musu da kai game da asalin rikicin, sannan kuma ya warware ƙarerayin da 'yan tawayen ke yi cewa ana yaƙar su ne saboda su Kiristoci ne. Daga cikin hujjojin da ya ke kafa musu akwai cewa ai shugaban na Najeriya a wannan lokacin Kirista ne kuma ɗa ga fitaccen fasto. Wannan jakadanci na Shehu Shagari ya haifar wa da Najeriya ɗa mai ido ta hanyar janye hannayen waɗacan ƙasashe, abin da ya kawo karya lagon yaƙin.
 • 1968, Kwamishinan Ma'aikatar Ɗaukar Ma'aikata da Horaswa na Jahar Arewa-Maso-Yamma. A wannan ma'aikata Alh. Shehu Shagari ya samar da daidaito wajen ɗaukar ma'aikata bisa la'akari da yankunan da ke wannan jaha, ya inganta walwala da jindaɗin ma'aikata, ya cusa hallayar ƙwazo, ɗa'a, da kuma gaskiya a zukatan ma'aikata, da sauransu.
 •  1969, Kwamishinan Ilimi a gwamnatin jahar Arewa-Maso-Yamma. Zamowar Alh. Shehu Shagari kwamishina a wannan ma'aikata, ya bashi cikakkiyar damar bunƙasa ayyukan waccan kwamiti nasa, wanda wannan shi ne maƙasudin da ya saka gwamnatin wannan jaha ta gayyace shi ya zama jami'inta. Tabbas, kwalliya ta biyan kuɗin sabulu, domin kuwa an gina makarantun firamare da sikandire tare da yi musu komai da yawansu ya ruɓanya na baya sosai.
 •  1970-1971, Kwamishinan Ma'aikatar Bunƙasa Tattalin Arziƙi ta Tarayya. Wannan shi ne karo na biyu da Alh. Shehu Shagari ya riƙe wannan muƙami; ya taɓa riƙe wannan ma'aikata daga shekarar 1959 - 1960 a zamanin Firimiya Tafawa Ɓalewa. Sai dai cewa a wannan karon an faɗaɗa ayyukan ma'aikatar ya zama har da sake ginawa da kuma raya garuruwan da yaƙin basasa ya rusa, tsugunnar da waɗanda rikicin ya kora da kuma sasanta tsakanin 'yantawayen na Biyafara da kuma hukumomin Najeriya.

  Zaman Alh. Shehu Shagari a wannan ma'aikata ya bayar da gagarumar gudunmawa. Ya samu nasarorin da suka kai har ga sakin fursunonin yaƙi tare kuma da yi musu afuwa.

 •  1971-1975, Kwamishinan Kuɗi na Tarayya.
 •  1976, Shugaban Hukumar Raya Birnin Sakkwato. Ɗaya daga cikin manyan nasarorin da Alhaji Shehu Shagari ya samu a zamansa na shugaban wannan hukuma, akwai gina katafariyar kasuwar Sakkwsto mai ɗauke da rumfuna dubu shida da aka tsara rukuni-rukuni har rukunnai goma sha shida, katafaren filin ajiye ababen hawa, masallaci da sauran su.
 •  1976 - 1979, Shugaban Kamfanin Fijo.
 •  1977-1978, Ɗanjalisar Nazarin Sabon Tsarin Mulki. Majalisa ce da tun asali shugaban Mulkin Soja na Najeriya Janaral Murtala Muhammed ya kafa, a matsayin Kwamatin Sake Tsara Sabon Tsarin Mulkin Najeriya. Daga baya, bayan wancan kwamiti ya gama nasa aikin; sai ya miƙa sabon Kundin Tsarin Mulkin a shekarar 1976 ga wanda ya gaji wannan kujera, Shugaba Olusegun Obasanjo. Shi kuma dai ya samar da wannan majalisa ta nazarin sabon tsarin mulki. Wannan majalisa ita ta samar da tsarin da ya canja akalar salon gudanar da mulkin Najeriya wanda ya tashi daga salon dimokuraɗiyyar Ingila na firimiya ya koma tsarin shugaba mai cikakken iko kamar yadda Amurka ke yi; wanda kuma wannan shi ne sabon kundin tsarin mulkin Najeriya na 1979 (1979 Constitution). Alhaji Shehu Shagari yana daga cikin waɗanda suka nazarci wannan kundi, sannan kuma shi ya zamo farkon wanda ya fara shugabantar Najeriya bisa wannan tsari na shugaba mai cikakken iko.
 •   1979 - 1983, Shugaban Ƙasar Najeriya: Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, shi ne mutum na farko da ya fara zama shugaba mai cikakken iko a tarayya Najeriya. An zaɓe shi a matsayin shugaban Najeriya a zaɓen da aka gudanar a cikin shekarar 1979, a ƙarƙashin tutar jama’iyyar NPN.

Ƙungiyoyi

 • Ƙungiyar Harkokin Matasa. A cikin shekarar 1946, Malam Shehu Shagari ya kafa Ƙungiyar Harkoki Matasa, wacce asalin sunanta na Turanci shi ne Youth Social Circle. Babbar manufar wannan ƙungiya ita ce, wayar da kan jama’a da kuma matsa ƙaimin kyautatuwar al’amuran jin daɗin rayuwar jama’arta.
 • Jama’iyyar Mutanen Arewa. Malam Shehu Shagari yana daga cikin mutanen da suka kafa wannan ƙungiya, wacce ake kiranta da Northern Peoples Congress (NPC) a Turance. Ƙungiya ce da aka kafa a cikin shekarar 1949. A Kaduna aka yi babban taron ƙaddamar da wannan ƙungiya. .
 • Ƙungiyar Kishin Ƙasa (National Movement), wacce daga baya ta rikixe ta zama jama'iyyar NPN a shekarar 1979.

Jama’iyyun Siyasa

Tun jamhuriya ta farko, Malam Shehu Shagari ya ke siyasa. A iya tsawon siyasarsa, malam Shehu Shagari ya shiga jama’iyyu kamar haka:

 • A jamhuriyya ta farko, malam Shehu Shagari ya zama ɗan jama’iyyar NPC, jama’iyyar da asalinta ƙungiyar walwala ce, daga baya kuma ta rikiɗe ta koma jama’iyyar siyasa.
 • A jamhuriyya ta biyu, Malam Shehu Shagari ya yi jama’iyyar NPN, jama’iyyar da ta faro daga ƙungiya mai suna ƙungiyar kishin ƙasa (National Movement). Sannan kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jama’iyyar tun daga tushe.

Alhaji Shehu Shagari yana jawabi

Gudunmawowi

 • 1967, Alh. Shehu Shagari sun kafa wani Kwamati a Lardin Sakkwato mai suna, Kwamatin Bunƙasa Ilimi a Lardin Sakkwato. Bayan zamowarsa ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kwamitin, Alh. Shehu Shagari shi ne sakataren wannan kwamiti.

  Babbar manufar kafa wannan kwamiti ita ce bunƙasa ilimin zamani a faɗin Lardin Sakkwato. Tunanin samar da wannan kwamiti kuma ya biyo bayan kisan Sardauna da aka yi; kafa kwamitin ya samu yarjewar mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III. Wannan kwamiti ya samu gagarumar nasarar samar da makarantun Islamiyya a matakin firamare da yawansu ya haura ɗari.

  Hakanan ta fuskacin sikandire, wannan kwamiti ya samu nasarar gina makarantu guda huɗu a kowace gunduma daga cikin gundumomin Lardin Sakkwato guda huɗu. An fara gina sikandire ta farko ƙarƙashin wannan shiri a cikin garin Sakkwato wacce aka saka wa suna  Ahmadu Bello Academy don girmama sir Ahmadu Bello. Sai kuma Kanta College da ke Argungu, wacce ita hukuma ce ta bayar da kyautar ginin. An kuma gina wata a Birnin Kebbi da aka kira Halliru Abdullahi. Sai kuma ta huɗunsu, Yawuri College, wacce itama hukuma ce ta bayar da kyautar ginin don ƙarfafar wannan shiri.

 • 1979 – 1983: Haƙiƙa, shugaban ƙasar Najeriya Alhaji Shehu Shagari ya bayar da gagarumar gudunmawa a fannoni daban-daban na rayuwa a lokacin gudanar da mulkinsa. Taskace waɗannan ayyukan alheri na raya ƙasa da Alhaji Shehu Shagari ya malala, babban aiki ne ba ƙarami  ba, saboda haka a wannan rubutu za a kalato wa mai karatu ɗan abin da ya samu.

  (a). Harkar bunƙasa tattalin arziƙi: A wannan fannin, shugaba Alhaji Shehu Shagari ya yi ƙoƙari matuƙa ta fuskacin fara biyan ɗimbin basussukan da gwamnatin soja ta shugaba Obasanjo ta gadar masa.

  (b) Fannin Ilimi: gwamnatin shugaba Alhaji Shehu Shagari ta bayar da gudunmawa wajen bunƙasa harkar ilimi a Najeriya. Daga cikin abubuwan da ta gudanar akwai:

 • Inganta makarantun kwalejojin taraya (federal colleges of education), da kuma ɗaukaka darajar wasu guda bakwai daga cikin talatin da shida zuwa masu bayar da digiri.
 • Gina wasu sababbin kwalejojin kimiyya (federal colleges of education technical) guda shida.
 • Gina jami’o’in kimiyya da fasaha guda bakwai kamar haka: Jami’ar Aikin Gona (federal university of agriculture), Abekuta; Jami’ar Fasaha (federal university of technology), Minna; Jami’ar Aikin Gona (federal university of agriculture), Makode; Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (Abubakar Tafawa Ɓalewa University), Bauchi; Jama’iar Fasaha (federal university of technology), Akure; Jami’ar Fasaha (federal university of technology), Yola; Jami’ar Fasaha (federal unversity of technology), Owerri.
 • Kafa Buɗaɗɗiyar Jami’a (Open University), Abuja.  
 • Samar da tsarin tallafin karatu a fannin kimiyya da fasaha.

  (c). Fannin wutar lantarki: Gwamnatin shugaba Alhaji Shehu Shagari ta gina tashoshin samar da wutar lantarki a garuruwan Jebba cikin jahar Neja; Apan da kuma Igben da ke cikin jahar Ikko (Lagos). Ta kuma kai hasken wutar lantarki zuwa ƙauyuka da dama a faɗin tarayyar Najeriya.

  (d). Fara gina babban birnin tarayyar Najeriya: Daga cikin muhimman nasarorin da gwamnatin shugaba Alhaji Shehu Shagari ta samu, akwai fara gina babban birnin tarayyar Najeriya wato Abuja. Daga cikin muhimman abubuwan da aka kammala akwai: gidan gwamnati (state house); filin jirgin sama (Nnamdi Azikwe International Airport); madatsun ruwa; tituna; gina unguwannin Area I da II da kuma samar musu da ababen more rayuwa kamar lantarki, ruwan sha, da sauran su; samar da motocin safa-safa; gina hukumar raya birnin tarayya (FCDA), da sauran su.

  (e). Harkar Masana’antu: A wannan fanni, shugaba Alhaji Shehu Shagari ya samu nasarar:

 • Ƙaddamar da matatar manfetur ta Kaduna (a cikin shekarar 1980).
 • Bayar da lasisin buɗe gidanjen manfetur masu zaman kansu.
 • Kafa masana’antun mulmula ƙarafa (steel roling companies) na Jos, Oshogbo da kuma Katsina.
 • Gina katafariyar masana’antar sarrafa tama da ƙarafa ta Ajakuta wacce a yanzu ke cikin jahar Kogi a tarayyar Najeriya.
 • Kafa masana’antun harhaɗa motoci: kamfanin harhaɗa mota ƙirar marsandi (ANAMCO) a garin Inugu; kamfanin harhaɗa mota ƙirar Boksuwaja a garin Ikko (Lagos); kamfanin harhaɗa mota ƙirar fet (Fiat) a garin Kano; kamfanin harhaɗa mota ƙirar siteya (Styer) a garina Bauchi; kamfanin harhaɗa mota ƙirar linda (Lyland) a garin Ibadan.

  (f). Harakar Muhalli: Gwamnatin Alhaji Shehu Shagari ta gina gidaje masu tarin yawa a faɗin tarayyar ƙasar nan. Kusan dukkan biranen jahohin tarayyar ƙasar Najeriya na lokacin guda goma sha tara, an gina musu gidaje. Irin waɗannan rukunin gidaje su ne suka zama gidajen da ake kira Shagari Kwatas kamar yadda ya ke a Kano da kuma wasu jahohin tarayyar Najeriya.

  (g). Kafa Ma’aikatar Tarbiyya da ɗa’a (ministry of national guidance). An kafa wannan hukuma da babbar manufa ta yaƙi da rashin ɗa’a tare kuma da gina ‘yan Najeriya a kan kyakkywar tarbiyya.

  (i). Kafa Ma’aikatar Matasa, Wasanni, da Haɓɓaka Jin daɗin Rayuwar Al’umma (ministry of youth and sport).

Sauka Daga Mulki

Juyin mulkin da sojoji suka gudanar a ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 1983, shi ne abin da ya kawo ƙarshen mulkin Alhaji Shehu Shagari bayan an sake zaɓen sa a karo na biyu, kuma a cikin jamhuriyya ta biyu, duk dai a ƙarƙashin tutar jama’iyyar NPN.

Manazarta:


Abubakar A. T. (2001). Maitama Sule Ɗanmasanin Kano. Ahmadu Bello University Press, Zaria-Nigeria.

Yakasai T. (2004). Tanko Yakasai, The Story of a Humble Life, An Autobiography, Volume I. Goverment Printers, Kano-Nigeria.

Muhammad da Isma'il. (2003). Tarihin Shehu Shagari. An buga a TPCS Ltd/Al-Rissalah Printing and Publishing Co. (Nig) Ltd. Domin M and I Essence Publi sher, Kaduna-Nigeria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub