Sarki Musulmi Ahmadu
Gabatarwa
Sarkin Musulmi Ahmadu ɗan Abubakar Atiƙu ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne Sarkin Musulmi na biyar. Ya gaji ɗan baffansa. An yi masa mubaya’a a masallacin Juma’a na Wurno, a cikin watan Rabbi’ul Auwal, kwanaki uku bayan rasuwar Sarkin Musulmi Aliyu ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo.
Sarakuna da wazirai, da sauran jama’a su suka haɗu suka yi masa mubaya’a, sannan kuma suka hore shi da tsayar da sunna da kuma nisantar bidi’a.
Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen kafa adalci a cikin gari. An samu aminci a lokacinsa, ya kawar da zalunci a harkar cinikayya. Shi ya ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da wata ƙabilar Auzinawa (Azbin). Sun yi yarjejeniya kamar haka: na farko su daina sayen gonaki; na biyu, su daina shigo da gunki; na uku, su amsa kiran sarakunansu; na huɗu, su amsa kiran sa idan ya neme su a kan wasu abubuwan da suka shafi jama’a kamar jihadi da sauran su; na biyar, su giramama shugabannin su.
Sarkin Musulmi Ahmadu, ya yaƙi garuruwa da dama daga ciki akwai Rambori, Tasawa, Gumi, da sauran su. Shi ne sarkin da ya faɗaɗa Daular Musulunci Arewaci.
Ya rasu a garin Chimmola, garin da ya zamar masa fadar mulkinsa kuma aka binne shi a can. Ya rasu ranar Juma’a a daidai lokacin sallar Juma’a a cikin watan Jimada Akhir. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru bakwai da watanni biyu da kwanaki ashirin da shida. Ya rayu tsawon shekaru sittin da ɗaya da kwanaki uku a duniya.
Manazarta:
Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.
Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.
Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).
Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.
Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.
Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).
Sarakunan Musulunci
- Shehu Ɗanfodiye
- Muhammadu Ballo
- Abubakar Atiƙu
- Aliyu Babba
- Ahmad Atiƙu
- Aliyu Ƙarami
- Ahmadu Rufa'i
- Abubakar Mai Raɓah
- Mu'azu
- Umaru ɗan Aliyu
- Abdurrahman
- Muhammadu Attahiru I
- Muhammadu Attahiru II
- Muhammadu Maiturare
- Muhammadu Tambari
- Hassan ɗan Mu'azu
- Abubakar III
- 1Ibrahim Dasuƙi
- 1Muhammadu Maciɗɗo
- Muhammadu Sa'adu
Tutocin Shehu Mujadaddi
Ƙofofin Sakkwato
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin