Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarkin Musulmi Muhammadu Attahiru I


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Attahiru na farko, ɗa ne ga Sarkin Musulmi Ahmadu, shi kuma ɗan Sarkin Musulmi Abubakar Atiƙu, shi kuma ɗan Shehu Usmanu Mujaddadi. Shi ne Sarkin Musulmi na goma sha biyu. Mulkinsa bai tsawaita ba. A zamaninsa Turawa suka shiga Sakkwato.

An yi masa mubaya'a a cikin watan Rajab, a garin Wurno a cikin gidan Waziri Muhammadu Buhari. Bayan an yi masa mubaya'a sai ya tashi daga Wurno ya koma Sakkwato ya zauna tsawon wata guda yana mai nufin tafiya Makka. A lokacin wannan zama nasa ne Sarkin Kano Aliyu Babba ya zo ya yi masa mubaya'a, sannan kuma ya auri 'yar Sarkin Musulmi Attahiru I.

Da sarkin Kano Babba ya ɗauki hanyar sa ta zuwa gida, bayan ya iso Gidan Goga, sai labari ya same shi cewa Turawa sun shiga Kano, sun kame ta. Sai tsoro ya kama shi, ya sulale cikin dare ba wanda ya san inda ya yi. Da gari ya waye rundunarsa ta yi haramar tafiya, aka neme shi sama da ƙasa aka rasa, sai suka kama hanyar su ta zuwa gida. A kan hanya suka haɗu da Turawa suka yi yaƙi, nan take Waziri Ahmadu ya yi shahada. Daga nan wasu suka ci gaba da tafiya, wasu kuma suka juya zuwa Sakkwato.

Shi kuwa Sarkin Musulmi Attahiru I, da labari ya iske shi sai suka yi shawara a tsakanin su, wasu daga cikin su suka ce, idan Turawan suka iso a nemi sulhu da su; wasu kuma suka ce a yaƙe su; wasu kuma a nasu ra'ayin, a yi gudun hijira tun gabanin haɗuwa da su.

Shi kuma Sarkin Musulmi ya karkata kan yin hijira, saboda haka suka shiga shirin yin hijira. Suka yi ta tattara awakai, shanu, jakuna, dawakai, raƙuma da wasun waɗannan na daga abubuwan buƙata ga matafiyi, sannan suka saka ranar tafiya. Suna tsaka da shirin tafiya, sai labari ya zo musu cewa Turawa sun zo dab da Sakkwato. Saboda haka suka katse shirin tafiya aka tayar da runduna, Sarkin Musulmi ya fita yaƙi bayan Sallar Jumu'a zuwa bayan gari. Aka tura masu leƙe suka duba hanya, ba su hangi kowa ba. Haka nan ma washegari, suka yi ta duban hanya har zuwa maraice, ba motsin kowa. Har jama'a sun fara faɗin cewa ba za su zo ba, sai daga baya suka bayyana.

Haka aka gwabza yaƙi tsakanin Musulmi da rundunar Turawa. Daga baya, Sarkin Musulmi Attahiru I, ya samu damar wuce wa da wasu daga cikin jama’arsa. Haka ya bi ta Ƙasar Kano har ya isa Gombe. Nan Turawa suka sake tare shi a wani gari mai suna Burmi, aka sake gwabza wani yaƙin da ya yi sanadiyyar shahadar sa.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub