Sakkwato Ƙofar Ƙware

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sakkwato Ƙofar Ƙware



Ƙofar Ƙware

Sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga wani gari da ake kira Kware. Dukkan mai zuwa wannan gari ta wannan ƙofa ya ke fita. Ɗan'autan Shehu Mujadaddi mai suna Isa wanda kuma aka fi kira da Autan Shehu, shi ne ya zama dagacin wannan gari a zamanin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

Manazarta:


Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council Sokoto. Sokoto-Najeriya.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub