Sarki Musulmi Mu'azu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sarki Musulmi Mu'azu


Gabatarwa

Sarkin Musulmi Mu’azu ɗa ne ga Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo, shi kuma ɗan Shehu Mujaddadi. Shi mutum ne mai tsananin kunya, adalci da kuma tsoron Allah. Shi ne Sarkin Musulmi na tara, sannan kuma jikan Shehu na ƙarshe da ya yi sarauta daga cikin ‘ya’yan Sarkin Musulmi Muhammadu Ballo.

An yi masa mubaya’a a masallain Juma’a na Wurno a cikin watan Rabbi’ul Auwal. Ya yaƙi Sabon Birni.

Ya rasu ranar Talata 27 ga watan Rabbi’ul Auwal. Ya yi sarauta ta tsawon shekaru huɗu da watanni tara.

Manazarta:


Adamu A. da Gwadabe M.M. (2005). Alhaji Muhammadu Macciɗo Abubakar III The 19th  Sultan of Sokoto The Bridge Builder. Amana Publishing LTD., 4, Sokoto Road, Zariya, Kaduna – Nijeriya.

Ballo M. (1974). Infaƙul Maisuri Fii Taarikhi Bilaadittukruur. Daarul Kutub, 1974.

Bukhari J. (1954). Nubzatun Ƙasiiratun Ala Taariikhi Sakkwato (Rubutun Hannu cikin Harshen Larabci).

Idris M. B. (2013). From Maratta to Sokoto. Sultanate Council, Sokoto - Nigeria.

Last M. (1977). The Sokoto Caliphate. Longman Group LTD., London. An buga a Maɗaba’ar Sheck War Tang, Hong Kong.

Waziri Junaidu. (Ba kwanan wata). Labɗul Multaƙaɗaati Minal Akhbaaril Muftariƙatu Fil Mu’allifaati. (Rubutun Hannu Cikin Harshen Larabci).


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub