Daular Sokoto

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kafuwar Daular Sakkwato


Gabatarwa

Daular Sokoto wacce kuma wasu lokutan akan kira Daular Usmaniya, ta samu ne bayan Jahadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo a farkon ƙarni na goma sha tara.

Can wani lokacin a baya, farkon ƙarni na goma sha shida, a kewayen Kogin Rima da Kogin Sokoto an yi wasu shahararriyar daula mai suna Kanta ko kuma Kebbi, wacce sarki Kanta Kota ya mulka. Wannan daula har sai da ta kai bunƙasar da tana iya nunawa Daular Barno ƙarƙashin mulkin ‘Mai Ali’ yatsa. Ƙarfin ikon wannan daula ya malalar har zuwa ƙasar Agadas. Wannan daula ta wanzu da wannan ƙarfi nata na tsawon ɗaruruwan shekaru, kamar yadda Last (1977) ya ruwaito.

A farkon ƙarni na goma sha takwas, tauraruwar wannan daula ta Kebbi ta dusashe, wata daular kuma mai suna Zamfara ta ɗaukaka. Wannan ya faru sakamakon harin da ita Daular Zamfarar ta kai wa ita Daular Kebbi kuma ta samu galaba a kanta. Waɗannan dauloli sun sun wanzu kowace na jin ta isa, duk da cewa ƙarfin Zamfara ya danne na Kebbi, amma dai kowacce daga cikinsu ta isa da kanta. Ita daular Kebbi tana yamma da Kogin Neja, Daulolin Zamfara Daular Gobir kuma suna daga gabashin Kogin na Neja.

Wannan Kogi na Neja a cikinsa jama’ar waɗannan dauloli uku suke gudanar da sana’ar kamun kifi. Duk da cewa akwai wasu kogunan guda biyu; Kogin Rima da Kogin Sokoto, amma dai su wadatar kifin da ke cikinsu ba isa sana’a bag a jama’a waɗannan dauloli.
Last (1977) ya ruwaito cewa, sannu a hankali waccar Daula ta Zamfara ta riƙa faɗaɗa, har sai da ta zamo ta fi kowace daula ƙarfin faɗa a ji a wannan nahiyar, wacce zuwa ƙarshen ƙarni na goma sha takwas, sai da ta mamayi yankin kogin Rima.

Wannan ƙarfi na daular Zamfara, bai tsawaita ba, daga baya Daular Gobir ta danne ta. Wannan daula ta Gobir sai da ta faɗaɗa har kusan tazarar da nisanta da Birnin Zamfara bai haura mil 25 ba daga arewa-maso-gabas.

A farkon ƙarni na goma sha tara, wannan daula ta Gobir ta durƙushe. Durƙushewar Daular Gobir, shi ne ya kawo kafuwar sabuwar Daular Musulunci mai helikwata a Sakkwato wacce ta haɗiye dukkan waɗancan dauloli guda uku masu ƙarfi (Zamfara, Kebbi da Gobir) da ma wasunsu, kamar yadda wannan rubutu ya ƙuduri aniyar yin bayani daki-daki.

Ƙasar Hausa

Kasancewar wannan babbar Daular Musulunci mai helikwata a Sakkwato ta tsiro ne a ƙasar Hausa, zai zamo abu mai matuƙar amfani a ɗan yi magana dangane da wannan yakin na ƙasar Hausa.

Ƙasar Hausa wani yanki ne da ke cikin Afirka. Shi ne yankin da Laraba suka kira ‘Biladi Sudan’, wanda ke da ma’ana ta garurun baƙaƙe. Yanki ne mai faɗin gaske a Afirka. A wannan yankin ƙasar Hausa ke da yanki mafi faɗi. Faɗinta yana farawa tun daga tafkin Chadi daga gabas kenan, ta runtuma har zuwa tsakiyar Nijar daga yamma kenan (wato idan ka je ka tsaya a bakin tafkin Chadi, sai ka sako gabanka yamma har sai ka kai tsakiyar Nijar duk a cin ƙasar Hausa ka ke, wanda kuma yanki ne na garuruwan baƙaƙe). Tana da faɗin sama da mil dubu ɗaya da ɗari biyar daga yamma, sannan kuma kuma sama da mil dubu biyu daga gabas (Johnston, 1967).

Wannan yanki na garuruwan baƙaƙe, ya sha samun kutse daga Larabawa waɗanda ke da manufa ta mulkin mulkiya sannan kuma suna tatsara arziƙin ƙasa tun wajen ƙarni na shida kafin daga baya a farkon ƙarni na ashirin Turawa su shigo. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa z aka ga cewa idan kwatanta wayewar ƙasar Haussa za ka ga cewa ta Larabawa, musamman ta fuskar al’adu da addini.

Zuwan Bayajidda ƙasar Hausa, na daga cikin abubuwan da ake kallo a matsayin tushen wayewar ƙasar Hausa. An samu kafuwar wasu masarautu guda bakwai da aka yi laƙabi da Hausa bakwai sakamakon zuwan Bayajidda. Waɗannan masarautu su ne; Daura, Kano, Rano, Zazzau, Katsina, Garun-Gabasa, da kuma Gobir.

Bayan kafuwar waɗannan masarautu, an kuma samun kafuwar wasu masarautun waɗanda suka yi ƙarfi. Su waɗannan masarautu su aka yiwa laƙabi da Banza Bakwai. Daga cikin irin waɗannan masarautu akwai Zamfara, Kebbi, da kuma Yawuri.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub