Ibrahim Narambaɗa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Makaɗa Ibrahim Narambaɗa A Fadojin Ƙasar Hausa


Alhaji Ibrahim Muhammad
Ɗanmadamin Birnin Magaji
08149388452, birninbagaji4040@gmail.com


Tsakure

Wannan takarda ta ƙuduri niyyar fayyace irin matsayi da rawar da Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali ya taka wajen kyautata al’amuran sarauta da hanyoyin samunta, da na gudanar da ita a wasu fadojin ƙasar Hausa. Domin cimma wannan manufa an saurari waƙoƙin makaɗa Narambaɗa sama da guda goma da nufin tsinkayen irin yadda sarauta take a ƙasar Hausa da yadda ake kokuwar nemanta idan ta faɗi da kuma yadda mu’amaloli sukan kasance a cikin masarautun ƙasar musamman a dauri. Ƙasar da Ibrahim Narambaɗa ya fito ƙasa ce mai yalwar arzikin ƙasa da na ma’adanai da kuma tsarin sarautu masu biyayya ga ɗabi’u da al’adun gudanarwa mabambanta. Wannan yanayi ya yi tasiri sosai wajen yadda ake gudanar da mulkin  sarautar gargajiya  a cikin Hausawa kamar yadda yake cikin waƙoƙinsa na fada. Daga wasu waƙoƙin Narambaɗa  da aka yi nazari an samu tarihin garuruwa da sunayen sarautar ƴaƴan sarki da na barori da yanayin ƙasa da kuma wasu al’adun sarakuna kamar a ƙasar Isa da Zazzau.

Tarihin kowace al’umma yana cikin adabinta na baka. Dalili shi ne, adabi shi ne madubin kyallo yadda ake tafiyar da rayuwa a al’adance. Hausawa ma tarihinsu naɗe yake a cikin adabinsu. Waƙar baka wani rumbu ne na adana tarihin al’ummar Hausawa, kan haka ne aka nemi sanin yaya al’ummar Hausawa suka ginu ta fuskar mulki irin na Sarauta. Yunƙurin wannan ya samo asali asali ganin tarihin samar da sababbin jihohi da ƙananan hukumomin mulki na wannan zamani, na son ya dusashe tarihin  tsarin mulkin ƙasar Hausa a ƙarƙashin Sarakunan mulkiirin na gargajiya kafin zuwan baƙi a ƙasar Hausa. A lura da cewa, rabon ƙasa a dalilin samar da sababbin jihohi da ƙananan hukumomi ya sa wasu sarakuna ƙirƙira sababbin sarautu domin a tafi da zamani. Amma waiwayen da wannan tsokaci zai yi shi ne, yaya waƙoƙin makaɗan fada suka fitar da taswirar yankunan ƙasar Hausa da irin tsarin mulkinsu, da tarihin masarautunsu a wancan zamani? Nazari da sharhi a cikin waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa ya ba da amsar wanann tambaya. Taskar Waƙoƙin Narambaɗa ta adana irin kokowar Sarauta da ta shiga tsakanin magadan Sarautu daban-daban na ƙasar Hausa musamman a yankin Zamfara da kuma yadda suka mulki yankunansu. Hanyoyin da aka bi wajen tattara bayanan bincike kamar tattaunawa da wasu daga cikin sarakunan da ke raye, da kundayen  tarihin da aka nazarta, sun nuna, ba don irin waɗannan waƙoƙin makaɗan fada ba, kamar su Narambaɗa, da tarihin sarautun ƙasar Hausa da yadda tsarin mulkinsu ya kasance a da, da kuma a yanzu, ya ~ace a kundin tarihin al’ummar Hausawa. Maida hankali ga ƙumshiyar abinda su Narambaɗa suka adana a cikin waƙoƙinsu, zai zama waiwaye adon tafiya ga tafiyar tsari mulki irin na sarauta a ƙasar Hausa

Latsa nan ka Juyi Takarda

Latsa nan domin sauraron waƙoƙin Narambaɗa


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub