Taron Shuwa Arab Lagos

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Taron Wata-Wata Shuwa Arab, Lagos


Gabatarwa

Masarautar Shuwa Arab ta Jahar Lagos tana gudanar da taro a duk ƙarshen wata. A wannan taro ne al’ummar Shuwa Arab na Jahar Lagos suke zuwa fadar Sultan su taru. Taro ne da yake bai wa sarki damar jin ƙorafi daga bakin mai ƙorafi kai tsaye, haka nan shi ma mai ƙorafin yake samun cikakkiyar damar isar da ƙorafinsa ga sultan kai tsaye.

Warware rigingimu da suka shafi auratayya, rigima tsakanin mutum da mutum, matsalar bashi, da sauran al’amuran da suka shafi al’adu da addinin al’ummar Shuwa Arab su ne abubuwan da wannan masarauta take gudanarwa.

Manazarta:


Tattaunawa da Sultan Jibril Yahya Ibrahim a Fadarsa da ke Lagos a Ranar Asabar 29/2/2020

Tattaunawa da Alhaji Ahmad Turakin Masarautar Shuwa Arab ta Lagos a Fadar Masarautar da ke Lagos a Ranar Lahdi 1/3/2020  
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:


Latsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafinSauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub