Tatsuniya: Alhaji da Hajiya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Auren Barewa da Mutum


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wata barewa da ta rikiɗe da zama mace mai kyawun gaske; son-kowa ƙin-wanda ya rasa. Wata rana sai ta ɗauki akushinta (kwatashi) ta kai shi tsakiyar karofi ta ajiye. Sai ta ce da mutanen da ke wurin, “duk wanda ya ɗauki tsakuwa, ya jefa ta daga nan (ta tsaya a daidai wani guri), ta buɗe wannan akushi, to shi zai zama mijina”.

Da mutane suka ji haka, sai suka yi ta jefa tsakuwa. Wannan ya jefa bai buɗe ba, wancan ya jefa bai buɗe, sai can daga ƙarshe aka samu wani ya yi sa’a ya jefa, akushin ya buɗe.

Sai wannan barewa ta ce, “yawwa, yanzu na samu miji”. Saboda haka sai suka rankaya tare da wannan mutum zuwa garinsu dan a ɗaura musu aure da wannan mutum. Bayan an ɗaura aure, sai ta tare a gidan mijinta.

Duk sanda ranar girkinta ta zagayo, akan tura ta gonad an ciro kuvewar miya. Idan ta je gonar sai ta yi birgima a ƙasa, ta rikiɗe ta koma barewa, ta kira ‘yan’uwanta ta hanyar rera waƙa kamar haka:

Cinkalkalkal, cinkalin kalaya
Turmin ‘yankale ya yi furen ceɗiya
Tudu na korar tudu da ƙaho
Ban da kwatsa-kwatsa
Ban da ƙanana.

Idan ‘yan’uwanta suka ji haka sai su fito, su zo su taru, su cinye kuɓewar da take gonar. Sai su yi bankwana da ita su koma gida. Ita kuma sai ta yi birgima ta koma mutum, ta ɗauki zanenta ta ɗaura, ta koma gida tana cewa, “ai dama da gangan aka tura ni ciro kuvewar nan, gashi nan na je ban samo komai ba”.

Da mijin nata ya ga haka, wata rana sai ya bi bayanta bata sani ba. Da isarsa gona sai yaga tana birgima. Bayan ta gama birgima sai ya ga ta koma barewa. Daga nan kuma sai ya ji tana waƙa, bayan gama waƙartata, sai ya ga bareyi sun fito suna cin kuɓewar da take gonar. Shi kuma da ya ga haka sai ya fasa su. A lokacin da yake fasa su, ya ga matar tasa ita ma ta gan shi. Daga nan sai ya dawo gida.

Da barewar nan ta ga abin da ya faru, sai ta yi wuf, ta yi birgima ta koma mutum ta ɗebi kuɓewa ta nufi gidan mijin nata. Da isar ta gida sai mijin ya ce:

Miji: “Wacece wannan?”
Barewa: “ni ce”.
Miji: “ina za ki?”
Barewa: “ɗaki”.
Miji: “a’a, koma daji”.
Barewa: “na ƙi”.

Daga nan sai ya ɗauki sanda ya bita da gudu, ya kora ta daji. Tun daga wannan lokaci bata sake koma masa gida ba.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub