Tatsuniya: Baban Rogaji da Wasu Samari Biyu

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Baban Rogaji da Wasu Samari Biyu


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari akwai wani attajiri mai garken shanu. Wata rana yana zaune a ƙofar gidansa, sai wani saurayi ya zo ya ce zai yi masa kiwon shanu shi kuma ya biya shi. Sai Baban Rogaji ya ce da saurayin nan, yaro za ka iya kiwon nan kuwa? Sai saurayin nan ya ce da Baban rogaji zai iya. Sai Baban Rogaji ya ce to idan za ka iya ga sharruɗan kiwon. Na farko, idan kuka shiga daji, kai za ka bi hanya mai ƙaya su kuma su bi hanya mai kyau. Na biyu kuma idan kuka je gindin ɓaure, su za su ci nunanne, kai kuma za ka ci ɗanye. Na uku kuma, idan kuka je shan ruwa, su za su sha ruwa mai kyau, kai kuma za ka sha gurɓataccen ruwa. Na huɗu kuma, idan kuka je gurin kwanciya, su za su kwanta a fili, kai kuma za ka kwanta a kan ciyawa. Sai saurayin nan ya ce zai iya. Sai Baban Rogaji ya saya masa takalma, ya bashi sanda, ya bashi shanu.

Saurayin nan ya fita kiwo, a kan hanyarsu ta tafiya, sai ya koma gefen hanya su kuma shanun ya saka su a tsakiyar hanya. Da suka shiga daji sosai, sai suka hangi ɓaure, da suka je gindin ɓaure, sai ya hau bishiyar, ya kaɗo musu nunanne, shi kuma ya ci ɗanye. Da suka je bakin rafi gurin shan ruwa, sai da ya bari sun sha ruwa mai kyau sun ƙoshi, shi kuma ya sha gurɓatacce. Daga nan sai gurin kwanciya, sai da ya sama wa shanun nan guri mai kyau, shi kuma ya shiga ciyawa ya kwanta. Haka ya yi ta yi har lokaci ya yi, ya dawo gida.

Da suka iso gida, sai Baban Rogaji ya tambayi shanu yadda aka yi. To dama cikinsu akwai wata mai magana. Sai ta kada baki ta ce:

Ummo, ummo.
Baban rogaji kiwo ya yi kyau.
Hanya mai kyau mu muka bi.
Ɓaure mai kyau mu muka ci.
Ruwa mai kyau mu muka sha.
Guri mai kyau mu muka kwanta.

Da Baban Rogaji ya ji haka, sai ya ce yaro ka cika alƙawari. Sai ya shirya masa goma ta arziƙi ya sallame shi. Shike nan daga nan sai shima wannan saurayi ya je ya kafa nasa garken.

Da wani lokacin tafiya kiwo ya zagayo, sai wani saurayin ya zo ya ce shi ma zai je kiwon. Sai Baban Rogaji ya ce da shi anya kuwa samari za ka iya? Sai saurayin nan ya ce zai iya. Sai Baban Rogaji ya ce to idan za ka iya ga sharruɗan kiwon. Na farko, idan kuka shiga daji, kai za ka bi hanya mai ƙaya su kuma su bi hanya mai kyau. Na biyu kuma idan kuka je gindin ɓaure, su za su ci nunanne, kai kuma za ka ci ɗanye. Na uku kuma, idan kuka je shan ruwa, su za su sha ruwa mai kyau, kai kuma za ka sha gurɓataccen ruwa. Na huɗu kuma, idan kuka je gurin kwanciya, su za su kwanta a fili, kai kuma za ka kwanta a kan ciyawa. Sai saurayin nan ya ce zai iya. Sai Baban Rogaji ya saya masa takalma, ya bashi sanda, ya bashi shanu.

Da suka fita bayan gari, saurayi ya tabbatar babu wanda yake ganinsa, sai ya kora shanu cikin ƙaya shi kuma ya bi hanya mai kyau. Suna ta tafiya a haka har suka kai cikin daji gurin da ɓaure yake. Da suka je bishiyar ɓaure, sai ya hau kan bishiya ya riƙa tsinko ɗanye yana jefo musu shi kuma yana cin nunanne. Haka nan ma da suka je gurin shan ruwa sai da ya fara sha sannan su ya basu gurɓataccen ruwa. Bayan an gama kiwo da aka je gurin kwanciya, sai ya share guri ya kwanta su kuma ya kora su cikin ciyawa. Haka ya yi ta yi har lokacin komawa gida ya yi.

Da saurayin nan ya dawo gida sai Baban Rogaji ya yi masa sannu da zuwa sannan ya tambaye shi labarin kiwo. Sai saurayin nan ya ce ai duk yadda ka ce a yi, haka aka yi. Shike nan sai ya juya ya tambayi shanun nan. Sai mai maganar nan ta fara da cewa:

Ummo, ummo.
Baban Rogaji kiwo bai yi kyau ba.
Hanya mai ƙaya mu muka bi.
Ɓaure ɗanye mu muka ci.
Ruwa gurɓatacce mu muka sha.
Gurin barci mai ƙaya nan muka kwanta.

Da saurayin nan ya ji haka sai kunya ta kama shi. Shi kuma Baban Rogaji sai ya kawo jakuna ya bashi. Da aka bashi jakunan nan, sai kutare suka bishi suna yi masa gwalo ƙudaje suna bin sa.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub