Tatsuniya: Ɓarawon Gwal

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Ɓarawon Gwal


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani mutum, wata rana ba shi da kuɗi, sai ya samu labarin wata mayya kuma tana da gwalagwalai na ado. Sai mutumin nan ya shirya zuwa sata gidan matar nan, sai ya hau dokinsa. To dama yana da karnuka guda uku a gidansa, a cikinsu akwai mai suna Kasau, da kuma mai suna Cinyau, da kuma mai suna Lasau. Sannan kuma yana da mata biyu. Da zai fita, sai ya ɗaure karnunkan nan a gida, kuma ya ce kar a sake su.

Da ya fito daga gida sai ya tafi wajen masu fasa dutse, sai suka ba shi dutse ya saka a jakarsa. Sannan ya wuce wajen masu faskaren itace, suma suka bashi ya saka a jaka, sai kuma ya je wajen masu sai da ƙwai, suma suka ba shi ya saka a jaka. Daga nan sai ya rankaya sai gidan mayyar nan.

Da zuwansa gidan mayyar nan sai ya yi sallama sannan ya ce da ita, shi baƙo ne yana neman gidan da zai riƙa yin aikin wanke-wanke. Da matar nan ta ji haka sai ta ce to ba komai ya zo ya riƙa yi mata wanke-wanken.

Ana nan, ana nan, wata rana da daddare, matar nan ta shiga ɗaki tana barci, sai mutumin nan ya laɓaɓa ya shiga ɗakin da ta ke ajiye gwalagwalai ya ɗebo ya je ya hau dokinsa. Bayan ya hau dokin zai fita, a garin sauri sai dokin nasa ya bugi wani bulo, sai bulon ya ɓalle daga jikin gini, sai ginin ya zube. Ƙarar zubar ginin nan sai ya farkar da mayyar nan. Tana leƙowa sai ta ga mutumin nan da kaya a kan doki. Sai shi kuma ya zaburi dokin nan ya fita da gudu, ita kuma mayyar nan sai ta bishi, yana gudu a kan doki, ita kuma tana bin sa.

Da mutumin nan ya ga alamar mayyar nan za ta kamo shi, sai ya buɗe jakar nan ya fito da dutsen nan ya jefe ta da shi, saura ƙiris ya buge ta, amma ta samu ta tsallake, ta kuma ci gaba da bin sa da gudu. Da ya ga ta tsallake, sai ya sake fitowa da itacen nan ya sake jifanta da shi, shi ma ta samu ta tsallake. Yana gudu tana bin sa. Can da ya ga babu dama sai ya fito da ƙwan nan ya jefe ta da shi, ita kuma ta cafke ƙwan nan ta shanye.

Mutumin nan dai gudu ya ke yi a kan dokin, mayyar nan kuma tana bin sa har sai da ta iso mutumin nan ta kama ƙafar dokin nasa ta cinye.

Da mutumin nan ya ga mayyar nan ta kama ƙafar dokin nan ta cinye, sai ya sauka daga kan dokin ya ci gaba da gudu a ƙasa har sai da ya kai gindin wata bishiya ya kama ya haye kan bishiyar nan. Da ya hau kan bishiyar sai ya kama kiran karnukan nan nasa yana cewa, Kasau, Cinyau, Lasau. Kasau, Cinyau, Lasau. Can sai karnukan nan suka fara haushi.

Da amaryar mutumin nan ta ji karnuka sun fara haushi, sai ta ce da uwargidan, ni fa zan kunce karnukan nan. Sai uwargidan ta ce ita babu ruwanta a ciki.

Can kuma da mayyar nan ta gama cinye dokin nan, sai ta sake biyo mutumin nan. Da mutumin nan ya ga mayyar nan ta kusa zuwa gindin bishiyar da ya ke, sai ya sake kiran karnunkan nan, ya sake cewa da su, Kasau, Cinyau, Lasau. Kasau, Cinyau, Lasau. Sai karnukan nan suka sake yin haushi. Da amarya ta ji haushin karnukan nan sai kawai ta sake su. Tana sakinsu, sai suka fita da gudu, har sai da suka riga mayyar nan zuwa gindin bishiyar nan, suna zuwa, sai mutumin nan ya sake cewa, Kasau, Cinyau, Lasau. Kasau, Cinyau, Lasau. Saboda haka mayyar nan tana zuwa gindin bishiyar nan sai Kasau ya kasheta, shi kuma Cinyau ya cinye ta, Lasau kuma ya lashe sauran jininta da ya zuba a gurin.

Daga nan sai mutumin nan ya sauko daga kan bishiyar nan, ya shiga kasuwa ya sayi nama, ya sayi ƙuli/ƙarago, ya sayi suturu, ya tafi gida. Yana zuwa gida sai ya ce da matan nan nasa, wacece ta kunce karnukan nan? Sai uwargida ta ce amaryarka ce ta kunce su, sai ya ce to kowacce ta tafi ɗakinta. Sai ya fito da ƙuli/ƙaragon nan ya baiwa uwargida, ita kuma ta karɓa ta shiga ɗaki tana ci. Ita kuma amarya ta shige nata ɗakin tana cewa ba ita ta kunce karnukan nan ba, sai ya bita ɗakinta, ya fito da suturar nan ya bata ta saka. Da uwargida ta leƙo ta ga kayayyakin nan a jikin amarya, sai ta ce, oho! Dama abin haka ne? Sai ta ce to ni na tafi gidanmu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub