Tatsuniya: Ɓarayin Rake

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Ɓarayin Rake


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata rana ce dai, sai makaho, da kuturu, da gurgu suka tafi satar rake. Da suka je gonar rake, sai suka kama shan rake. Sai makaho ya ce da su, a ɓare mini, a mirmire mini, sa saka mini a bakina na ji daɗi. Sai suka samu rake suka ɓare, suka mirmire shi, suka sakawa makaho a bakinsa. Sai ya sake cewa a ɓare mini, a mirmire mini, saka mini a bakina na ji daɗi. Sai suka samu rake suka ɓare, suka mirmire shi, suka sakawa makaho a bakinsa.

Suna cikin shan rake suna jin daɗi, can sai suka hango mai gona ya ciri wani ƙaton rake. Sai duk suka sulale suka bar makaho zaune a cikin gona. Mai gona ya laɓaɓo har ya zo kusa da makaho, da makaho ya ji motsi sai ya ce, a ɓare mini, a mirmire mini, sa saka mini a bakina na ji daɗi. Sai mai gona ya fito da wannan ƙaton rake ya rafka wa makaho a gadon bayansa, sai ya ce, kai uwaku, ya ku ke yi min shegantaka. Yana rufe baki sai ya sake jin saukar wannan rake a gadon bayansa. Yana shafa dama da hagunsa sai ya ji ba kowa, yana kai hannu bayansa sai ya ji wani mutum daban, ai kuwa da makaho ya runtuma da gudu, sai ya riƙa gudu yana faɗuwa, da haka har ya fito wajen gona. Su kuwa kuturu da gurgu me su ke yi in ban da dariya.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub