Tatsuniya: Gizo da Noman Gyaɗa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Gizo da Noman Gyaɗa


Wata rana Gizo da Ƙoƙi, abin duniya ya yi musu zafi. Sai Ƙoƙi ta ce da Gizo, “Ina ga da za mu yi noma da mun samu sauƙi”. Da Gizo ya ji haka sai ya ce, “Ƙwarai hakan ya dace”. Sai Ƙoƙi ta ce, “to me ka ke ganin zamu noma? Mu shuka shinkafa ne, ko alkama, ko kuma acca?” Sai Gizo ya ce, “a’a, mu shuka gayaɗa kawai”. Sai suka yarda akan cewa za su shuka gyaɗa. Amma ashe shi Gizo yana nufin ya yiwa Ƙoƙi wayo da wannan shawara tasa.

Da aka tashi yin shuka, sai Gizo ya ce da Ƙoƙi, ai ba a shuka gyaɗa sai an soya ta. Sai Ƙoƙi ta amince ta soya gyaɗa, ta baiwa Gizo ta ce ya je ya shuka. Da Gizo ya je gona dan yin shukar gyaɗa, sai ya ɗaura lilo a jikin bishiya, ya hau lilon nan yana cin gyaɗa, yana rera waƙa kamar haka:

……………………….

Da haka-da haka, yau ya je gona, gobe ya je, har wannan gyaɗa ta ƙare, ba tare da ya shuka ba.

Da damina ta yi nisa, sai ƙoƙi ta fara tambayarsa maganar gona, shi kuwa Gizo sai ya hau bada labari yana cewa, “Ai gonar nan ta yi kyau sosai”.

Da kakar gyaɗa ta fara yi, sai Ƙoƙi ta ce da Gizo ya fara ciro musu wannan gyaɗa su riƙa ɗan taɓawa kafin a farɗe ta. Saboda haka a duk lokacin da Ƙoƙi ta buƙaci gyaɗa sai Gizo ya je gonar mai gari ya yago ya kai mata. Sannu a hankali Gizo ya kusa cire gyaɗar gonar mai gari baki ɗayanta.

Wata rana sai mai gari ya gane cewa ana cirar masa gyaɗa, saboda haka sai ya zuba masu gadi a gonar suka ɓoye a gurin da ba mai ganinsu. Can sai ga Gizo ya zo cirar gyaɗa. Caraf, masu gadin nan suka cafke Gizo, suka tafi da shi gurin mai gari. Daga nan aka yanke masa hukunci, aka kore shi daga gari.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub