Tatsuniya: Gizo da Ɗanrago da Ɗantaure

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Gizo da Ɗanrago da Ɗantaure


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Gizo ne dai suna zaune da Tinkiya da Akuya a gari ɗaya. Wata rana Gizo yana so ya ci nama, sai ya ce da ɗanrago ya zo su tafi ci rani. Sai ɗanrago ya ce da Gizo, sai na je na gaya wa babata. Sai Gizo ya ce da shi ya je ya gaya mata, da ɗanrago ya je sai tinkiya ta ce da shi a dawo lafiya.

Shike nan sai Gizo da ɗanrago suka shirya suka tafi. A kan hanyarsu ta tafiya sai ɗanrago ya tsinci cokali, sai Gizo ya ce da shi kar ya ɗauka. Sai ɗanrago ya wuce bai ɗauka ba. Sai suka ci gaba da tafiya, bayan sun ɗan yi nisa da gurin da ɗanrago ya tsinci cokali, sai suka ga shinkafa da miya. Sai Gizo ya ce da ɗanrago, kai ɗanrago ina cokalin nan? Sai ɗanrago ya ce, ai kai ka ce kar na ɗauka, na baro shi a can. Sai Gizo ya ce da ɗanrago, maza garzaya ka ɗauko. Da Gizo ya ga ɗanrago ya tafi sai ya tsugunna ya kama cin shinkafar nan sai da ta kusa ƙarewa sannan ya rage wa ɗanrago. Da ɗanrago ya dawo, sai Gizo ya ce da shi, a ina ka maƙale ne? Ai na yi zaton ba za ka dawo ba, amma ga wata ‘yar ragowa nan na bar maka. Sai ɗanrago ya saka baki ya cinye.

Daga nan sai suka ci gaba da tafiya, ba su yi nisa sosai ba sai ɗanrago ya sake tsintar ludayi, sai Gizo ya ce da shi kar ya ɗauka. Sai suka wuce suka ci gaba da tafiya. Suna cikin tafiya sai suka ga fura a dame da suga. Sai Gizo ya ce da ɗanrago, ina ludayin nan? Sai ɗanrago ya ce da shi, ai kai ka ce kar na ɗauka. Sai Gizo ya ce da shi, to maza ka juya ka ɗauko, amma fa kar ka jima. Yana tafiya, sai Gizo ya kama shan fura, sai da ya kusa shanyewa sai ya bar wa ɗanrago ‘yar kaɗan. Da ɗanrago ya dawo sai Gizo ya ce da shi, ai ka ga tsiyarka, kai baka san a aike ka yi sauri ba. Ka ɗauki waccar ragowar ka sha. Sai ɗanrago ya ɗauka ya sha.

Shi ke nan sai suka sake ci gaba da tafiya, suna cikin tafiya sai suka iso wata mararraba. Hanya ɗaya ta yi tudu, ɗaya kuma ta bi gangare. To kan tudun akwai wuta, gangaren kuma akwai ruwa. Saboda haka sai Gizo ya ce da rago ya bi tudun da sauri, da ɗanrago ya ji haka sai ya bi tudun nan da gudu har ya faɗa cikin wutar nan. Can sai Gizo ya ji fush, fush, fush. Sai ya ce yawwa, nama ya gasu. Sai ya fito da naman ɗanrago ya cinye. Daga nan ya koma gida ya ce da tinkiya, ai ɗanta ya ɓata, saboda haka sai ta yi haƙuri. Tinkiya ba ta ce da shi komai ba, ta yi haƙuri.

Bayan an kwana biyu, sai Gizo ya ce da ɗantaure ya zo su tafi ci rani. Sai ɗantaure ya ce sai ya je ya gaya wa babarsa. Sai Gizo ya ce ya je. Sai ɗantaure ya je ya gaya wa akuya ya ce za su tafi ci rani shi da Gizo, sai akuya ta ce to shike nan ba komai, amma a riƙa kula.

Da ɗantaure ya dawo sai suka yi shiri suka tafi shi da Gizo. Suna cikin tafiya sai ɗantaure ya ga cokali, sai ya ce Gizo, ka ga wani cokali, in ɗauka ko kar na ɗauka? Sai Gizo ya ce kar ya ɗauka. Sai ɗantaure ya faki idon Gizo ya ɗauki cokali ya ɓoye shi a gemunsa, ya ce wannan zai yi mana amfani a nan gaba. Suna cikin tafiya sai suka ga shinkafa da miya. Sai Gizo ya ce da ɗantaure, ina cokalin nan? Sai ɗantaure ya ce ga shi, ai dama na ɗauka saboda na san zai yi mana amfani a gaba. Sai Gizo ya ce, ka ga ni fa bana son irin wannan, idan muna tafiya in ban ce a yi abu ba, to a dena yi. To zo mu ci. Sai suka cinye shinkafar nan tare da ɗantaure. Bayan sun gama ci, sai ɗantaure ya jefar da cokalin nan.

Daga nan sai suka ci gaba da tafiya, suna cikin tafiya sai ɗantaure ya ga ludayi, sai ya ce da Gizo, la, na tsinci ludayi, in ɗauka ko kar na ɗauka? Sai Gizo ya ce kar ya ɗauka. Sai ɗantaure ya faki idonsa ya ɓoye ludayi a gemunsa. Suna cikin tafiya sai suka ga fura damammiya da suga. Sai Gizo ya ce da ɗantaure, ina ludayin nan, sai ya ce ga shi. sai Gizo ya ɓata rai, ya ce to, zo mu sha. Sai suka shanye furar nan. Da suka gama sha, sai ɗantaure ya jefar da ludayin nan.

Daga nan sai suka ci gaba da tafiya. Suna cikin tafiya sai suka iso mararrabar nan, hanya ɗaya ta yi kan tudu, can kan tudun kuma wuta ce take ci. Ɗayar kuma ta yi gangare, ita kuma ƙasanta ruwa ne. Sai Gizo ya ce da ɗantaure ya bi tudu, shi kuma ya bi gangare. Sai Gizo ya ajiye jakarsa ya gangare. Da ɗantaure ya ga Gizo ya ɓace, sai ya buɗe jakar Gizo ya ɗauko takalmin Gizo ya wurga shi cikin wutar nan shi kuma ya faɗa cikin jakar Gizo ya rufe. Can sai gizo ya ji takalmansa suna fashewa fus, fus, fus. Sai ya ce yawwa, nama ya gasu. Sai ya fito ya ɗauko takalman nan ya kama ci, yana cikin ci yana cewa, kai naman ɗantaure ƙauri ne da shi, da haka ya cinye.

Bayan Gizo ya gama cin nama sai ya ɗauki jakarsa ya kama hanyar gida. Yana cikin tafiya sai ɗantaure ya kama waƙa daga cikin jaka yana cewa:

Ɗantaure:   Gizo wawa ya ci takalmi.
Gizo:           ‘Yar jakata kin iya waƙa, da da sule biyu da na ɗan baki.
Ɗantaure:   Gizo wawa ya ci takalmi.
Gizo:           ‘Yar jakata kin iya waƙa, da da sule biyu da na ɗan baki.
Ɗantaure:   Gizo wawa ya ci takalmi.
Gizo:           ‘Yar jakata kin iya waƙa, da da sule biyu da na ɗan baki.
Ɗantaure:   Gizo wawa ya ci takalmi.
Gizo:           ‘Yar jakata kin iya waƙa, da da sule biyu da na ɗan baki.

Gizo ya yi ta tafiya har ya dawo gida. Yana zuwa gida sai ya ce da akuya ai ɗanta ya ɓace sai ta yi haƙuri. Akuya ta ce to ai shike nan ba komai. Tana rufe baki sai ɗantaure ya buɗe jaka ya fito. Ya ce munafuki, gani da raina za ka ce na ɓata. Sai ɗantaure ya ce da akuya, ƙarya ya ke yi, so ya yi ya halaka ni. Sai ya kwashe dukkan labarin abubuwan da suka faru ya gayawa akuya.  Da gizo ya ga haka sai ya wurgar da jakar ya ruga da gudu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub