Tatsuniya: Maraya da Matar Ubansa

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Maraya da Matar Ubansa


Gata nan gata nan ku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani yaro sunansa Janiya Jannati. Shi Janiya maraya ne, babarsa ta mutu, yana zaune tare da matar ubansa. Ita kuma wannan mata bata son wannan yaro. To dama babarsu tana da dukiya, kuma an raba musu gado. Daga cikin abubuwan da ya gada akwai wata saniya mai magana.

Wannan mata kullum tana ta haƙon yadda za ta kashe yaron nan. Ashe duk abubuwan da take ƙullawa, saniyar nan ta sane da ita. Wata rana sai matar nan ta shirya cewa za ta zuba magani a cikin abinci ta baiwa yaron nan ya ci ya mutu. Sai saniyar nan ta ce da shi:

Janiya, Janiya, Janiya Jannati.
Za a baka tuwo da magani, Janiya Jannati.
Tuwon nan idan an baka, Janiya Jannati.
Kar ka ci, ka zo turkena, Janiya Jannati.
Ka tona rami ka zuba, Janiya Jannati.
Ka bar ɗan saura, Janiya Jannati.
ka mayar ka ce ka ƙoshi, Janiya Jannati.

Shike nan, sai aka baiwa yaron nan tuwo da magani a ciki. Sai ya tafi turken saniyar nan, ya haƙa rami, ya binne. Ya bar ragowa, ya mayar da akushin ya ce ya ƙoshi. Matar nan ta kashe kunne tana sauraron mutuwar yaro, amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa.

Ana nan, ana nan, sai wata rana ta sake dabara, ta ce za ta zuba magani a kunu, ta bashi. Da yaron nan ya je gurin saniyar nan sai ta ce da shi:

Janiya, Janiya, Janiya Jannati.
Za a baka kunu da magani, Janiya Jannati.
Amma idan an baka, Janiya Jannati.
Kar ka sha kunun ka zo turkena, Janiya Jannati.
Ka haƙa rami ka zuba, Janiya Jannati.
Amma ka bar ɗan saura, Janiya, Jannati.
Ka mayar da akushin ka ce ka ƙoshi, Janiya, Jannati.

Da aka baiwa yaron nan kunu, sai ya tafi turken saniyar nan ya haƙa rami, ya juye a ciki, ya bar ragowa ya mayar ya ce ya ƙoshi. Matar nan ta karɓi akushin nan tana ta murna. Ta saurara cikin dare ko za ta ji cikin yaro ya murɗe ya mutu. Shiru, bata ji komai ba. Sai abin ya ɗaure mata kai.

Ana nan, sai ta sake dabara ta ce, bari ta kai shi ɗakinta ta ƙona shi cikin dare. Da yaron nan ya je baiwa saniyar nan abinci, sai ta ce da shi:

Janiya, Janiya, Janiya Jannati.
Yau za a ƙona ka a ɗaki, Janiya Jannati.
Amma idan aka kai ka ɗaki, Janiya Jannati.
Kar ka yi barci, Janiya Jannati.
Idan matar ubanka ta fita, Janiya Jannati.
Ka cire rigar ɗanta ka saka, Janiya Jannati.
Ka saka masa taka, Janiya Jannati.
Ka tura shi makwancinka, Janiya Jannati.
Kai kuma ka koma nasa ka kwanta, Janiya Jannati.

Da dare ya yi, sai matar uban nasa ta ce da shi, Janiyana, na ga ɗakinka sauro yana damunka, yau ka zo ku kwana a ɗakina tare da ɗan’uwanka. Sai Janiya ya ce da ita to, zan zo.

Da dare ya yi, sai Janiya ya tafi ɗakinta, ya kwanta a kan shimfiɗar da ta yi masa. Sai ya yi likimo, kamar yana barci, can tsakar dare, sai ya gan ta, ta taso saɗaf, saɗaf, ta fice waje. Kafin ta dawo sai ya ta shi a hankali ya cire kayan jikinsa ya saka wa ɗanta, shi kuma ya saka na ɗan nata. Sannan ya ɗauke shi a hankali ya kai shi makwancinsa, shi kuma ya koma makwancin ɗan nata ya kwanta. Yana gamawa sai ga matar nan ta shigo da wuta. Tana zuwa, ba ta yi wata-wata ba kawai sai ta zuba wa ɗan nan nata ba ta san shi ne ba. Da ɗan ya ji zafi, sai ya riƙa sowa yana cewa, iya ni ne fa, ita kuma tana cewa, mutu dan ubanka, yau jaraba ta ƙare. Yaron nan ya ƙone ƙurmus. Da gari ya waye, sai ta ga ashe ɗanta ta ƙona. Sai ta haɗiyi zuciya ta mutu.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub