Tatsuniya: Mutum da Zabi

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Mutum da Zabi


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Akwai wani mutun yana so ya ci nama, sai ya rasa yadda zai yi, can sai wata dabara ta zo masa. Sai ya samu ruwa da wuƙa da buhu, ya tafi gurin da zabi su ke kiwo. Da ya kai gurin sai ya tsaya a gefe guda ya buɗe bakin buhun nasa ya ce da zabin nan:

Ku taru zabi ku taru, ku taru zan muku wasa.

Da zabin nan suka taru sai ya ce da su, idan na yayyafa ruwa sai ku gudu ku shige cikin buhun nan. Da ya yayyafa ruwa, sai zabi suka shige cikin buhun nan nasa. Bayan sun shisshiga da yawa, sai ya rufe bakin buhun ya yi tafiyarsa. Da ya je gida, ya riƙa fito da su da ɗai-da ɗai yana yanka wa.

Bayan ya gama yanka wa, sai ya fiffige, ya gasa yana ci. Yana cikin cin naman nan, sai ga wani abokinsa. Sai abokin nasa ya tambaye shi yadda aka yi ya samu wannan nama. Shi kuma sai ya gaya masa yanda ya yi ya samu waɗannan zabi.

Da abokin mutumin nan ya ji wannan labari sai shima ya ɗauki buhu ya tafi gurin da zabi su ke kiwo. Da ya je, sai ya ce da su:

Ku taru zabi ku taru, kutaru zan yanka ku.

Da zabi suka ji haka sai duk suka gudu. Sai wata ‘yar ƙarama maras wayo, ta je gurinsa, ya kamata ya yanka.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub