Tatsuniya: Tsiniyama da Lafiyana

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Tsiniyama da Lafiyana


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

A wani gari can zamanin baya an yi wasu matasa su biyu, waɗanda basa jin maganar iyayensu, sunayensu; Tsiniyama da Lafiyana.

Wata rana, sai Lafiyana ya ce da Tsiniyama, “Yanzu abin da ya kamata mu yi shi ne mu ƙona rumbun babanmu”, da Tsiniyama ya ji haka, sai ya ce da Lafiyana, “Lallai wannan shawara taka ta yi daidai”, saboda haka sai suka ƙone rumbun. Bayan sun ƙone rumbun, sai babansu ya tsine musu, kuma ya kore su daga gidansa. Sai suka koma kasuwar garinsu suna kwana.

Waɗannan yara duk da cewa sun bar gidan baban nasu, basu daina ta’adi ba sai ma abin da ya ƙaru. Ana nan ana nan, wata rana sai Tsiniyama ya baiwa Lafiyana shawarar cewa yakamata su kashe ‘yar mai gari (wato ‘yar sarkin garinsu kenan). Lafiyana ya yarda da wannan shawara ta Tsiniyama, saboda haka sai suka kashe wannan ‘ya ta mai gari. Bayan sun kasheta sai mai gari ya sa a kamo su dan a yanke musu hukuncin kisa, amma, hakan bata samu ba suka riƙa ɓuya. Wannan hali da suka shiga na ɓuya, ta saka su cikin mayuwacin halin da har ta kai ga shi Lafiyana ya rasa ransa. Ganin mutuwar Lafiyana, sai Tsiniyama ya sulale cikin dare ya shiga uwa-duniya.

A cikin wannan yawon duniya da Tsiniyama yake yi, wata rana sai ya haɗu da wani makiyayi yana kiwon dabbobi, sai ya ce da makiyayin ya je ya huta a inuwa shi zai taya shi kula da dabbobin. Da makiyayi ya ji haka sai ya ji daɗi, zatonsa shi ya samu mutumin kirki. Zuwan makiyayi inuwa ke da wahala, sai barci ya kwashe shi, da Tsiniyama ya tabbatar da makiyayin nan ya yi barci, sai ya ƙwaƙule idanuwan dabbobin nan ya gasa su tsaf, sannan ya ɗauka ya tafi gurin makiyayin nan ya tashe shi daga barci ya ce da shi, “malam ka ga irin maiƙoƙon (gurjiya) garinmu”, sai makiyayin nan ya karɓa yana ci yana santi yana cewa, “Kai, amma maiƙoƙon garin nan naku tana da daɗi”.  Bayan makiyayin nan ya gama cinye maiƙoƙon nan tsaf, sai Tsiniyama ya ce da shi, “Malam ni zan ƙara gaba”, da makiyayi ya ji haka sai ya yi masa godiya, shi kuma ya koma wajen dabbobinsa.

Da zuwan makiyayi wajen dabbobin nasa, sai ya ga wasu basu da idanuwa, saboda haka sai ya ƙwallawa Tsiniyama kira, da Tsiniyama ya ji, sai ya juyo zuwa ga Makiyayi, sai Makiyayi ya tambaye shi ya ce, “Yaya na ga wasu dabbobina babu idanuwa?”. Sai Tsiniyama ya amsa da cewa, “Maiƙoƙon da ka ci ta ubanka ce?” Sai Makiyayi ya ce, “Amma kai dai Allah ya tsine maka”, sai Tsiniyama ya ce da shi, “Ai dama can ni sunana Tsiniyama”, ya wuce ya bar Makiyayi cikin mamaki.

Da Tsiniyama ya ci gaba da tafiya, sai ya ci karo da wani alaramma rataye da gafakarsa, sai ya kada baki ya ce da shi, “Alaramma na ga alamar gajiya tare da kai, kawo gafarka taka mana na ɗan riƙe maka ko ka ɗan huta!” Da alaramma ya ji haka sai ya miƙa masa, suka ci gaba da tafiya alaramma na gaba Tsiniyama kuma na biye da shi, can bayan wani lokaci, sai Tsiniyama ya buɗe wannan gafaka ya fito da takardun ciki ya wurga sama, sai takardun Al-Ƙur’anin da suke ciki suka tashi sama, sai Tsiniyama ya ce da alaramma, “Alaramma ka ga irin balbelun garinmu”, sai alaramma ya ɗaga kai sama ya hangi fararen takardun nan sai ya ce, “Lallai balbelun garinku suna da kyau”. Sai suka ci gaba da tafiya, suna cikin tafiya sai suka iso mararraba, sai Tsiniyama ya ce da alaramma shi zai bi ta nan, da alaramma ya karɓi gafakarsa sai ya ji babu nauyi, sai ya ce da Tsiniyama, “Ina Al-Ƙur’anina?”, sai Tsiniyama ya kada baki ya ce, “Balbelun garin namu da ka gani na ubanka ne?”, sai hankalin alaramma ya tashi, ai kafin alaramma ya buɗe baki ya yi magana, Tsiniyama ya haukace.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub