Tatsuniya: Yarinya da Ƙawayenta

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tatsuniya: Yarinya da Ƙawayenta


Gata nan gata nanaku. Ta zo mu ji ta.

Wata ce dai, wata ce dai, za su tafi wasan kalangu wani gari mai suna Dahira da ita da ƙawayenta. Sai ta je gurin ummarta, ta ce da ita ta bata zaninta za su je wasa. Sai ummar tata ta ce ba zan ba ki ba sai kin samo min ‘ya’yan ɓaure. Shike nan sai ta tafi daji, ta je gidindin ɓaure ta ce da shi:

Yarinya:     Ɓaure, ɓaure gareka na zo.
Ɓaure:         In ba ki me?
Yarinya:     Ka ba ni ‘ya’ya.
Ɓaure:         Ki kai wa?
Yarinya:     In kai wa inna.
Ɓaure:         Ta ba ki me?
Yarinya:     Ta ban zani na, mu je mu wasa a Dahira.

Da ɓaure ya ji abin da yarinya ta ce, sai shi ma ya ce ba zai bata ba sai ta kawo masa kashin shanu, ta zuba masa taki. Daga nan sai ta tafi garke. Ta je ta samu shanu ta ce da su:

Yarinya:     Shanu, shanu gurinku na zo.
Shanu:        Mu ba ki me?
Yarinya:     Ku ba ni kashi.
Shanu:        Ki kai wa wa?
Yarinya:     In kai wa ɓaure, ya ba ni ‘ya’ya na kai wa inna, ta ban zani na mu je mu wasa a Dahira.

Sai suma shanu suka ce ba za mu baki ba sai kin samo mana ciyawa mun ci sannan mu ba ki kashi. Daga nan sai ta tafi daji, ta ce:

Yarinya:     Kai daji gurinka na zo.
Daji:            In ba ki me?
Yarinya:     Ka ban ciyawa.
Daji:            Ki kai wa wa?
Yarinya:     In kai wa shanu su bani kashi, in kai wa ɓaure ya bani ‘ya’ya, in kai wa inna, ta ban zanina mu je mu wasa a Dahira.

Sai daji ya ce to ga ciyawar nan ki ɗebi yadda ki ke so. Sai yarinyar nan ta ɗebi ciyawa, ta kai wa shanu suka ci, suka yi ka shi ta ɗiba, ta kai wa ɓaure, shi ma ya bata ‘ya’ya masu kyau, ta ɗiba ta kai wa ummarta. Da ta kai wa ummarta ta sai ce na gode, ga zaninki nan, ki ɗaura, a dawo lafiya. Ita kuma yarinya ta karɓa ta ɗaura suka tafi wasa Dahira.

Tunƙurunƙus, badan Gizo ba da na yi ƙarya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub