Tsangarwa Farmers Association

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Tsangarwa Farmers Association


Gabatarwa

Tsangarwa, gari ne a ƙaramar hukumar Gwaram da ke cikin Jahar Jigawa a Najeriya. Allah Ya albarkaci wannan gari da wadattaciyar ƙasa da ruwan da za a iya aiwatar da ayyukan gona (noma da kiwo) damina da rani. Noma kuma shi ne tushen arziƙi wadda ta hanyarsa ake ciyar da duniya.


Ƙungiyar Manoman Garin Tsagarwa, wato Tsangarwa Development Association wadda ake taƙaita ta da TSAFA, ƙungiya ce da take da manufa da kuma burin haɓɓaka harkar noma da rayuwar manoma a wannan gari na Tsangarwa. Taken wannan ƙungiya shi ne, MANOMI KE CIYAR DA DUNIYA. Alfanun noma kuwa ya fi ƙarfin iyakance. Kaɗan daga ciki sun haɗa da:

 1. Samar da ayyukan yi.
 2. Samar da kuɗaɗen shiga.
 3. Samar da abinci.
 4. Inganta harkokin tsaro.
 5. Inganta Kiwon Lafiya.
 6. Samar da abincin dabbobi da sauransu.

Samar da Ayyukan Yi

Noma, hanya ce ta samar da hanyoyin dogaro da kai, a bisa ƙiyasi, mun auna cewa idan har za a noma gonaki hamsin (50) kacal da rani a duk shekara, to Tsangarwa za ta samar da guraben ayyukan yi ga sama da mutane ɗari biyu da hamsin (250); wato abin da ake kira direct labour a Turance.

Samar da Kuɗaɗen Shiga

Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras. Bawan damina attajirin rani. Kaɗan kenan daga cikin irin kirarin da Bahaushe yake yi wa noma da manomi.
Ta hanyar noman rani, za a iya samar da ƙarin ciniki ga masu gudanar da wasu sana’o’i har nau’uka sama da goma sha biyar (15) da ake kira indirect labour a Turance. Waɗannan nau’ukan sana’o’i sun haɗa da:

 1. Masu sayar da iri.
 2. Masu sayar da taki.
 3. Masu sayar da kayan feshi.
 4. Masu haƙa rijiya.
 5. Masu gyaran rijiya.
 6. Masu sayar da kayan gyaran rijiya.
 7. Masu gyaran injinan ban ruwa.
 8. Masu sayar da kayan gyaran injinan ban ruwa.
 9. Masu sayar da manfetur, baƙin mai da mangas.
 10.  Masu harkar sufuri.
 11.  Masu dillancin kayan gona.
 12.  Masu sayar da kayan gona.

Samar da Abinci

Babban amfanin noma sama da komai kuma shi ne yaƙi da yunwa a duniya ta hanyar samar da abincin da za a iya kai shi koma ina ne a duniya. A sauƙaƙe, daga Kasuwar ‘Yankaba da ke Kano da kuma Kasuwar Dawanau, kayan da aka noma a Tsangarwa za su iya kai wa ko’ina a duniya.
Kenan, gudunmawar da ƙungiya za ta bayar ta hanyar noman rani kawai, za ta iya kai wa har fadar Shugaban Najeriya idan ta samu kakkyawar kulawa.

Inganta Harkoki Tsaro

Rashin aikin yi, yunwa da talauci suna daga cikin manyan hanyoyi samar da rashin tsaro a duniya. Idan har aka haɓɓaka harkar noma (noma rani a nan, kasantuwar lokacin rani ne mutane suke zaune basa aikin komai sai tafiya cirani a mafi yawancin lokaci), to abinci zai samu, za kuma a samu guraben ayyukan yi da ƙarin kuɗaɗen shiga. Saboda haka za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a garin Tsangarwa da kewaye.

Ingantan Kiwon Lafiya

Yunwa da gurɓatacciyar iskar shaƙa, hanyoyi ne da ke haifar da cututtuka. Ta hanyar noma ake samun wadataccen abinci da kuma ingantacciyar iskar shaƙa daga numfashin tsirrai da ake nomawa. Saboda haka, lafiya za ta inganta musamman a lokacin rani da ruwan sama yake ɗaukewa.

Samar da Abincin Dabbobi

Kamar yadda aka sani, tun daga farkon lokacin noma har zuwa girbin amfani, dabbobi suna samun ɗanyar ciyawar da suke ci su yi tatul. Amma idan rani ya yi takan kai su ga cin ƙasa abin da yake yi musu illa ga lafiyarsu da kuma tursasa wa makiyaya yin hijira daga wannan gari zuwa wancan domin nema wa dabbobi abinci. Ta hanyar noma rani za a shayar da ƙasa ta fitar da ɗanyar ciyawar da dabbobi za su ci a lokacin rani.

Dokar Tsare Dabbobi

Gwamnatin Jahar Jigawa ta yi kyakkyawan tanadin dokokin ɗaure dabbobi a Kundin Dokokin Jahar Jigawa (Jigawa State Laws), babi na talatin da biyu (Chapter 32); dokar da aka yi wa laƙabi da Control of Animals Law a Turance. Ana iya latsa nan domin sauke wannan kwafin dokoki.

Sashe na tsakwas na wannan doka, ya bai wa ƙungiyoyi irin namun nan damar yin ram da irin waxannan dabbobi tare kuma da damƙa su ga ofishi ko hannun jami'in 'yansanda mafi kusa ba tare da jinkiri ba domin fuskantar hukunci.
Muna fatan yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da hukumomi, bankuna, ƙungoyoyin manoma da kamfanonin harkokin gona domin cimma wannan manufa tamu ta alheri.
Bisa haka muna kira ga duk wanda ke da sha’awar zuba jari a wannan harka da cewa ya tuntuɓe me.


Shafukan Sada Zumunta:


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub