Ganuwar Zazzau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Ginin Ganuwar Zazzau


Ganuwar Zariya ita ce kantagar da ta kewaye birnin Zariya. An gina wannan ganuwa ne domin samar da kariya ga jama’ar birnin Zariya daga hare-haren mayaƙa da miyagun dabbobi kamar yadda yake a sauran birane. Suleiman (2007), ya ruwaito cewa an gina wannan ganuwa ne a cikin ƙarni na 15.

Wannan ganuwa ta Zariya, sabuntawa ce ta asalin ganuwar da sarakunan haɓe suka gina. Suleiman (2007), ya kawo cewa harin da sarkin Kano Kanajeji (c. 1390 – 1410), da kuma buƙatar da ke akwai na haɗuwar jama’a waje guda domin bunƙasar tattalin arziƙi da inganta yanayin tsaro da sauransu, shi ya wajabtawa jama’ar Zazzau sake sabunta ginin ganuwar da ma canzawa fadar masarautar sheƙa zuwa gurin da take a yau wanda ake kira Zariya.

Jama’ar birnin Zazzau su suka haɗu suka aiwatar da wannan aiki na gini tare da la’akari da bayar da gudunmawa a fannin da ya dace. Misali, maƙera su ke samar da kayan aiki kamar irin su fartanya, galma, sangwami, magirbi, da sauransu. Magina su ke da alhakin binciko gurbin da za a yi gini, tsara abubuwan da za a yi amfani da su wajen gini, aiwatar da gini da kuma tattalinsa. Masassaƙa su ke sassaƙa katakon da ake amfani da shi wajen yin ƙyamare, da sauran katakwayen da ake buƙata wajen gini, maƙaɗa su suke zaburantar da jama’a, haka nan sauran jama’a duk sun bayar da gudunmawa kamawa daga masu dafa abinci, masu ɗauko ruwa, masu ɗebo ƙasa, masu kwaɓa, da sauransu. A haka aka gina wannan ganuwa kamar yadda ya zo a Sueliman (2007).


Wannan ganuwa na ce zamanin gwamnan Kaduna, Manjo Janaral Lawal Ja'afaru Isa aka sake ginata. Tana nan a jikin Ƙofar Jatau.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin Zaria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub