Kofar Doka Zariya

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zariya Ƙofar Doka


Wannan ƙofa ta samo sunanta ne daga bishiyoyin da suke kewaye da ƙofar. Akwai bishiyoyi masu wannan sunan na 'Doka' a kewaye da wannan ƙofa. A wata faɗar kuma da ta ke kama da wannan, an ce daga wata bishiya ce ƙwaya ɗaya da ke gidan sarki Abubakar wanda yanzu gurin aka mayar da shi gidan yari. Wata faɗar kuma an ce sunan wani mutum ne da ke zaune kusa da ƙofar. Ta wannan ƙofa ake fita zuwa Kano da Katsina.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub