Zariya Kofar Jatau

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zariya Ƙofar Jatau


Ƙofar Jatau an gina ta ne a farkon ƙarni na 17, a zamanin sarki Jatau wanda ya yi mulkinsa daga 1782 zuwa 1802. Wannan shi ne dalilin da ya saka ake kiranta da wannan suna na ƙofar Jatau. Amma a wata ruwayar an ce a'a, ta samo sunanta ne daga sunan wanda ke gadin ƙofar.

Idan muka yi duba izuwa ga lokacin da aka gina waɗannan ƙofofi guda biyu, za mu fi yarda da cewa shi sarki Jatau da ya gina su, ya gina ne a ƙarshen mulkinsa, saboda haka zaton cewa daga sunansa aka yi wa wannan ƙofa suna ya fi rinjaye.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja’afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub