Zariya Kofar Kibo

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zariya Ƙofar Tukur-Tukur/Ƙofar Kibo


Sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga Dutsen Tukur-Tukur, wanda ya ke kusa da wannan ƙofar.


Dutsen Tukur-Tukur

Amma daga baya, a cikin ƙarni na 19 sunan nata ya canza zuwa ƙofar Kibo, sunan da aka yanka shi daga kibau (kibau jama'u ne na kibiya wacce ake harbi da ita). Wannan kuma ta faru ne sakamakon yaƙin da aka yi a wannan ƙofa tsakanin sarkin Ningi Haruna da sarkin Zazzau Sambo (1879-1888 A.D.), faɗan da ya faru sakamakon gayyato sarkin Ningi da Galadima ya yi da nufin ƙwace masarautar daga hannun shi Sarki Sambo bayan, da Sarki Sambo ya yi nufin tafiya Sakkwato. Wannan ƙofa ta ita ake fita zuwa Zamfara, Kabbi (Kebbi), Yawuri, da kuma Sakkwato.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub