Zariya KofarKona

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Zariya Ƙofar Kona


Sunan wannan ƙofa ya samo asali ne daga wani gari da ke gabas da birnin Zariya. Shi kansa garin ya samo asali ne daga wani malami da almajiransa da suka fito biɗa. A ƙoƙarinsu na samun gurin da ke da albarkar noma, sai suka ga kamar wannan guri ya dace, sai shi malamin ya tambayi almajiransa da cewa, “Ko nan za mu zauna?” to sai suka haɗu a kan su zauna a nan ɗin. Bayan an kafa garin sai aka riƙa kiransa da suna Kona. Sannan kuma da shi malamin suka ta shi yin hijira daga wannan gari domin shigowa cikin birni, an ce ta wannan ƙofa suka shigo. Saboda haka ake kiranta da wannan suna.

Manazarta:


Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.

Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.

Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub