Ƙofofin Birnin Zazzau
Suleiman (2007), ya ruwaito Baikie ya ce ƙofofin Zariya guda tara ne, sai ya lissafo su kamar haka:
- Ƙofar Kona
- Ƙofar Gayan
- Ƙofar Kuyambana
- Ƙofar Doka
- Ƙofar Bai
- Ƙofar Galadima
- Ƙofar Matarkwasa
- Ƙofar Jatau
- Ƙofar Tukur-Tukur/ Ƙofar Kibo
Ya kuma ci gaba da faɗin cewa ƙofar Matarkwasa ana kiranta da Sabuwar ƙofa, ƙofar da aka rufe ta a cikin ƙarni na 19.
Waɗannan ƙofofi ba a lokaci guda aka gina su ba, an gina shida ne da farko sannan kuma daga baya aka sake gina wasu guda uku. Shidan da aka fara ginawa su ne:
A farkon ƙarni na 17 bakwa sai aka sake gina wasu guda biyu:
Sai kuma Ƙofar Matarkwasa wacce a ƙarni na 19, a shekarar 1808, da sarki Makau ya fasa tsakanin Ƙofar Jatau da Ƙofar Kuyambana ya shiga fada ya ɗauke takobin sarki ya gudu da shi.Manazarta:
Arnette E.J. (1920). Gazetteer of Northern Provinces of Nigeria. Gazetteer of Zaria Province. Waterlow & Sons Limited. London, Dunstable & Waterford.
Dalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria.
Suleman U. (2007). A History of Birnin ZAria from 1350 – 1902. M.A. History, Ahmadu Bello University, Zaria.
Sarakunan Zazzau
- Musa Bamalli
- Yamusa Babarbare
- Abdulkarim
- Hammada
- Muhammadu Sani
- Sidi Abubakar
- Abdussalami
- Abdullahi
- Abubakar
- Abdullahi
- Muhammadu
- Usman Yero
- Shehu Idris
Ƙofofin Zazzau
- Ƙofar Kona
- Ƙofar Gayan
- Ƙofar Kuyambana
- Ƙofar Doka
- Ƙofar Bai
- Ƙofar Galadima
- Ƙofar Matarkwasa
- Ƙofar Jatau
- Ƙofar Tukur-Tukur
Tura wannan shafi zuwa ga abokai ta:
TweetLatsa madannin "Like" ka nuna goyon baya ko kuma "Share" ka yaɗa shafin