Sarkin Zazzau Abubakar

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Abubakar ɗan Malam Musa 1871 – 1875


Gabatarwa

Shi ne sarki na sittin da tara a jerin sarakunan Zazzau, sannan kuma sarki na tara a jerin sarakunan Fulani, haka kuma sarki na uku a jerin sarakunan Mallawa.

Sarkin Musulmi ya naɗa shi kai tsaye ba tare da tuntuɓar masu naɗin sarkin Zazzau ba. Shi ne ke riƙe da muƙamin Wamban Zazzau tun zamani sarki Abdussalami har zuwa zamanin sarki Abdullahi.

A zamaninsa ya naɗa ma’aji na biyu da nufin kula da yankin Tsakiyar-Kudancin Zariya musamman yankin Kachiya, saboda gazawar sarkin Kajuru wajen mulkar ƙabilun Kamantan, Jaba, da kuma Ikulu. Sannan kuma ya yi yaƙi da mutanen Gwodo garin da ke kusa da Jema’a.

Ya yi sarautar Zazzau tsawon shekara huɗu, ya rasu a shekarar 1874.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria. Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London:

Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub