Sarkin Zazzau Hammadan

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Hammada ɗan Yamusa 1846 – 1846 A.D.


Gabatarwa

Malam Hammada shi ne sarki na 64 a jerin sarakunan Zazzau, sannan kuma sarki na 4 a jerin sarakuna Fulani, kuma sarki na biyu a jerin sarakuna gidan Barebari. Shi ɗa ne a wajen malam Yamusa Babarbare. Naɗin sarautarsa ya biyo bayan rasuwar Malam Musa Bakatsine. Masu naɗa sarkin Zazzau suka zaɓe shi sannan kuma suka tura sunansa zuwaga sarkin Musulmi Aliyu Babba.

Saratutarsa bata tsaiwata ba, ya yi sarauta ta tsawon kwanaki hamsin da uku Allah ya karɓi abunsa.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria.

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub