Sarkin Zazzau Musa Bamalli

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Musa Bamalli


Gabatarwa

Malam Musa Bamalli mutumin Mali ne, wanda hakan ce ma ta saka ake ƙiransa Bamalli, wato mutumin Mali. Shi mutum ne masani kuma jarumi, Allah ya yi masa baiwa da son yaɗa ilimin addinin Musulunci tare da ganin an yi aiki da shi. Malam Musa Bamalli dama can a Zariyayake da zama tun kafin Jahadin Shehu Ɗanfodiye.

Malam Musa Bamalli ya yi karatun addini a garin Zariya a gidan Limamin Kona. Sun zauna tare da abokinsa Malam Abdulkarimu Bakatsine. Bayan da ya samu karatu a gidan Limamin Kona kuma sai ya tsunduma cikin harkokin wa’azi, inda ya riƙa bin garuruwa yana wa’azi, daga ciki akwai Igabi.Sannan kuma daga baya ya bar garin Zariya ya riƙa bin garuruwa ya karantar da addinin Musulunci tare kuma da Wa’azi.

Malam Musa Bamalli ya samu halartar yaƙin da Shehu Ɗanfodiye ya yi da sarkin Gobir a Tafkin Kwatto, wanda shi ya kai ga nasarar tumɓuke saratautar gargajiya ta mutanen Gobir a lokaci guda kuma ya zama murhun kafa Daular Musulunci ta Shehu Ɗanfodiye a shekarar 1804 kamar yadda Ɗalhatu (2002) ya ruwaito.

Bayan samun nasarar yaƙin Tafkin Kotto kuma sai ya karɓi tuta a hannu Shehu ya nufi Zariya. Ya tafikar da mukin sa akan salon mulkin Haɓe (Hausawa), sannan kuma ya zo da wasu sabbin hanyoyin mulki.

Malam Musa Bamalli shi ne ya fara raba mulki da shari’a ta hanyar samar da ofishin alƙali, sannan kuma shi ya ƙirƙiri ofishin waziri wanda aikinsa shi ne bai wa sarki shawara. Sunan Wazirin nasa Malam Cufudu. Sannan kuma shi samar da ofishin sa’i inda ya naɗa Malam Abdulkarimu a wannan ofishin, sai kuma ofishin Madaki, inda aka naɗa Malam Yamusa a matsayin Madakin Zazzau, da sauran muƙamai masu fa’ida kamar yadda ya zo a ruwayar (Umaru, 2002). Ya kuma ci gaba da cewa bai bar malamai ma a bay aba, saboda ya shigar da su cikin gwamnatin tasa.

Malam Musa Bamalli, ya yi sarautar Zazzau tsawon shekara goma sha bakwai. Ya rasu a shekarar 1821 A.D.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria.

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub