Sarkin Zazzau Sidi Abdulkadir

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Malam Sidi Abdulkadir 1853 – 1853

Gabatarwa

Malam Sidi Abdulƙadir Bamalli ne. Shi ɗa ne ga sarki Malam Musa Bamalli, shi ne sarkin Zazzau na sittin da shida sannan kuma sarki na shida a jerin sarakunan Fullani, hakanan kuma sarki na biyu a jerin sarakunan Mallawa.

Naɗinsa ya biyo bayan rasuwar Malam Muhammadu Sani. Masu naɗin sarki suka tura sunansa zuwa Sakkwato inda sarkin Musulmi Aliyu Babba ya amince da naɗinsa a kan karagar mulkin Zazzau.

Da hawansa karagar mulki, ya yi ƙoƙarin kawo daidaito tsakanin gidaje uku, Mallawa, Barebari, da kuma Katsinawa waɗanda ke gadon sarautar Zazzau. Wannan yunƙuri da ya yi ta hanyar naɗin sarautar, ya haifar masa da turjiya daga tsatsonsa gidan Mallawa. Ya naɗa Abdullahi ɗan sarki Hammada a matsayin Madakin Zazzau, sai kuma wani ɗan sarki Hammada ɗin a matsayin Galadiman Zazzau, sai kuma Aliyu ɗan sarki Abdulkarimu Bakatsine a matsayin Iyan Zazzau. Waɗannan naɗe-naɗe nasa ya tunzura sauran ‘yan’uwansa Mallawa, inda suka kalli abun a matsayin yunƙurin kawar da zuriyar ta mallawa daga sarautar Zazzau, duk da cewa shima Bamallin ne. saboda haka sai suka haɗe masa baki suka kuma kai kokensu zuwa ga sarkin Musulmi. Da wannan koke nasu ya je kunnen sarkin Musulmi, sai sarkin Musulmi ya wakilta Wazirin Sakkwato da nufinn ya zo ya sasanta tsakani.

Da isowar Wazirin Sakkwato Zariya, sai Malam Sidi Abdulƙadir ya hana shi shiga garin na Zariya. Saboda haka dole Wazirin Sakkwato ya tsaya garin Gimi, wanda yake da tazarar kusan mil goma daga garin na Zariya. Duk da haka dai Waziri ya aike wa Sarkin Zazzau yana tambayarsa dalilin faruwar wannan al’amari, shi kuma sai ya amsa masa da cewa, “Wannan ba matsalar Sakkwato ba ce", saboda haka sai Waziri ya koma gida.

Sarkin Musulmi ya kalli wannan al’amari a matsayin rashin ɗa’a, a saboda haka sai ya yi umarni da cire shi sarki Sidi Abdulƙadir daga kujerar sarautar Zazzau.

Bayan cire sarki Sidi Abdulƙadir daga sarautar Zazzau, ya ƙaura zuwa Wurno inda ya zauna a can har rai ya yi halinsa.

Manazarta:


Ɗalhatu U. (2002). Malam Ja'afaru ɗan Isiyaku, The Great Emir of Zazzau. Ahmadu Bello Uniɓersity Press. Zaria – Nigeria

Northern Nigeria Ministry of Information (1965). The Fascinating Provinces of Northern Nigeria. Gaskiya Corporation, Zaria-Nigeria.

Smith M.G. (1970). Government in Zazzau 1800-1950. London: Oxford University Press for the International African Institute. 371p. (Amaury Talbot Book Prize). Reprinted in 1964 and 1970.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub